29

426 20 0
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@ mamsuhaimerh

*29*
             Bansan dad'ewar da nayi a d'akin ba, kabbarar sallah naji na tashi domin bansan anyi Kiran sallah ba, na shiga zurfin tunanin yanda kud'in ya dawo gidana, duk da Saleh ya wula'kantani amma ba duka ne laifinsa ba, idan har Zan Sanya kaina a matsayinsa bazan yarda da kaina ba.

Ranar da na kai musu kud'in ban bar gida ba haka ma washegari babu inda naje, a cikin kwanakinnan ban fita ba sai yau ko dai bayan sun tsaida ni suka Sami damar shigar da kud'in cikin gidana? To ta yaya? Key yana hannuna shima Saleh key d'insa na hannunsa, ko dai sunyi amfani da key d'in jumana ne tunda duk lock d'in namu iri d'aya ne?

To waye zai shigo ya ajiye kud'in bayan ina tare dasu a tsaye? Ko dai Jumana suka baiwa wannan aikin? Amma sam babu alamun an shiga gidan lokacin da na shiga, su dai bazasu yi aiki da aljanu akan wannan 'karamin abun ba.

Kaina ne ya fara saramin saboda yawan tunani, saidai na kasa kautar da tunanin a raina, babban abinda ke d'aga min hankali shine yanda zuciyata ke neman Kare Saleh bayan duk abubuwan da ya fad'amin, want irin so nakewa Saleh da nake neman cutar da kaina a kansa? Tunda nake ban ta'ba ganin 'bacin ransa kamar yanzu ba, sannan tunda nake a duniya ban ta'ba jin d'acin maganganu kamar wad'anda suka fita daga bakinsa ba, danginsa sun zageni sosai da maganganu masu zafi, amma Basu ta'ba min rad'ad'in da maganganun Saleh suka yimin ba, amma idan har na duba a mahangar tunani yanada ikon yin haka, iyayena ne kad'ai zasu yarda dani a irin wannan lokaci ko 'yan uwana b kowa zai yarda dani ba, saboda haka na 'kuduri sake magana da Saleh a karo na 'karshe nasan mijina yana sona duk abinda yayi cikin 'bacin rai ne.

Bayan Nayi sallar azahar na d'auko wayata, missed call d'in mama na gani domin tun 11 na kirata nace mun fito, a yanzu bazan iya kiranta na fad'a mata wannan matsalar ba har sai naga tafi 'karfina Wanda bana fatan hakan ya faru.

Tashi nayi saboda 'karfin hali na d'aura girki, empty nake jina ko kukan da zanyi naji sanyi a raina babu hali, girkin da nake absent mindedly nakeyi ko 'kamshin banaji a hancina.

Canza kayan jikina nayi zuwa marasa nauyi na zauna jiran saleh, sa'ka nake a raina ina warwarewa har naje conclusion, d'ayan biyu ne ko dai ya fahimceni y yarda dani ko kuma ya d'auki matakin da ya dace a kaina, bazan sake bari ya zageni akan gaskiyata ba, wai nice Mai son zuciya bayan ga tsantsar son kai da son zuciya a wajen danginsa.

'karan motarsa naji alamun ya fita, tuntuni yana tareda munafukan 'yan uwansa kenan, a kujerar na kwanta har la'asar, alamun dawowarsa naji amma bai shigo gida ba, ajiye motarsa yayi ya tafi har Isha, damuwa da 'bacin rai sun had'emin sai sauke numfashi nakeyi ina runtse idona.

Sai 8:40 ya shigo, Yana sallama ya nufi bene ba tareda ya kalleni ba, binsa nayi a baya yana zama ina shiga d'akin. "Boo-boo ya kamata muyi magana".

"Kallona yayi idanunsa har yanzu na nuna 'bacin rai, murmushin takaici yayi yace "wace magana zamuyi kuma? Ai mun gama magana".

Kujerar mirror naja na zauna nace "zamuyi magana ne irin ta masu hankali ba maganar da zamu dawo daga baya muna nadama ba"

"Sunce zakiyi haka ai" ya fad'a can 'kasan ma'koshinsa da alamu baisan naji ba, controlling kaina nakeyi kafin na fashe domin Nima na fara zuwa bango, had'e hannuna nayi nace "su waye sukace zanyi haka? Bayan wannan 'kazafin kuma me sukace na aikata? Boo-boo meyasa bazaka gane intension d'insu a kaina ba? Burinsu su rabaka dani su rabaka da farin cikinka, idan har suna sonka zasu so abinda kakeso amma dubi tunda nazo suke nunamin 'kiyayya har takai ga sunyimin wannan sharrin, meyasa ba zakayi tunani irin na masu hankali ba kaga inda wannan abun ya dosa?"

"Kina nufin duk abinda nayi a cikin hauka ne? For the last time Bilkisu stop dragging my family into your mess, danginka danginka, komai dangina har a yanzu da suke fafutuka da mara lafiya laifinsu kike gani, sai yaushe zaki fara hangen laifinki ki dena ganin na dangina?!!"

NAYI DACE.Where stories live. Discover now