49

568 30 0
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@ mamsuhaimerh

*49*Bayan zuwan ambulance na sanar musu ba wani abu bane, banda ma shirmen Aliyu kawai daga fara amai zai kira min asbiti?

Bayan sun dubani sun tabbatar babu wata matsala suka bani magani a cikin motar sannan suka sallamemu muka tafi.

Muna zuwa gida zazza'bi ya rufeni gaba d'aya hankalinsa Aliyu ya tashi, da alamun bai ta'ba ganin marar lafiya ni kuwa baisan dad'in hakan nakeji ba nima na fara jina a mutum.

Kashe AC d'in d'akin yayi ya kunna min heater tare da lullu'bata, dafa kaina yayi yace "sannu Bilkisu ya kikeji?"

"Dad'i" na fad'a tareda 'kudundune jikina, wani kallo yayimin yace "lafiyarki kuwa? Ya mutum yana ciwo zaice yana jin dad'i? Wai kinsha maganin da aka baki ma kuwa?"

Tashi nayi na zauna na jingina a kafad'arsa nace "ya Aalee ba dole naji dad'i ba? Wannan wahalar da zan sha itace zata sanyawa 'ya'yana tausayina, ba wannan ba ma wannan shine first and last time da zanyi laulayi this is so important to me, indai maganin zai hanani ciwon ne to bazan sha ba, wannan shine stage na farko a motherhood kuma banaso nayi skipping".

Shafa kaina yayi yace "Bilkisu bansan ya kikeji ba amma cuta ko ya take batada dad'i idan ciwon yayi yawa zaiyi affecting babies d'inmu ko kuwa? Banaso a samu matsala".

"Babu matsalar da zamu samu da yardar Allah, mata da yawa suna shan wahalar da tafi tawa wata sai an kwantar da ita a asbiti, wata tsabar ciwo fita hayyacinta takeyi, nawa me sau'ki ne fa".

Maganin ya d'auko daga kan bedside drawer yace "to ki daure kisha ba lallai maganin ciwon zai miki ba amma zai rage miki ko da zazza'bin ne, tunda muka dawo ko ruwa baki sha ba gashi abinda kika ci ya dawo kisha magani sai kici abinci yanda suka ce".

Kar'bar maganin nayi nace "okay zansha to d'aukomin ruwa please".

Yana tashi na ciro maganin, bayan na duba naga vitamin ne na yanke shawarar sha, d'ayan kuwa 'boyewa nayi.

Bayan nasha ya fara tambayata me zanci, sunayen abincin da yake lissafowa ne suka sanyani amai da gudu na tashi na nufi toilet.

Ko sunan abinci banason naji ga yunwa tana addabata amma ko zakici yacemin sai naji zuciyata na tashi, malt na samu nasha kafin na kwanta, itama ina bacci ta tasomin na tafi na amayar.

Washegari da safe mukayi waya da Mama, ban sanar mata ba so nake na bata mamaki idan na koma gida naje saidai ta ganni da abuna, Mum ma yacemin kar na sanar mata domin basu san za'ayi min aikin ba.

Bayan two weeks muka koma aka duba babies suna lafiya lau, a ranar muka baro Dubai domin 'kasar ta isheni, cikina har ya fara fitowa amma kayan da na saka basu bayyanar dashi ba

Ko da muka shiga jirgi hannun Aliyu na kan cikina, shi gani yake laulayin da nakeyi zaiyi affecting cikina saida na sanar masa yanda abun yake lafiyarsu ce ta sanyani hakan tukuna ya barni na huta.

Muna isowa gida naji wani annushuwa, twins na hango suna d'ago mana hannu muka 'karasa wurinsu, a tare sukayi hugging d'ina suna tsalle na cije baki domin sun danne min babies d'ina amma ban nuna ba, Aliyu yayi 'ko'karin janyesu nace masa a'a.

Bayan sun sakeni muka gaisa da Raudah, itama hugging d'ina tayi tace "lallai Dubai ta kar'beki kinga yanda kikayi fresh kuwa?"

Murmushi na mata ba tareda nace komai ba na nufi Mum, dur'kusawa nayi ya d'agoni tareda hugging d'ina tace "welcome home".

Turarenta ne ya daki hancina naji amai na tasomin, 'ko'karin dannewa nakeyi amma na kasa da sauri na bar jikinta na nufi wurin da zanyi.

Gaba d'aya wurina suka yo cikin damuwa Mum ta dafani tace "sannu Bilkisu dama...." Tsayawa tayi da maganarta ta fara 'karemin kallo, wani faffad'an murmushi ta saki na sunkuyar da kaina, Raudah ganin yanayin mum yasa ta zare ido tace "OH...MY...GOD!!"

NAYI DACE.Where stories live. Discover now