A KAN ƊA.....
Na
Hauwa'u Salisu
( Haupha)Page 9
Cikin wani salo na sigar macizai matar ta miƙe tsaye ta dubi Tanko da ke sume ta fashe da dariya mai amsa amo, ɗif ta gimtse bakinta ta kalli fuskar Tanko ta watsa masa wani ruwa mai sanyi da ba wanda yasan daga inda yake, sai ga Tanko zaune yana ƙibƙibta idanuwa hankali tashe ba inda bai kyarma a jikinsa. "Taurin kanka ya ja maka masifa da bala'i wanda baka isa ka magance su ba sai ka bi hanya guda ɗaya rak mai wahalar tsiya gareka, a baya muna turo Zillaziyya tana kawo maka jini kana wanka kana biyan bukatarka to mun soke hakan yanzu kaine duk tsakar dare zaka fita kaje gun boka da kanka, sannan kaine zaka nemo jinin da ake amfani da shi, matarka kuwa ta zama silar ƙaruwar arzikinka nan da shekaru uku zamu salwantar da ita ka amfana da jikinta"bat ta ɓace sai time ɗin ya hango Indo nata sheƙa barci kan gado abunta, lamarin da ya tunzura zuciyarsa kenan ya fice yabar ɗakin yana jin haushin yanda tai sake Aljanu suka shiga ɗakinta.
"Dauda kayi wauta da ka aura wa Tanko Indo, domin lamurran sun canza Tanko nada karfin iko da izzar da tafi taka yanzu domin yana tare da Boka Burgam uban matsafa, yanzu haka jinin Indo ya zama sadaka ga Bokan dan haka nan da wasu shekaru idan ba kai himmar kashe Auwal kashanye jininsa ba zaka rasata kuma bamu iya komi kan lamarin. "To yanzu ya zan na raba auren Indo da Tanko? "Babu hanyar hakan domin Boka Burgam ya gama tsara komi, kai dai kayi abin da nace kafin cikar wa'adin da zasu sha jininta kawai, akwai wata hanya guda da zaka bi ka samu Auwal amma dole sai ya cika shekaru goma wanda a shekarar ne jinin Indo zai zama abincin Boka Burgam wanda hakan zai ɗaukaka Tanko irin ɗaukakawar da sai ya bar ƙauyen nan ya koma babban gari dan samun damar gudanar da lamuransa cikin sirri da sauƙi,lokacin zaka samu dama kan Auwal domin ba zai tafi da yaronba saboda wani boyeyyen dalili nasa da bamu sani ba,dan haka ka yi abin da ya kamata ko dai ka haƙura su cinye Indo ka samu Auwal da sauƙi ko ka ɗau mataki.Haupha ce 🙋
YOU ARE READING
A KAN ƊA....
Short StoryGajeren labari ne na Malam Tanko wanda bai da burin da ya wuce ya samu haihuwar ɗa namiji bai san mace, kwatsam ya samu labarin wani Boka wanda bai ɓata lokaci ba ya tasa matarsa Hanne zuwa gun Bokan,an tabbatar masa da buƙatarsa zata biya amma fa s...