37

539 30 0
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad @ mamsuhaimerh

*37*
             Ina zaune na zubawa akwatina ido na rasa kayan da zan sanya domin ban zo da shirin fita ba kayana casual ne wad'anda zan fita aiki dasu, idan naje na cure na saka uniform idan na tashi na maidasu jikina na taho babu wani kayan kwalliya.

Kallonsu nayi sun gama shiryawa sai naji kamar nace na fasa zuwa, sunyi matu'kar kyau cikin lace sun yafa mayafansu a kafad'a d'aya suna d'aura d'ankwali, kallona Raudah tayi tace "anty Bilki Yaya Aali bayason jira fa gara kiyi ki shirya da wuri, naji maama na cewa bataso mu wuce 9:30 a waje".

Zuba tagumi nayi nace "bansan me zan saka ba", zama tayi ta fara zaro kayana tana kallo tana ajiyewa, wata doguwar rigata ta ciro milk colour ta bud'eta tace "wannan tayi kyau sosai, I am telling you yayanmu bazai iya d'auke idonsa daga kanki ba".

Ban kulata ba na kar'bi kayan na zura kan vest d'in jikina, kafin na d'au mayafi taja hannuna muka nufi mirror d'in d'akin ta zaunar dani tace "twins ku fito min da ita".

Kit d'in make-up naga sun d'auko cikin sauri nace "no!", Dariya sukayi gaba d'aya Raudah tace "dan Allah Bilki ki daure kiyi kwalliya ko yaya ne ki dan fito Kinga dare ne, kuma there is no way zamu fita dake a haka mu kallemu, ai it's not fair".

Kallon hannuna nayi na d'ago nace "Aunty Raudah ba wai bana son make-up bane, kawai it's inappropriate nayi at this time".

D'aga girarta tayi tace "saboda me? Idan kina tsoron kar wasu maza suyo kanmu ne karki damu munada ya Aalee, bayan haka ba yawo zamuyi ba, muna cin shawarmannan muka d'an zagaya dawowa zamuyi, ba lallai ma 10 tayi mana a waje ba".

"Ba tsoron wani abu nake ba, nidai mu fita kawai ba sai nayi wani make-up ba please".

"No" ta fad'a tareda hard'e hannunta a 'kirji".

Murmushi nayi nace "Aunty Raudah da aure a kaina bazan fita da kwalliya haka ba zunubi ne zai hau kaina".

Shiru tayi ta zubamin ido ina ganin tambayoyi kala kala a fuskarta amma ta kore tace "okay, amma ai ko powder da d'an light janbaki kya saka ko kuwa hakanan zaki fita?"

Komawa nayi na zauna na d'auki powder, kar'ba d'aya daga cikin twins tayi, ko yaushe zan fara ganesu? Shafamin tayi ta d'auko janbaki red ta shafamin sannan tayi contouring yanda kalarsa zata ragu, d'ayar twin d'in kuma ta kama gashina tana tajewa, sun juyar da fuskata daga madubin saboda haka bansan me suke aikatawa ba, mayafin rigar tawa suka d'auko naga sun had'a Ido, yarannan sun iya magana ta ido sosai, ajiye mayafin mai tajemin gashi tayi ta d'auko wani silver kalar kwalliyar rigar ta fara min rolling d'insa saida suka gama sannan suka ce na kalli kaina a mudubi, ni kaina nasan nayi kyau ga mayafin ya sauka yanda zai rufe jikina dukda rigar bata bayyana jikina ba, duk da haka ji nake kamar na karya dokar shari'a, kafin na gama tunani Raudah tace "selfie" kafin na ankara ta d'aukemu, ina kallon kaina a mirror twins kuma na kallona ta gefe, pic d'in yayi kyau amma dukda haka saida twins sukayi kanta ta d'aukesu basu shirya ba.

8:20 mun gama komai mun fita, suna ri'ke da jakunkuna ina ri'ke da purse, gaba twins sukayi zasu kira Aliyu suka barni da Raudah a palour, d'inkin jikinta na kalla nace "d'inkin ku yayi min kyau".

"Tailor d'in namu kuwa anan yake idan kinaso sai na had'a ki dashi". Ta fad'a tareda d'aukan jannat ta d'aurata a cinyarta, sai yanzu na lura suna kama sosai da jannat twins kuma sunfi kama da Aliyu sannan sha'kuwar jannat da Raudah tafi yawa, rufe idona nayi nace "Allah sarki Huda". 

"Wacece Huda? Ur baby?" Kallonta nayi domin bansan taji maganar da nayi ba nace "sort of".

'daga gira tayi tana jira naci gaba twins suka shigo, kallonmu Aliyu yayi yace " 'yammata na kunyi kyau fa, yau zansha fama da mazaje kenan don hanasu kallonku" ya fad'a tareda d'aukan jannat ya fara kissing fuskarta tana dariya, kallona yayi yace "Aunty Bilki zaki ara mana motarki da ita zamu fita".

NAYI DACE.Where stories live. Discover now