A KAN ƊA page 4

77 9 0
                                    

A KAN ƊA ....
   
      Na

Hauwa'u Salisu
    ( Haupha)

              Page 4

Mal.Tanko bai ƙasa a gwiwa ba yabi matar nan dan ganin inda ta ke ,don Allah ya sa ƙaunarta a ransa duk da yanzu shekarun Hanne shida da rasuwa bai taɓa jin yana sha'awar ƙara aure ba, duk da akwai tarin mutanen da alokacin baya suka sha bashi kyautar ƴaƴansu ya aura ya nuna rashin buƙatar hakan, wanda hakan yasa danginsa yin fushi da shi mai girma. Cikin sa'a kuwa yaga ta shige gidan wani abokinsa wanda ke sana'ar kaɗa(Auduga)da can baya mutumin mai suna Dauda yaso ƙwarai ya ƙulla alaƙa da malam Tanko amma sai Hanne tai ruwa tai tsaki tace bata aminta ba da alaƙarsu domin ana zargin Dauda da maita, dole tasa ya dinga kakkaucema Dauda har ya haƙura shima ya kama gabansa Daudan.
Fitar da malam Tanko yayi haka da nisa yasa Auwal saurin miƙewa tsaye daga inda yake zaune ƙofar gidan nasu ya afka cikin gidan da gudun tsiya, bai zame ko ina ba sai gaban ɗakin da Babansa ke kwana ciki, yana buɗewa ya ga abin da yasa numfashinsa kusan ɗaukewa duk da ƙarancin shekarunsa, cike da mamaki ya isa cikin ɗakin yana ƙara duban abin da idanunsa suke gane masa, ba komi ne ya gani ba illa tarin kuɗaɗe birjik bandir-bandir a tsakar ɗakin, amma kullum ya fita waje yaga mai tallar yalo ko rake sai ya tambayi Baban nasa kuɗi dan ya siya, amsa guda yake bashi itace "Ban da kuɗi Auwal" to shin su waɗannan ba kuɗi bane ? Cikin sauri ya zari naira ashirin ya bar ɗakin da murnar idan mai yalo yazo wucewa ya siya.
Bai sha wahalan ganin Dauda ba dan tamkar yaga tsohon ɗan'uwansa da ya ɓace shekaru masu yawa haka Dauda ya karbesa da murna, bayan sun gaisane ya bayyana masa abin da ya kawosa gidan, wato wata mata ya gani yana so ya biyota, jim kaɗan Dauda yayi kafin yace "masha Allahu, haƙiƙa nayi farin ciki duk da cewa ba nina haifeta ba, amma ina da iko da ita domin ƙanwatace mijinta ya rasu ta dawo guna da zama, sunanta Aisha (Amma anfi kiranta da Indo)"
A ƙasan ran Dauda yafi Mal Tanko murna dan burinsa zai cika na shekaru goma.

Haupha ce 🙋

A KAN ƊA....Where stories live. Discover now