Yana ganin ya kashe ɓarawon ya ɗauki wani gari ya shafe jikin ɓarawon da shi, nan take wani amon sauti ya mamaye gidan, ba a jima ba sai ga wani mummunan mutum ya bayyana jikinsa ko ina gashi ne ba kyan gani.
Ya dube shi ya dubi gawar ya kwashe da dariya.
Ya jima yana dariyar kafin ya ɗaure fuskarsa ya nuna gawar da sandar hannunsa nan take gawar da shi kanshi suka ɓace bat.Duk abin da akai akan idon shi akai sai ya sake aminta da cewar mahaifinshi matsafi ne na gaske
Kardai ace shi ne ya kashe ma shi mahaifiya ?
Hankalinshi ya tashi ya kasa natsuwa inda yake ɓoyen sai ga shi gaban Babansa yana kuka mai ciwo bakinsa na kyarma yake tambayar "itama Mama haka kai mata ko ? Itama dodo kaba ita ko ? Na tsaneka na tsaneka Baba !Da gudu ya shige ɗakinsa ya rufe yana kuka mai ciwo daman ashe da gaskiyar mutanen gari ?
Ashe daman duk kuɗaɗe da kadarorin gidan na haramunne ?
Kenan ya kashe mutane da dama ?
Gaskiya ba zai jure ba dole yasa ya daina ko kuwa ya tona masa asiri ga mutanen garin.
Auwal komi ya kacame masa domin bai taɓa tsammanin haka daga mahaifin nashi ba.Malam Tanko kuwa ya shige ɗakinsa ba tare da ko kallon inda Auwal yake yayi ba.
Yana shiga ya fara kiraye-kirayen sunayen Aljanun da yake aiki da su.
Cikin kaɗuwa yake neman shawarar yadda zai tsallakar da Auwal daga sharrin Boka Burgam domin ya ga Auwal yau.
Yasan kuwa tunda ya ganshi dole akwai abin da zai faru domin ya gaya ma shi kada ya sake wani ya ganshi.
Su kansu aljanun sun razana suka tabbatar da babu abun da zasu iya aikatawa har sai abin da boka Burgam ya aiwatar.Malam Tanko ya fusata yace "Akan Ɗana banƙi ba na rasa komi ba ciki hada rayuwata don haka ba zan iya ƙyale duk wanda zai kawo ma Auwal hari ba.
Aljanun suka ɓace batare da wata magana guda mai inganci ba, domin suna gudun azabar boka Burgam shi ma Tanko don ba sosai yasan boka Burgam bane yasa yake wannan cika bakin.
Auwal har ƙagara yake gari ya waye ya koma gun mahaifinsa don ya tambayeshi abin da ke yawo akan shi na mutuwar mahaifiyarsa da wahala idan ba kasheta yayi ba .
YOU ARE READING
A KAN ƊA....
Short StoryGajeren labari ne na Malam Tanko wanda bai da burin da ya wuce ya samu haihuwar ɗa namiji bai san mace, kwatsam ya samu labarin wani Boka wanda bai ɓata lokaci ba ya tasa matarsa Hanne zuwa gun Bokan,an tabbatar masa da buƙatarsa zata biya amma fa s...