A KAN ƊA page 11

75 7 0
                                    

Cike da mamakin yanda gidan ya koma suffar kunkuru suka dubi ogan nasu dake masu jawabin kowa ya fito da layunsa da tsuminsa, anzo inda shiri zai amfani. Duk sun aminta nan da nan suka fara fiddo layu suna ɗaurawa a damtsen hannuwansu wasu na saka laya cikin baki suka tunkari ƙaton kunkurun suna jin cewar suma wasu hatsibabaine a fagen iya shegen.

Duk abin da suke yana kallonsu, ya dubi ɗakin Indo da Auwal take wani hayaƙi ya fita daga idanunsa ya shige ɗakunan, barcinsu ya koma na doguwar suma.

Ya sake kallon ƙofar gidan, sai ga hanya ta samu da kanta.

Ɓarayin kuwa suna gama shirinsu ogan nasu ya dubi kunkurun da idanunsa wani haske ya fito ya shige jikin kunkurun take sai ga ƙofar gidan ta bayyana. Ihu suka saka suna cewa " Ashema ƙaramin taƙadarine mai gidan, suka faɗa cikin gidan kai tsaye suna dube-dube.
Yana zaune suka wuce shi ba tare da sun ganshi ba, kai tsaye ɗakin da yake aje kuɗi suka nufa, ba ƙaramin mamaki sukai ba ganin kuɗi har wasu sunyi Gara wasu sun lalace tsabar ajiya, wasu kuwa sabbi dal dasu kamar yanzu aka fito dasu daga banki.
Jakunansu suka kwanto suka cika da kuɗi har suna zuba sannan suka shiga ɗayan ɗakin, shi kuma hatsine cike cikinsa shima wani ya lalace wani duk Gara ta kamasa sukai matuƙar maamkin mai gidan da abin da yake aikatawa ya tara wannan dukiya da uban hatsi haka a cikin gidan .

Har sun kai kofa sai wani mai zalama ya koma wai zai sake zubo kudin a cikin rigarsa tunda jakarsa ƙarama ce sauran suka fice, suna fita kofar gidan ta rufe ta shafe kamar ba'ayita ba a wajen.

Cikin wani yanayi mai kama da ɓacin rai Tanko ya bayyana ya dubi ɓarawon yace "Daman jini nake buƙata dan haka ka zama gawa, jininka ya zama abin sha ga boka Burgam uban duk wani matsafi. Nan take ɓarawon ya fara kyarma, yana murza layar dake ɗaure a damtsen hannunsa, amma abin mamaki bai ɓace ba kamar yanda yasaba duk sanda ya murzata ɓacewa yake yi .
Tanko ya kwashe da dariya kafin ya nuna wata wuƙa ƙarama mai kaifi da haske da hannu, nan take wuƙar ta bi iska ta shige maƙoshin ɓarawon ya faɗi ƙasa ba rai.

Ya bushe da dariya yace "Na rantse da Allah sannu a hankali zan dinga shayar da boka Burgam jinin mutane har sai yayi mun afuwa ya barni da matata Indo abar sona.

Su kuwa ɓarayin suna fita waje suka fara zazzage kuɗaɗen suna murna suna ihu, karshe suka manta da wanda ya koma suka kwashe kuɗin suka nufi ƙauyensu, kofar gidan duk kuɗi warwatse a ƙasa dubu-dubu ko lankwasa babu .

Ku biyoni gaba dan jin ya zasu kwashe.

Haupha ce

A KAN ƊA....Where stories live. Discover now