A KAN ƊA page 8

65 8 0
                                    

A KAN ƊA....

   Na

Hauwa'u Salisu
       (Haupha)

       Page 8

Cikin farin ciki Tanko ya shiga ɗakin bakinsa ya kasa rufuwa hakan yasa ya manta da sallama, ya afka ciki kawai da burin ganin Amarya Indo. Tana zaune kan gado ta ƙudundune jikinta baki ɗaya bai iya ganin ko da yatsanta, cike da jin daɗi ya fara mata magana "Wato Indo naji daɗi sosai da aurenki hakan yasa na fahimci ni namiji ne ba ƙaramin jarumiba, domin da ina da tsoro da yanzu ban aure ki..yasa hannu ya janye mayafin data rufe jikinta, ƙafafuwanta suka fara bayyana, idan ba gizo idanunsa ke masaba kafar Indo ta koma kofaton doki kafcece, hakan yasa ya ɗago ya kalli fuskarta,baki ɗaya ta juye zuwa wata baƙar mace mai ido ɗaya a tsakiyar goshi hanci guda sai uban baki da wasu manyan haƙora tana ta wasa da shirgegen maciji a hannunta.Gaba ɗaya numfashin Tanko ɗauke wa yayi ya zube gun a sume.
Dauda na tsugunne gaban dodonsa cikin daren yana jiran umarnin abin da zai bashi, ya ga dodon ya zabura yayi ƙara mai tsoratarwa, hankalinsa ya tashi dan yasan idan yayi hakan wani mummunan lamarine tafe.
Auwal nata barci abinsa bai san abin da ke faruwa ba.

Kome zai faru idan Tanko ya farka?
Ko wane lamari ne zai faru ga Dauda?

Ina godiya gareku yanda kuka nuna farin cikinku gareni ranar Birthday Na👏
Haupha ce 🙋

A KAN ƊA....Where stories live. Discover now