10

615 34 0
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@mamsuhaimerh

*X=10*
            D'auke kaina nayi daga gareshi nace

"Idan baka amince Dani bane kaima mu tafi asbiti,iya zama na dakai ya kamata ace kasan abinda Zan iya da Wanda bazan iya ba,ko baka sani ba a matsayinka na mijina nauyinka ne ka goyi bayana a gaban danginka ko ma me zamuyi a bayan idonsu mayi"

"Amma yanda suke nunamin rashin soyayya kaima a gabansu baka nuna ka damu Dani,ko Ni na bud'e Baki nace nayi planning zaka yarda?Kai kasan yanda Allah ya jarabceni da son 'ya'ya,da akwai yanda zanyi na d'auko ciki na saka a jikina wallahi ko wane Hali ne zanyi,Amma Allah yayi time Dina baiyi ba,muje asbiti kawai a dubani ka kauda zarginka,da na Yan uwanka Nima na samu sukuni"

Takunsa naji ya matso kusa Dani,kasa juyawa nayi na kalli fuskarsa Domin Raina a bace yake sosai,cikin lallashi yace

"Ba wai ban yarda dake bane boo, kawai maganar ce tazo kin bazata"

"Indai zaka dinga d'aukan maganar Yan uwanka haka wataran kashe Mana aure zasuyi,nasan bakaso na fad'a Amma boo-boo Yan uwanka basa Sona hka ma mahaifiyarka,sau d'aya ka amince da hakan ka nuna gskiya na fad'a,kayi backing Dina up a gabansu,idan kana barina da wayona a cikinsu wataran bazan tsira ba,inaga ma rashin kwanciyar hankali ne ya hanani samun ciki"

Hugging Dina yayi ta baya yace
"Sorry dear,ya wuce kiyi ha'kuri"

"Bai wuce ba boo-boo,shekara d'aya hajiyarka ta bamu saboda bata aminta Dani ba,muje asbiti Dan Allah ko ma zo Mata da result ba cewa Babu planning a jikina"

Juyoni yayi ya kalli cikin idona yace

"A'a boo,Babu inda zamuje,na yarda dake Ni kadai na Isa na zama shaida,wata shida kawai bai Isa ace mun fara yawon asbiti ba,nasani lafiyarki kalau lokaci be baiyi ba,sannan wannan shafaffen cikin naki dama ai bazai d'auki baby ba saboda haka ki dage da cin abinci har babynmu ya samu space ya zauna"

Murmushi nayi na jin dad'i,hannuna ya ri'ke muka shiga d'aki take ya canza hirar

Bayan Saleh ya fita masallaci da magrib sai ga sultana,tun kafin ta shigo Palo tace

"Dan Allah bilki kiyi ha'kuri,wallahi bansan haka zai ja maki matsala ba da na kame bakina,naso na fahimtar dasu Amma sun kasa fahimta,kiyi ha'kuri kinji?INSHA Allah Zaki Basu kunya duka,dukda Yan uwana ne bana son abinda suke maki wallahi"

Murmushi nayi nace

"Bakomai sultana,nasan ba da niyya kikayi ba,Kuma wallahi ya wuce a wurina.kawai...."

"Daga yanzu Zan iya bakina ba sai kin fadamin ba,duk abinda ya gudana tsakaninmu iya Nan zai tsaya na maki al'kawari"

Murmushi nayi Amma zuciyata ta fara waswasi akan sultana,a zamana na San labarin soyayyar sultana da Saleh

Sultana cousin din Saleh ce,mahaifiyarta da hajiya uwa d'aya uba d'aya tun daga yaye aka kawota wajen hajiya,tunda tazo tafi yarda da Saleh akan kowa,hatta hajiyar ma,hakan yasa ta taso cikin shakuwa da Saleh tamkar yayanta

Lokacin da ta fara girma hajiya ta fara tsokanarta da amaryar saleh,tun Tana Kuka har ta fara sabawa,a haka Kuma sai ta fara Jin soyayyarsa na shigarta,ta boye Bata fad'a ba Ashe hajiya ta lura da hakan

Shi Kuma gogan Yana can Yana rainona,Nima na taso ya furta Yana Sona,Mahaifiyar Saleh da ta sultana sukayi magana ba tareda saninsa ba Akan an bashi sultana,baa tashi sanar Masa ba saida suka fara shirin fidda ranar aure,da farko ya amince said yaga bazai iya ha'kura Dani ba sannan ya bijirewa umarninsu

Bai bani labarin dramar da akayi Kan haka ba yace dai ran kowa ya baci Amma da maza suka shiga lamarin Dole su hajiya suka hkura,sultana har ciwo tayi daga baya hajiya tace ta hadata da Usman saboda ran mahaifiyarta ya baci,babu musu ta amince

NAYI DACE.Where stories live. Discover now