🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
INDON BABA TSOHO
🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀Writing by
RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comبسم الله الرحمن الرحيم
Page 23
Suna fitowa daga gidan Sauban da Safwan suka fara rige_rigen tambayar sa meke faruwa tsakanin Dady da Abba da kuma Baba tsoho, murmushi ya yi sannan ya ce "abubuwa da dama sun faru tsakanin Abba da Dady kuma waɗan da suka haɗa su suna gefe suna walwalar su."
Sauban ya ce "ban gane ba kayi mani bayani yanda zan gane." Murmushi mai ciwo Habu ya yi sannan ya ce "a lokacin da kuma cika kwanaki arba'in a duniya ni kuma inada shekara biyu kenan da ya ke a lokacin uncle Umar da uncle Aliyu gida ɗaya suke zaune a lokacin kuma cikin mamy ya tsufa haihuwa yau ko gobe, wata yayar momy ce take zaune da momy a lokacin itake kula da ku tunda taga uncle Umar ta maƙale masa ana ce mata Yaya Zulaiha uncle bai ɓoye mata ba ya nuna mata rashin amincewar sa hakan ya baƙanta ran momy da yayar nata dan a lokacin sosai uncle ke samun kuɗi wata rana uncle Aliyu ya yi tafiya daga ranar suka fara shirya tuggun da zasu ƙullama uncle Umar ya ma bar gidan gaba ɗaya kuma su rabashi da yayan nasa wanda tun tasowar su suke son junan su momy tasha cema Dady, Abba ne ke masa asiri akan kasuwanci sa dan a lokacin komai Dady ya taɓa taɓarɓarewa yakeyi ganin bai ɗauka ya saka su yanke shawarar ƙula masa sharrin da zai raba sa da ƴan uwan sa gaba ɗaya kuma wannan duk shawarar Hajiyar su ne ita ke tura su yin komai amma duk da haka yaya Zulaiha ta dame Hajiyar ta shanye a gurin ƙulla makirci dan ita har bokaye ta na mu'amala da su ranar da Dady zai dawo a ranar kuma komai ya faru."
Shiru ya yi bai yi magana ba kallon sa Sauban ya yi wanda har fuskar sa ta fara canza kala, nisawa Habu ya yi sannan ya ce "kuyi haƙuri da duk abinda zan faɗa maku."
"Ba komai kaci gaba kawai."
"Yaya Zulaiha ce ta zo ta buga masu Abba ƙofa akan ya tai make su bakuda lafiya zaku mutuwa a gigice ya fito ya bi bayan ta suka shiga ɗakin momy yana shiga yaya Zulaiha ta rufo ƙofar kwance ya sami momy daga ita sai ɗaure ƙirji ta taso ta nufosa shi kuma sai ja da baya yakeyi saida ta kawo dab da shi sannan ta saki wata ƙara wacce Dady shigowar sa kenan a gidan a bakin ƙofa ya sami yaya Zulaiha ta na bubuga ƙofar da ƙarfi momy ke magana tana ce dan Allah Umar kayi hakuri kar ka manta ni matar yayanka ce duk da asirin da kake mai akan kar ya yi dukiya bai ishe ka ba sai ka keta ma matar sa haddi, a zafafe Dady yake tura ƙofar a lokacin su Baba tsoho sun fito suna jin duk abinda ke wakana har mamy ma ta fito dan ita har ta fara naƙuda koda aka buɗe ƙofar momy duk ta jiwa kanta ciwo shikuma Abba yana tsaye duk jikin sa ya gama yin sanyi ba abinda ya ke sai kallon ta sannan kuma hawaye na fita daga idanun sa, Dady na shiga bai tsaya komai ba ya cakumo kwalar rigarsa ya fara dukan sa ta ko ina idanun sa sunyi jajir saida yayi masa lilis sannan ya sake shi a cikin daren Baba tsoho ya kore Abba da mamy da kuma gargaɗin kar ya sake zuwan masa gida kuma duk ya tako koda garin nan bai yafe masa ba, haka yaja matar sa dake naƙuda suka fita basu ɗauki komai ba asibiti dake cikin garin Gwadbawa ya kaita cikin ƙanƙanin lokaci ta haifi ɗa namiji yana ɗaga yaron yayi masa huɗu ba da sunan yayan sa wato Dady sosai mamy ke mamaki a wannan lokaci uban gidan sa ya kira ya bashi labarin abinda