page 5

478 37 0
                                    

🎀🎀🎀INDO BABA TSOHO🎀🎀🎀

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

Bisimillahi rahmani rahim

Assalamu alaikum my fans ina yima kowa barka da shan ruwa Allah ya maimaita mana amin.

Page 5

A bakin get Sauban yayi parking , yakalli  Ameera da khairat kusaka mana ku kaima momy kayan kuce mata mun wuce airport d'auko dady .

Shagwab'e fuska Ameera tayi tace yaya Sauban muma zamuje ,hararar da ya zabga Mata ,shiyasa ta tuna da wanda take magana ai bashiri ta bud'e marfin motar ta wuce ciki ,itadama khairat tunda yayi magana ta fita bata tsaya jin k'arin bayani ba.

Juya kan motarsa yayi ya d'auki hanyar airport, basu dad'e da zuwaba jirginsu yayi lording , wani farin dattijo  na hango Wanda shekarun sa baza su wuce 70  ba amma hutu da jin dad'i bazai nuna shekarun sa ba.

Dasauri Safwan ya karasa gurin yaname yimasa oyoyo hugging d'insa yayi murmushi d'auke a fuskarsa yace my lovely son ykk nayi missing  d'in ka.

Shima safwan dariya yakeyi, dady kamar baka ganni ba ?
Sauban yayi maganar , ah my soja zance ko likita ?
Duk Wanda kace dady muje  gida idan ka huta sai mu gaisa, gurin mota suka nufa , Safwan da dady baya suka shiga, tsaye  Sauban yayi yace wai man me kake nufi ni driver ne da zaka, kama kashege baya gaskiya saidai kadawo gaba .

Dady yace oh wai kungirma amma hara yanzu bakubar rigima ba, kaima kasan indai inah gari Safwan bayada gurin zama sai kusa dani, yihakuri zoka jamu mutafi.

Turo baki Sauban yayi kamar k'aramin yaro saida ya dungure wa Safwan kai sanan yashiga yaja, murmushi ne kwance akan fuskar dady kai da gani yana cikin farin ciki.

Tunda suka kamo hanya Safwan keba dady labari har sun kusa isa gida baiyi shiru ba, shi kuma dady sai biye masa yake, juyuwa Sauban yayi yace kai parrot kafa ishe mutane da surutu.

Ina ruwanka dani kawai kayi harkar gabanka kana matsayin driver amma kanasawa mutane baki.

Kuttt nikake kira driver.....
Kaga rabu dashi karka kulashi dady ya katse shi ganin yana neman Parker motar, jinjina kai kawai Sauban yayi bai sake magana ba, shi kuma  Safwan yanata faman kunshe dariya.

********

Gwaggo narba wlh nikam zan tahiyata rana tanayi.
Kayi hankuri mana na aika a dubo ta yanzu ga ta hita nasan batayi nisa ba ka k'ara hankuri.

Da gudu ta shigo tana cewa ina Habu bai dai tahi ya barni ba ko?
Daga ina kike tun dazu inah jiran ki amma kin tahi wurin bak'in yawon ki.

Habu tahiya hwa nayi sallama da k'awayena dan ba dawo wa zanyi ba wurin baba tsoho zan koma .

Gwaggo tace dako wlh na huta  kaga tashi ku tahi kar rana tayi maku.
To Gwaggo sai nadawo kila indawo yau ko kuma sai gobe.

To Allah ya tsare ya kaiku lfy , amin suka amsa ...

Indo sai kun dawo ko ?

Cab Gwaggo ai nikam na tahi kenan bazan dawo ba .

To ki gaida Baba tsoho sai nazo nima zanzo na duba shi ranar assabar .

To Gwaggo sai kin taho , sallama sukayi Mata Habu ya d'auki jakar Indo  ya fito k'ofar gida koda ya fito ya samu Indo har ta hau mashin girgiza kai yayi aransa kuwa addu'a yake Allah ya shirya masa k'anwar sa , hawa shima yayi suka d'auki hanyar gwadbawa basu wuce 50 minutes ba suka sauka kasancewar babu nisa sosai tsakanin su ...

