20

574 34 0
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@mamsuhaimerh

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*

*We are here to make you happy, smile and to réalized that we are the best among all......DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO.*

*20*
             Tashi yayi ya ma Mama sallama cewa zai tafi, ina zaune kamar bansan ma yayi maganar ba, ina kallon Mama tanamin alamu da Idonta na masa rakiya ni kuwa na zum'buri baki na zauna har saida tace "tashi ki rakashi mana".

Amsawa nayi da to na tashi nabi bayansa, saida muka fita harabar gidan cikin shagwa'ba nace "yanzu fa tafiya zakayi ka barni ko?"

Hannunsa ya Sanya a 'kirjina yace "wa yace miki tafiya zanyi na barki? Karki damu ina Nan, da zarar kinyi kissing d'ina ki sanya hannunki a nan" ya kama hannuna ya d'aura kan nasa yace "idan kikayi haka sai ki ambaci sunana, Zan amsa miki da yanayin bugun zuciyarki".

Hannuna d'ayan ba d'aura a kafad'arsa nace "dama haka ka iya soyayya boo-boo na? Banda idon Mama na kaina ai binka zanyi mu gudu sai irin 11 d'innan ka  dawo dani a sace".

Dariya yayi ya sanya hannuwansa a 'kuguna ya dagani na koma daidai da fuskarsa, hannuna na sa'kala a wuyansa domin na daidaita yace "kamar wasu teenagers? Ai yanzu idan inaso na saceki kawai Kiran Mama zanyi nace zamuje unguwa".

"Ni kawai neman magana nakeji ai, so nake naga ya Mama zatayi idan nakai dare ban dawo ba sannan wani ya ajiyeni".

Girgiza kai yayi yace "naughty girl, kallonki kawai zatayi tace Allah ya shirya".

Tura baki nayi nace "yanzu shikenan bazamu fita ba?"

Ajiyeni yayi yace "yauwa....shawara tazomin yanzunnan, muje gida mana mu d'auko miki kaya".

"Hakane kuma fa, amma banason shiga gidannan boo-boo kaga dai yanda nake komawa a cikin gidan, kuma gashi banzo da komai ba sai kayan jikina bansan ma dame zanyi bacci ba".

Kama hannuna yayi yace "to ba sai mu siyo miki kayan baccin ba? Idan yaso gobe sai na kawo miki kayan da safe, muje kawai" ya 'karashe maganar Yana Jan hannuna yana gaba.

Dariya nayi nace "dakata mana malam, banda abinka ai sai su damu ganin ban dawo ba, muje mu fad'a musu zamu fita mana ko?"

Komawa mukayi na sanarwa mama zamu fita na d'auki zumbulelen hijabinta na saka, kashedi tayimin na mu dawo da wuri Kar muyi dare a waje.

Wani d'an 'karamin shago kusa damu mukaje na samu kayan baccin da saura abubuwan da zan bu'kata zuwa safiya, duba agogo yayi yace "kai, dubi fa sai yanzu 8:20 tayi, ina ya kamata muje?"

Tagumi nayi nace "nifa kawai so nake naga daga ni sai kai, sati nawa bamuji d'umin juna ba ya kamata mu d'an _tattauna_".

Dariya yayi yace "kinyi gaskiya, ya kamata muyi meeting na musamman, amma wajen had'uwar ne fa...kinga gida dai ke baya miki dad'in zama".

Kallon bayan motar nayi tareda murmushi na d'aga glass d'in motar na kunna Ac, cire hijabina nayi na kalli bayan motar nace "are you thinking what I am thinking?".

Zubamin ido yayi yace "oh ni saluhu, wannan mata tawa ko 'yar kunyarnan ta mata batayi".

"Nayi kunya na cuci kaina da aurena ko? Ka godewa Allah ma da ya baka mai 'ko'kari irina, idan kuma kunyar kakeso sai na koma, inace kaine ka ro'keni da Allah cewa na dena kunyarnan, nayi fushi ma maidani gida kawai". Na fad'a Ina maida hijabina.

Cikin sauri ya ri'ke hijabin yace "haba my humra, my saje, kinsan dai yanda nakeson sajennan nawa, to na fiki sonshi, yanda wayewar kannan taki ke birgeni bazan iya kisaltawa ba, inaso na tsokane ki need kawai domin idan kika had'e rai kinamin matu'kar kyau".

NAYI DACE.Where stories live. Discover now