A KAN ƊA page 6

68 8 0
                                    

A KAN ƊA.....

       Na

Hauwa'u Salisu
    ( Haupha)

    Page  6

"Tanko zan sake maimaita maka sharuɗɗan Boka dan naga alamar ka manta su, acikin sharuɗɗan an gayama babu kai ba ƙara auren kowace mace Ni kaɗai ce matarka dan haka ka kiyaye son wata inba Ni ba, na biyu karka kuskura kaba yaronka sisi daga wannan dukiya da muka mallaka maka duk randa ka bashi sisi to ransa ne ka bashi ya kashe da kanka. Cike da razana ya dube ta " ki taimaka kimun lamunin auren Indo ko da ace shine lamuni na ƙarshe da zaki mun Zillaziyya kin ji ? Bata saurare sa ba ta fice daga ɗakin ta bar gidan. Kan idon su Auwal ta fice dan haka da gudu suka bi bayanta abin da yayi masu daɗi shine ko waige bata yi mai nonon, sai dai tana shan kwanar farko ta anguwar ta ɓace masu bat. A razane suka dubi juna tare suke tambayar juna "Tana ina ? Ba mai amsar dan haka suka dawo gun zamansu suna tattauna yanda za suyi su samu kuɗi gobe kasuwar garin su ciwo kasuwa, wanda Auwal jinsa yake tamkar yana aljanna ya samu abokin da zai kaishi kasuwa bai taɓa barin cikin anguwar ba tun tasowarsa.

Abin duniya ya bi ya damu mal Tanko yana hango fuskar Indo yana jiyo amon muryai Aljana Zillaziyya cikin dodon kunnensa, yana cikin halinne Auwal ya zo ya gaya masa Abokinsa Dauda na sallama a kofar gida, cikin sauri ya fice yana jin cewa ko me zai faru sai dai ya faru amma sai ya auri Indo gobe ba jibi ba. Gaisawa su kai cikin fara'a Dauda ya dubi mal Tanko yace " Zuwa na gayama Indo ta amince da maganar aurenka yanzu kai muke jira. Cikin matsiyar faɗuwar gaba yace an gama ga sadakina Naira dubu 10k ka bata ana sallame sallah gobe a ɗaura auren. Tsabar hango burinsa ya kusa cika ya sa Dauda kasa zama ya koma da cewar zasu je ai shirin aure gobe idan rai ya kai.
Auwal mal Tanko ya kira ya gayama masa gobe za a kawo maka Goggo dan haka ka natsu ka bita kaji? Auwal wani daɗin yaji dan zai dinga ganin mutum a cikin gidan bayan tarin tsuntsaye da abubuwa masu yawa da yake arba da su a cikin gidan, shima Ahmad ganin abokinsa na murna yasashi murnar.

Haupha ce🙋

A KAN ƊA....Where stories live. Discover now