A KAN ƊA....
Na
Hauwa'u Salisu
( Haupha)Page 5
Dauda ya shige gidansa hankalinsa ya rabu kashi biyu, ga ƙoshi ga kwanan yunwa, haƙiƙa ba shine ya haifi Indo ba amma yanda yake sonta ko ƴaƴansa da ya haifa bai so, sai dai tun da jimawa dodonsa ya tabbatar masa da cewa Malam Tanko zai haifi yaro wanda jininsa kawai zai sha Dauda ya zama hamshaƙin attajiri a fagen sai da Auduga (kaɗa)han yasa kwanaki yaita bibiyarsa bai samu damar abota da shiba yau ga dama ta samu.
Mal Tanko na shiga cikin gidan kai tsaye ɗakinsa ya nufa jikinsa na kyarma fuskarsa ta juye tsantsar ɓacin rai, yana shiga kuɗin ya kalla ya kwaɗa kiran Auwal wanda ke niyyar fita waje jiran mai yalo, cikin sauri ya isa kofar ɗakin uban yana amsa kiran, kyakykyawan mari uban ya bashi a fuska ya dubesa a fusace yace "Yaushe ka fara karya magana ta ? Bani kuɗin da ka ɗauka dan ubanka. Cikin sanyin jiki Auwal ya bashi kuɗin ya fice kofar gida da gudu yana kuka, fitarsa ke da wuya ya hango wasu baƙi sunzo makwabtansu harda wani yaro dai-dai shi, wancan yaron ganin Auwal na kuka yasa ya fasa shiga gidan da suka zo ya rugo ga Auwal yana tambayarsa "Me kake ma kuka ne? Auwal kukansa kawai yake musamman da ya ga mai yalo yazo zai wuce,cikin sa'a yaron ya siyo yalon naira goma ya ba Auwal ɗaya ya ɗauki ɗaya,sai Auwal ya bar kuka suka koma cin yalo suna tambayar juna sunayensu.Daga cikin gidan wani ya fito kiran Ahmad ganinsa da Auwal har suna cin yalo yasa mutumin komawa ciki da gudu yana ihun Ahmad ya kashe kansa yau!
Dai-dai lokacin ƴar fulanin nan ta shawo kwanar gidansu Auwal kai tsaye ta taɓa su ta wuce cikin gidan, Auwal da Ahmad suka kalli kofar gidan suka kalli juna tamkar haɗin baki suka nufi gidansu Auwal ɗin kai tsaye.
"Tanko baka isa ka ja da maganar mu ba idan kace zaka ja da mu tabbas zaka ga bala'i da musiba kala daban-daban ga rayuwarka sannan yaronma zamu kwacesa mu salwantar" ban da kyarma babu abin da Malam Tanko ke yi tsugunne gaban ƴar fulanin ya kasa ko da furta kalma ɗaya.Haupha ce 🙋 5
Dauda ya shige gidansa hankalinsa ya rabu kashi biyu, ga ƙoshi ga kwanan yunwa, haƙiƙa ba shine ya haifi Indo ba amma yanda yake sonta ko ƴaƴansa da ya haifa bai so, sai dai tun da jimawa dodonsa ya tabbatar masa da cewa Malam Tanko zai haifi yaro wanda jininsa kawai zai sha Dauda ya zama hamshaƙin attajiri a fagen sai da Auduga (kaɗa)han yasa kwanaki yaita bibiyarsa bai samu damar abota da shiba yau ga dama ta samu.
Mal Tanko na shiga cikin gidan kai tsaye ɗakinsa ya nufa jikinsa na kyarma fuskarsa ta juye tsantsar ɓacin rai, yana shiga kuɗin ya kalla ya kwaɗa kiran Auwal wanda ke niyyar fita waje jiran mai yalo, cikin sauri ya isa kofar ɗakin uban yana amsa kiran, kyakykyawan mari uban ya bashi a fuska ya dubesa a fusace yace "Yaushe ka fara karya magana ta ? Bani kuɗin da ka ɗauka dan ubanka. Cikin sanyin jiki Auwal ya bashi kuɗin ya fice kofar gida da gudu yana kuka, fitarsa ke da wuya ya hango wasu baƙi sunzo makwabtansu harda wani yaro dai-dai shi, wancan yaron ganin Auwal na kuka yasa ya fasa shiga gidan da suka zo ya rugo ga Auwal yana tambayarsa "Me kake ma kuka ne? Auwal kukansa kawai yake musamman da ya ga mai yalo yazo zai wuce,cikin sa'a yaron ya siyo yalon naira goma ya ba Auwal ɗaya ya ɗauki ɗaya,sai Auwal ya bar kuka suka koma cin yalo suna tambayar juna sunayensu.Daga cikin gidan wani ya fito kiran Ahmad ganinsa da Auwal har suna cin yalo yasa mutumin komawa ciki da gudu yana ihun Ahmad ya kashe kansa yau!
Dai-dai lokacin ƴar fulanin nan ta shawo kwanar gidansu Auwal kai tsaye ta taɓa su ta wuce cikin gidan, Auwal da Ahmad suka kalli kofar gidan suka kalli juna tamkar haɗin baki suka nufi gidansu Auwal ɗin kai tsaye.
"Tanko baka isa ka ja da maganar mu ba idan kace zaka ja da mu tabbas zaka ga bala'i da musiba kala daban-daban ga rayuwarka sannan yaronma zamu kwacesa mu salwantar" ban da kyarma babu abin da Malam Tanko ke yi tsugunne gaban ƴar fulanin ya kasa ko da furta kalma ɗaya.Haupha ce 🙋
YOU ARE READING
A KAN ƊA....
Short StoryGajeren labari ne na Malam Tanko wanda bai da burin da ya wuce ya samu haihuwar ɗa namiji bai san mace, kwatsam ya samu labarin wani Boka wanda bai ɓata lokaci ba ya tasa matarsa Hanne zuwa gun Bokan,an tabbatar masa da buƙatarsa zata biya amma fa s...