Tunda ya girma yake fuskantar cewa mahaifin nasa nada wani boyeyyen sirri wanda bai san kowa ya sani hatta shi da yake ɗansa,dan haka sai ya samu kansa da jin cewar duk rintsi duk wuya sai ya gano sirrin nan da Babansa ke boye masa,akanme zai rayu cikin rashin sani mai tarin duhu ? Tabbas sai yabi dare da rana ya hankaɗo sirrin da yake boyewa ko da hakan zai sa yasamu tawaye daga mahaifin nasa, shi a matsayin yaro marar wayau ya lura ya ɗaukesa,dan haka zai bashi gundarin mamaki ta hanyar fallasa abin da ya jima yana boye masa, abin tambayarma shine, a tunaninsa har yanzu bai fara fuskantar abubuwan dake wakana ba kenan ? Lallai ne mahaifin nasa yaso kansa da yawa, domin ya jima yana ƙudundune masa abubuwa da dama,game da rayuwarsa,wanda yanzu shi ya kamata ya fiddosu filin Allah ta'ala ko da uban zai bunnesa da ransa,domin ya gama fahimtar uban bai sansa ko kaɗan, to idan ba rashin so ba miye amfanin kuɗin da yake tarawa suna lalacewa a banza ya hanasa amfana da ko sisi a cikinsu ? To ai yaji ance duk abin da uba ya tara na yaransa ne kenan banda ubansa a wannan ra'ayin ?
Gaba ɗaya haka ya hana kansa sukuni yana neman hanyar da zai bankaɗo sirrin da mahaifin nasa ke boyewa a bayyanar jama'a.
Shin zai tono kuwa ?
Ya labarin Malam Tanko ne ? Zai yi abin da dodonsa yace kuwa ?
Shin yaushe ne boka Burgam zai shanye jinin Indo ?Yaya labarin Aljana yar Fulani ?
Ya malam zai da gangar jikin barawon daya kashe ?Shin zai gane wanda ya turo masa barayi gidansa ?
Duk amsar da wasu ma amsoshin zasu zo maku a page nagaba insha Allah.
Taku ce Haupha ,karku manta ku je You tube channel ɗina mai suna HAUPHA TV ku yi mun SUBSCRIBE tare da danna kararrawa 🔔 Nagode .
YOU ARE READING
A KAN ƊA....
Short StoryGajeren labari ne na Malam Tanko wanda bai da burin da ya wuce ya samu haihuwar ɗa namiji bai san mace, kwatsam ya samu labarin wani Boka wanda bai ɓata lokaci ba ya tasa matarsa Hanne zuwa gun Bokan,an tabbatar masa da buƙatarsa zata biya amma fa s...