45

556 30 0
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@ mamsuhaimerh

*45*
              Wata lafiyayyar dinner aka had'a a can Abuja, sai 12:30 sannan muka bar wurin muka wuce gidan Aunty Aisha.

Bacci ne sosai a kaina amma su babu alamun bacci a tare dasu, tashi nayi idona na rufewa nace "to saida safenku bacci nakeji".

D'akin Raudah na nufa Aliyu ya kira sunana, juyawa nayi yace "Ina zakije? Ai gida zamu wuce".

Kallon Raudah nayi na kalli Aunty Aisha, tashi yayi tareda mi'komin hannu alamun na taho mu tafi, no'kewa nayi na 'kara sauri domin na shiga d'akin, takunsa nakeji a bayana cikin sauri, ban ankara ba naji ya ri'ko cikina ya raba 'kafafuwana da 'kasa, kunya ce ta kamani na fara wutsil-wutsil da 'kafa su Raudah kuwa ba abinda sukeyi sai dariya, maganarsa naji a bayana yace "da ace inada 'karfi a kafad'a zan saka ki".

A hakan ma naga 'ko'karinsa domin ya ri'keni kamar wata 'karamar yarinya, ture hannunsa nayi da 'karfina nace "Dan Allah ka sakeni su Raudah fa na kallona kar Aunty ta fito".

"Mum!!", Bata amsa ba ya sake kiranta, fitowa tayi tace menene?

"Wai matata bazata bini gidanmu ba".

"Ka ajiyeta, ai dama anyi sai gone za'a kaita".

Ajiyeni yayi da sauri kuwa na shige d'aki ba tareda na juya ba, ni idan tawa za'a bi nayita zamana a nan.

"To Aunty na bita d'akin kenan?" Na jiyo maganar Aliyu, shiru naji Aunty Aisha tayi masa Raudah ce ta amsa masa tace "kar ka shigar mana d'aki ko kuwa mu barta anan sai tayi sati".

Toilet na shige na d'aura alwala, su fa maza basusan kunya ba, gado na haye cikin 'kan'kanin lokaci bacci ya d'aukeni.

Wani 'karamin wuni akayi yau inda 'kawayen Aunty Aisha suka zo, Raudah da twins ma sun kira friends d'insu, nayi shigata cikin lace riga da skirt na d'anyi kwalliya, nunawa mutane Aunty ni takeyi yawancinsu suna sa min albarka yayin da wasu saidai kawai su kalleni su gyad'a kai, ko kud'i ne ya musu.yawa har ya danne walwalarsu oho.

Abu d'aya na lura dashi wanda ya sake bani tsoro da auren Aliyu, ba 'karamin arzi'ki Allah yayi musu ba nayi zaton motocin da yake saidawa irin ka siyo ka sayar d'innan ne amma inaa, kamfani guda ne dashi motoci harda na had'a titi yake saidawa.

Mahaifinsa ya bar masa business d'in motar a hannunsa tun bayan ya kammala karatunsa, kuma Allah ya sanya masa albarka har wata plaza ya bud'e a can Abuja, duk shagunan dake ciki an kama kuma yanda nakejin labarin suna kar'bar hayar kusan 200k ko fiye da haka a duk shekara, duk wannan labari a yau na sameshi saboda 'kawayen Aunty Aisha basuda abun yi sai bragging akan arzi'kinsu, itama kuma ba'a barta a baya ba.

Tsabar gulma duk matan suka zauna har bayan la'asar lokacin da za'a kaini, gida kam da na ganshi saida na hadiyi miyau domin kyawun gidan da girmansa ya isa ta waje, wani irin gate ne daga waje gaba d'aya baifi tsayin mutum ba, daga nan zaa wuce makeken compound sannan a shiga main house, gabana fad'uwa yakeyi saboda bansan kayan d'akin da aka min ba, Allah yasa ba tsofaffina aka kawo ba domin zanji kunya gaban 'kawayen Aunty Aisha, maybe ma su fara gorantamin ko su fara mata habaici, ugh kad'an daga illar auren me kud'i dukda nima alhamdulillahi ba talaka bace amma maganar gaskiya kaf abinda na mallaka baifi kud'in mota d'aya a kamfanin Aliyu ba.

Ko da muka shiga palour kasa barin lullubin kaina nayi, palour d'in sai ka taka stairs zakayi 'kasa  sannan ga kujeruna a wurin, roynd ne shape d'in palour d'in haka kujerun nawa ma round ne sunyi matu'kar kyau, ga wata tafkekiyar tv ta cika bango, d'aga kaina nayi naga wata chandelier wadda tayi yanayi da ta frozen, da sauri na sauke kaina jin Raudah ta makeni a kaina, ban gama kallo ba aka shiga dani d'aki, saida na d'auke numfashina ganin had'uwar d'akin, ni Bilkisu anya  zan iya zama a wannan gado? Bedsheet ne fari 'kal a kan gadon sai wasu red flowers a jiki basufi 6 ba, a hankali na zauna naji katifar ta wani lotsa, hmm yau akwai bacci me dad'i.

NAYI DACE.Where stories live. Discover now