A KAN ƊA page 3

85 8 0
                                    

A KAN ƊA....

    Na

Hauwa'u Salisu
     (Haupha)

        Page  3

Auwal yana da shekara shida ya fara fahimtar wani gagarumin al'amari wanda ke sa yaita matsama kansa da tambaya amma karshe ya kasa gane amsar tambayarsa, ga shi dai daga shi sai Babansa ke rayuwa a cikin gidan bai taɓa ganin wani ya shigo cikin gidanba sai wata mai nono fara itama kai tsaye wani ƙaramin ɗaki ta ke shigewa Baban nasa ya bita, sai zuwa can ta fito kai tsaye kofa ta ke nufa bata ko waige.
Yau dai ya gwada bin hanyar da yake tsammanin itace ke kai mutum waje, ilai kuwa yana fita ya kama waige-waigen neman ina kuma zashi tunda bai san kowa ba? Tsawa yaji daga bayansa ko bai juyaba yasan Babansa ne, gashi yana matuƙar tsoron Baban nasa dan bai taɓa ganin dariyarsa ba, amma a kullum sai ya rumgumesa ya shaida masa yana matuƙar kaunarsa, tun bai gane maganar uban har ya fara ganewa sai dai kuma bai taɓa bari ya shiga wani ɗaki ba a cikin gidan yakan gayamasa duk randa ya shiga wani ɗaki zai mummunar saɓa masa haka zai masa dukan tsiya.
Cikin tsoro ya kalli uban nasa cike da hawaye "Dan ALLAH Baba ka barni na zauna a waje yau dai" juyawa Mal Tanko yayi yabar Auwal tsaye a gun yana neman inda zashi, yara ya hango kamarsa sunata wasa ya ruga da gudu ya shige cikinsu suka fara wasan, sai dai basu jimaba wani mutum ya zo ya tambaya "waye wannan yaron baƙo ne ?Yara sukai shiru dan ba wanda yasan shi , nuna gidansu yayi ai kafin ya ankara daga yaran har mutumin sun ruga kowa yayi takansa kamar sunga dodo, sakin baki Auwal yayi yana kallon ikon Allah da tunanin me suke ma gudu haka? Wasa-wasa kullum Auwal ya fito ya shiga cikin yara sai su ruga su barsa, abin sai ya fara damunsa ainun. Kwatsam! Malam Tanko yana zaune kofar gidansa ya ga wata mata ta wuce ta ke a gun yaji yana ƙaunarta aurenta zai yi kuma.

To ya zai da maganar Boka?
Me yasa yara ke gudun Auwal ?

Haupha ce 🙋

A KAN ƊA....Where stories live. Discover now