A KAN ƊA....
Na
Hauwa'u Salisu
( Haupha)Page 1
Duk wanda ya san mal Tanko yasan bai da burin da ya wuce ya samu haihuwar ɗa namiji ba mace ba, yana da mata guda ɗaya mai suna Hanne shekara goma da aurensu bata taɓa ko ɓatan wata ba , gashi bai da dukiyar da zai nemi taimako asibiti saboda noma yake shima dan kar ace baiyi ne abu na gadon kaka da kakanni, rannan ya ji labarin wani Boka da ke yamma da ƙauyensu dan haka ya tasa Hanne gaba zuwa gun Bokannan da fatan Allah yasa yasamu taimakon da yake so na samun ɗa namiji ko da guda ɗaya ne, cikin sa'a suka samu Bokan wanda sai da Hanne ta nemi rugawa dan tsoro, sai dai sharuɗɗan da ya basu ne abin da ya girgiza zuciya da ruhinsu musamman ita Hanne da bazata ga abin da ta haifaba. Shima Mal Tanko an mai albishir daya sa ya kasa natsuwa domin ga koshi ga kwanan yunwa lamarin ya zama garesu. Ko me aka gaya masu ?
Haupha ce 🙋
YOU ARE READING
A KAN ƊA....
Short StoryGajeren labari ne na Malam Tanko wanda bai da burin da ya wuce ya samu haihuwar ɗa namiji bai san mace, kwatsam ya samu labarin wani Boka wanda bai ɓata lokaci ba ya tasa matarsa Hanne zuwa gun Bokan,an tabbatar masa da buƙatarsa zata biya amma fa s...