40

632 35 1
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@ mamsuhaimerh

*40*
              *I really appreciate your love for me and my writing, dukda naso na d'an huta nayi tunani akan abinda nake rubutawa amma some readers sun fini dad'in baki😅 and it won't be polite to say no saboda haka gani na dawo, Ina fata abinda zan rubuta zai muku sweet😚😚love from hajjaju😂*

A gajiye na shaso kwanar gidan Aunty, yau munsha aiki fatana kawai na samu na huta, mayafin abaya na yafa kasancewar na fito abokiyar aikina na sallah da hijabina kuma bazan iya jira ba, Saleh na hango a tsaye yana juya key a hannunsa sai raba ido yakeyi.

Mamaki nayi ganin Huda a hannunsa, ya kamata ace yana wurin aiki yanzu meyasa jabir ya barshi ya taho? Me yazo yimin ma in the first place?

Idanunsa na kaina har nayi parking, dukda nayi farin cikin ganin Huda amma ban wani nuna ba kar yayi tunanin shi nake farin cikin gani, domin ina ganinsa maganar sultana ce ta fad'omin ta auren da zaiyi.

Cikin 'karfi na daki murfin motar ina kallon idonsa a kan motar tawa, domin yasan tafi tashi tsada da kyau.

Murmushi ne ya bayyana a fuskata jin Huda ta kirani da maama, nayi tunanin ta mantani a wannan lokacin da muka d'auka bama tare amma abin mamaki ta ganeni, kar'bar ta nayi na rungumeta a 'kirjina.

"Motarki tayi kyau" ya fad'a yana kallon jikina babu ko kunya, doguwar riga ce a jikina mayafin ne dai a 'kirjina ya tsaya, murmushin takaici nayi nace "too bad ba da kud'in da na sata a gidanka na siya ba, da kud'ina na siya".

Yanayinsa ne ya canza kunya da nadama suka kamashi, "boo-boo am....."

Dakatar dashi nayi nace "me ya kawoka? Me kuma ka nema ka rasa da kazo wajen 'barauniyar tsohuwar matarka?"

Ri'ke keys d'in hannunsa yayi cikin 'karfi, saidai bai amsamin ba yace "kayanki Sultana ta bani na kawo". Bud'e booth d'in motar yayi ya janyo akwatina, ajiyeshi yayi nace "thanks".

Har zan juya gida na tuna da Huda dake hannuna, haka nan banso ba na mi'ka masa ita, ri'ke wuyana tayi tareda d'aura kanta a kafad'ata alamun bazata je ba, ya Allah Huda dai so take da dad'e da mutuminnan saidai dad'ewata tare dashi yana nufin dawo da duk abubuwan da suka faru baya wanda bana son hakan ya faru, ina jin 'bacin raina Yana tasowa ga gajiya ga yunwa.

"Huda kije wajen uncle kinji? Gobe sai a kawomin ke ki kwana a wajena".

Girgiza kai tayi ba tareda ta d'ago ta kalleni ba hakan ya bawa Saleh damar fara magana "Boo...."

"Bilkisu" nayi saurin gyara masa, baisan rad'ad'in da yake sakawa zuciyata ba idan ya ambaci wannan kalmar, sunkuyar da kai yayi sannan yaci gaba "wallahi na Gane kuskurena Bilkisu kuma nayi nadama sosai, bansan me ya faru dani a wannan lokacin ba har na aikata hakan, Bilkisu wallahi na yarda dake kema kinsan haka amma nasan na tafka kuskure mai girma a wurinki, dan Allah ki daure ki dawo Bilkisu wallahi na miki al'kawarin makamancin haka bazai sake faruwa ba, ina bu'katarki a rayuwata Bilkisu".

Shiru nayi na zuba masa ido, bansan me zan furta masa ba saboda maganganunsa a wurina are bullshit, tambayoyi da dama sunzo kaina kamar me yasa sai yanzu zaka nemeni? Idan da gaske kana sona meyasa ko ta hanyar sultana bazaka ji lafiyata ba? Meyasa a duk danginka babu wanda yazo ya bani baki akan kayi kuskure? Saidai wad'annan tambayoyin ina tsoron jin amsarsu, numfashi naja nace "me kakeso yanzu Saleh?"

Shiru yayi na seconds sannan yace "inaso ki dawo gareni Bilkisu, tunda da aurena a kanki".

Dariya ce ta 'kwacemin nace "are you stupid? Wani aurenka ne a kaina?"

Zare ido yayi sannan a hankali yace "har yanzu wata uku bai cika ba...".

Wata dariyar na sake yi nace "idda ba watanni uku bane gareni karka manta ni ba 'karamar yarinya bace, jini uku ne kuma nayi na gama".

NAYI DACE.Where stories live. Discover now