A KAN ƊA page 2

99 6 0
                                    

A KAN ƊA....
             Na

Hauwa'u Salisu
       (Haupha)           

        Page 2

Boka ya dubi Mal Tanko rai ɓace yace " Ba wanda ke zuwa gunmu da neman biyan buƙata ya fasa ko dan haka kawai ku saurari sharuɗɗan da zan gindaya maku kawai" ban da hawaye babu abin da Hanne ke yi dan da gaske ba zata aminta da sharaɗin Bokanba akan me zata rasa rayuwarta kan yaron da bata haifaba bama ta da tabbacin yazo da rai ko babu, Boka ya dude su yace " Tabbas zaka haifi yaro amma randa aka haifesa matarka zata mutu kai da aure har abada kuma sannan zakai kuɗi amma babu rabon yaron aciki duk randa ka ɗauki sisi ka bashi zai mace nan take hakama duk wadda ka aura zata ɓace, sannan kullum zamu aiko ma da Aljanar da zata biyama buƙatunka, nomanka zai shahara wani hatsin shine zai zama takin wani hatsin" Boka na gayama maganar ya ɓace shida bukkarsa baki ɗaya.
Tunda daga ranar Hanne ta fara laulayin ciki mai ban al'ajabi da mamaki ainun wanda yasa mutane fara tunanin anya kuwa lamarin cikin Hanne akwai abin kirki? Ranar wata Lahadi da dare wata farar Bafulatana ta bayyana ɗakin nasu jajir da ita kanta ɗauke da ƙwaryai nono tace "Yaune alƙawarin Boka zai cika Hanne zaki bada ranki fansa ga yaron cikinki" basu ankara ba ta ɓace nan ta ke Hanne ta fara jin alamar ciwon mara ƙugu baya kan kace me ta fita hayyacinta hakan yasa Malam Tanko ruwagawa neman ɗauki, sanda suka dawo suka iske yaro kwance Hanne ba rai jikinta.
Malam Tanko ya dafe kansa yana jin farin ciki da baƙin ciki lokaci guda.
Ranar suna aka sama yaron suna Auwal wanda mutane sun yi mamakin inda malam Tanko yasamo katon rago da hatsin da akai dudumar sunan, iyayen Hanne sun nemi ya basu yaron ya hana haka suka haƙura.
Sannu a hankali makwabtan malam Tanko suka fara kula da wani lamari dake faruwa a gidan ya hana kowa shigar masa gida ko da almajirine amma duk ranar duniya wata farar Bafulatana tana zuwa kai tsaye ta shige gidan cikin tsakiyar rana, da ta fito kuma tasha kwana ba mai sake ganinta....

Haupha ce 🙋

A KAN ƊA....Where stories live. Discover now