Bakin kofar gida Habu ya ajiye mashin d'insa ,kafin ma ya sauko har ta shige cikin ma dai_dai cin gida , kiranta ya keyi amma bata ma san yanayi ba girgiza kai yayi yace wagga d'iya akwai tab'ara .

Shima cikin gidan ya nufa da sallama , sai da ya jira aka amsa masa sanan ya shiga, Indo ya hango tana cin nama ga fura gefen ta gurinta ya nufa ya sakar Mata rank'wa shi kewai yau she zakiyi hankali......

Bai k'arasa ba yaji wani irin zafi akansa juyowa yayi domin ganin meye ne aka buga masa, Baba tsoho yagani tsaye rik'e da sanda , haba tsoho daga zuwa na abinda zafara yi min kenan .

Awo an maka  waya ce ka tab'a min Mata, yanzu dan Allah akan wanan ka shaud'a min wanan zan kad'ed'i yar sanda gaskiya yau zan koma garin mu idan ba haka ba kafin gobe sai dai akaima gwaggo k'asusu wana.

Awo  ka koma dama waya gayyato ka ?

Iya wai kina inah ake ciman mutunci bazaki hito ki shigamin ba walle ina tahiyata .

Yoo katashi mana nida nake da mazaje daya wa.

Baki Habu ya rik'e yace lallai tsohin nan to zama zanyi inya so ku dahwa namana kuci.

Indo matana kin k'oshi nasan narba ba abinci take baki ba dubi yadda kika zama kamar kazar mayu duk ke k'are ........

Bai karasa ba Habu yace namanta muke d'iba muna yin miya, da ita jimin tsohon nan da iya yi.

Wlh ka hita idona Habubakar Allah ya gwada min shegan taka yooo  baku ganin yadda yariya duk ta k'are?

Baba tsoho nikam ka ishe ni da hwad'a banida laihi amma kasani gaba kana min hwad'a , ke kuma munahuka kin zuba min idanu kamar na mujiya wlh saina halakaki kuma tare zamu kom......

Saukar kara daya ji shi ya hana masa k'ara sawa , iya yagani sai huce take, yanzu Habu takwara kake cewa zaka halaka taho ka halakata .

Wlh nikam ban kwana tahiyata zanyi ko ruwa baku bani ba daga mai shaud'a min sanda sai mai buguna da karan gareri .

Bakorar ka mukeyi ba kasan duk Wanda yatab'a Indon Baba tsoho to sai inda k'arhin mu ya k'are.

To shi kenan na hakura.

*********

Bayan sun gama dinner sun dawo falo gaba d'aya a halin gidan fira suke yi Wanda indai dady yana k'asar dole kowa ya fito ayi fira dashi,

Kushir ya gobe zamuje sokoto mun kwana biyu ba muje ba.

Dady gobe fa Monday inada aiki, ai dama haka zaka ce Sauban kasani babu abinda zai hana ayi wanan tafiyar dakai.

 

Momy tace haba my.......

Bata karasa ba ya d'aga Mata hannu yayi yace Amina har ke ban d'auke ma ba kuma bana bukatar jin uzurin kowa kuma gurin Baba tsoho zamuje dan haka gobe da safe zamu bi jirgi.

Momy bata yi yunk'urin yin magana ba dan tasan halin mai gidan ta magana d'aya yakeyi ba k'ari , momy khaleel ya katse Mata maganar zuci da takeyi , momy yanzu dagaske gobe zamuje sokoto?

Eh khaleel dan haka kowa yaje ya shirya amma inaga baza mu wuce 3 days ba.

Momy har 3 days?

Eh khaleel, k'afa ya fara bugawa, wata uwar tsawar da yaji shiyasa shi nutsuwa dan shi yama manta boss yana gurin, duk kutashi kuba mutane guri idiot ko yanzu in b'ab'ala ku.

Ai kafin ya rufe baki duk sun bar falon, dafa shi Safwan yayi yace cool down my man  sokoto akwai dad'i dan dai baka zuwa ne amma zaka ji dad'i am telling you.

Shike nan my man zanje kodan wanan tsohon daya dami mutane da tambaya ta zanje yabi abinda zai bani.

Rungume shi Safwan yayi yace I love you my twin bro.

Love you too.

Muje zuwa.

It's Rashma

INDO BABA TSOHOWhere stories live. Discover now