A KAN ƊA page 10

79 7 1
                                    

A KAN ƊA...

    Na

Hauwa'u Salisu
    ( Haupha)

   Page 10

Dauda ya dubi dodon yace babu wata hanya bayan wadancan hanyoyin? "Kwarai akwai wata gurguwar hanya amma da kamar wuya binta gareka, ka samu ka saka mutane su shiga cikin gidan hakan zai karya wani daga cikin sihirinsa na gidan wanda Indo da Auwal zasu fara arangama da ainufin abubuwan da ke boye cikin gidan wanda hakan shima samun hanyar nasarace gareka.cike da tashin hankali Dauda ke duban dodon, kafi kowa sanin ba mai iya shiga gidan Tanko sai da amincewar sa wanda babu ita ga kowane mutum face mutane uku yanzu Auwal da abokinsa sai Indo matarsa, to ta yaya zan tura mutane gidan? Sannan kaf ilahirin ƙauyen nan tsoron Tanko suke musamman da yake wasu lamurra masu ban tsoro, Tanko ya daina noma amma ana gama noma za a dinga sauke hatsi kofar gidansa wanda ba wanda yasan daga ina hatsin yake, sannan kuɗi garesa kamar dussa yanzu kowa ya sani dan shike siye rabin hatsin ƙauyen nan, a saninmu dashi ko aikin gadi bai yi kaga dole mutane su kiyayesa, amma zan nemi mafita.kai tsaye wani ƙauyen ɓarayi ya nufa yayi masu jagora har kofar gidan Tanko ya tabbatar masu da idan suka shiga gidan su da tsiya har abada ya wuce gidansa cike da farin ciki.

Dai-dai lokacin Tanko na zaune tsakar gida yana wani hayaƙi mai shegen wari, ɓurum sai ga Zillaziyya cikin ɓacin rai ta bayyana. "Tanko kiran me kake mun cikin dare?cike da tashin hankali ya nuna mata ƙwaryai da yake tara jinin dabbobin da yake yankawa yana kaima Boka Burgam tana hayaƙi tamkar zata kama da wuta, dariya ta kwashe da ita mai amsa kuwwa tace "Boka ya gaji da shan jinin dabbobi na mutane yake so  kuma jarirai dan haka Kai gaggawar samo jinin jinjiri inba haka ba Tanko kana cikin bala'i" ɓat ta ɓace ya daina ganinta, yana ɗago ido ya hango katti kofar gidansa, ko bai tambaya ba yasan ƴan fashi ne, sai abin ya bashi dariya wadda amonta ya amsa kuwwa har kunnuwan ɓarayin nan. Babban su yace yau fa munzo gidan masu tsubbu dole mukiyaye. Yana rufe baki gidan na komawa suffar ƙaton kunkuru.

Haupha ce 🙋

A KAN ƊA....Where stories live. Discover now