31

514 26 0
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@ mamsuhaimerh

*31*
            "Allah ya kyauta Kuma Allah yasa haka ne mafi alkhairi". Mama ta fad'a bayan min day lokaci shiru, amsawa nayi da amin ina goge hawaye na, ledar cake d'in da na shigo da ita na d'auka na bud'e na fara ci dukda Kuka nake, dariya mama da jabir sukayi Wanda ya sanyani murmushi, har na manta da wannan bilkisun mai sauke 'bacin ranta a kan abinci, wadda bata ri'ko Bata bari abu komai girmansa ya dameta, matu'kar Zan kai abu bakina zance ya 'kare.

Kallona sukeyi yanda nake sauke 'bacin raina kan junk food d'in dake gabana, a duk loma idan na kai maganganu nake a zuciyata Wanda bazan iya furtasu ba, janye ledar mama tayi tace "Kar Kuma kici wanda zakiyi amai".

"Amma mutane basuda halacci, duk taimakon da na yiwa Saleh baiji kunya ba ya sako 'kanwata? To mama ko dukansa takeyi ya saketa? Ai ya duba girmanku da mutuncin dake tsakanina dashi, sai ya san ya wula'kanta 'kanwata".

Girgiza kai nayi cikin sauri nace "a'a Yaya Dan Allah Kar kayi haka ba girmanka bane, ko dan abotar dake tsakaninku ka rabu dashi dan Allah Kar kayi masa magana ka nuna tamkar ba abinda ya faru,wannan tsakanina dashi ne banaso ka shiga da kansa zai san yayi kuskure".

Wani irin kallo jabir yayi min yace "har kin fara tunanin komawa gidansa kenan ko?"

Shiru nayi na zubawa hannuna ido, banaso ko hanyar gidan Saleh na sake bi, amma tsabar rashin zuciya irin nawa akwai tiny hope na gobe da safe Saleh zaizo ya bani ha'kuri mu koma zaman lafiya, me yake damuna ne? Wannan itace soyayya? Wani irin so nake ma saleh haka? Wace irin zuciya ce dani?

"Amma bilkisu kin bani mamaki bakida zuciya ko kad'an wallahi, mutumin da ya zageki ya zagi iyayenki ya sakeki ba tareda tunawa da zaman da kukayi dashi ba, ba tareda tuna zaman da nayi dashi ba har shi kike tunanin komawa gidansa? Bilkisu da nasan abinda zai faru kenan da ban goyi bayan aurensa ba, da Abdul Zaki aura ko kinaso ko bakyaso, ko ba komai d'an uwane bazai ta'ba wulakantaki ba musamman yanda yaga gatan da kike ciki".

"Yaya ni ba so nake na koma ba fa, kawai banaso ne wannan abin ya shiga tsakaninka dashi banaso hakan ya ta'ba ala'karka dashi".

Tashi tsaye yayi yace "idan har bakyaso hakan ya ta'ba ala'kata dashi ki barni nayi magana dashi, idan har na kauda kaina bazan ta'ba yafe Masa ba".

Fita yayi ya barni a zaune, mama kuwa tunda muka fara maganar ta tashi, jikina a sanyaye na shige d'aki na shimfid'a bedsheet na kwanta, Saleh zaizo bikona kuwa? Shin zaiyi nadamar sakina? A Daren yau zai iya bacci babu ni a gefensa? Nima zan iya bacci babu Saleh a gefena? Tambayoyin da suketa yimin yawo kenan har nayi bacci.

************
*SALEH*

Wani numfashi ya sauke bayan kalmar saki ta fita daga bakinsa, bai ta'ba tunanin ko da wasa zai saki Bilkisu ba amma gashi yau lokaci yayi, yasan cewa su hajiya basa sonta amma wannan karan bazai ta'ba yiwuwa ya goyi bayanta ba bayan yaga laifinta da idanunsa sannan ta d'aura laifin kan 'yan uwansa har ta kai ga zagin hajiya, tunawa yayi da maganar da hajiya ta fad'a masa wadda kusan ita ta tunzurashi ya saki bilkisu

Bayan sunyi hayaniya ya fita part d'in hajiya ya nufa, Hira ya samesu sunayi akan abinda ya faru, tsayawa yayi a inda yake tunanin bazasu hangoshi ba, baisan cewa zuwansa ne ya Ssanya suka fara maganar ba, ji yayi maimuna na cewa "Wallahi nayi mamakin bilkisu, nasan Bata sonmu bata son rayuwarmu, amma me zai kaita aikata haka? Ita kenan kowa ma ya mutu idan zata samu haihuwa , bata tunanin cetar ran amir zai iya sanya Allah ya kawo mata komai cikin sau'ki, Kuma babu kunya babu tsoron Allah tace Bata san ya kud'in suka shiga gidan ba".

"Hm, ai da ace ma yasan me tace mana da ta kawo kud'in da bai tsaya tantama akai ba, kin tuna kallon tsabar idon hajiya tayi tace "idan har Kina haka ne Dan ki rabani d'anki idan ya rabu Dani ya aureki sai kije kiyita haihuwar dashi, wace macece mai tarbiyya zata fad'awa uwar mijinta haka?" Kursum ta fad'a Tana murmushin mugunta domin duk motsin Saleh sunaji.

NAYI DACE.Where stories live. Discover now