ke faruwa a cikin daren nan suka wuce Sokoto sosai suke samun kulawa haka ya ci gaba da aiki a ƙarƙashin Alhaji Ahmed mai shinkafa har na tsawon shekara huɗu ana cikin haka su momy suka sake jin labarin inda ya ke kafin su zo masa shi kuma har ya tattara ya koma Zariya da zama anan kuma ya fara kasuwanci da kuɗin da ya samu a gurin Alhaji Ahmed mai shinkafa a hankali samun sa ya fara buɗewa duk da haka duk bayan wani lokaci yana kan hanyar sa ta zuwa Sokoto amma koda wasa bai taɓa zuwa gidan su ba sai dai ya wuce meli gurin ƙanwarsa wato Narba har ya ɗaukeni ya zo dani Zariya a lokacin inada shekara goma haka su Narba sukayi ma Baba tsoho ƙaryar cewa an kaini makarantar kwana da haka aka samu kwanciyar hankali abun mamaki kuma tunda Abba ya bar gidan babu wanda ya ke maganar sa sai lokacin da kuka zo kake tambaya ta uncle Umar Kuma ban san ta yadda akayi kuka san sunan sa ba haka naci gaba da karatu tare da Zaki wanda haka suke kiran sa har muka gama secondary School ya biya mana kuɗi muka fita ƙasar Amurika karatu wanda ni nakaranta business ina tai maka ma Abba shi kuma Zaki low, to tunda nake tare da Abba nake yawan ganinsa a cikin damuwa shine ya na ke tambayar sa saidai ya ce man bakomai akan damun da nake yi shi yasa ya bani wannan labarin shine ni kuma nayi alƙawarin kawo ƙarshen wanan al'amari tunda daga lokacin na koma gida kuma na hana a gayama Baba tsoho cewa nayi karatu nace a gaya masa kasuwanci nakeyi to kuma mun sami matsala da uban gidana shine kawai na dawo na kama harkar noma daƙyar na saba da wannan rayuwar anan kuma naga yanayin da Indo ke tsula tsiyar ta son ranta inada shekara ɗaya da dawowa nan ku kuma kuka zo shine na sami Indo nace mata inason muyi wani aiki tare da ita, bata Musa min ba ta amince akan ta kula min da duk wani motsin gidan tako amince da yariya ce mai shegen wayo to da kuka zo na sami Dady akan dan Allah ya taimaka ya tafi da Indo na nuna masa Baba tsoho ya ɗaure mata ginda ta na tsula tsiyar ta son ran ta cikin ikon Allah kuwa sai gashi Baba tsoho ya amince sai ni kuma na fara tunanin ta hanyar da zanbi na shiga gidan ku sai gashi cikin ruwan sanyi Safwan ya man tayin zuwa Abuja wannan abun ya fi komai daɗi, tura Indo kuwa da nayi ya yi matuƙar mana amfani da kuwa yaya Zulaiha taje gidan da niyyar mallakar Dady da dukiyar sa akan saka idon da Indo keyi yasa taga magunguna da yaya Zulaiha ta zo da su ba shiri Indo ta Kira ni lokacin ina Zariya hankali na ya yi matuƙar tashi mamy ce ta bada shawarar idan momy na ajiye kayan mata ta ɗauka ta musanya mata da su ta duba amma ba'a samuba hankali na yayi matuƙar tashi wata mai aikin gidan ku ce ta taimaka mata wacce ake kira da mama Dije to ita ta samo mata magunguna ta musanya, da ta gaya Mani nayi farin ciki sosai sannan na gaya mata tayi duk yanda zatayi ta saka yaya Zulaiha ta bar gidan haka Indo ta saka ta agaba azabar yau daban ta gobe daban har tayi sanadiyar da Dady yaji wani zance wanda Indo ce ta furta shi ba tare da haka ya faru ba wannan shine sanadiyar yaya Zulaiha ta bar gidan."
To kunji wannan shine sanadiyar rabewar kan Dady da Abba gefen titi Sauban ya samu ya kifa kansa marfin motar Habu ya buɗe ya fito ya buɗe ɓangaren da Sauban ya ke ya ce masa ya fito ba musu ya fito ya koma inda ya tashi shikuma ya ja motar ganin har yamma tayi idan basuyi hankali ba kuma suyi dare a hanya Safwan kam kuka kawai ya keyi jin wai momy sa ce sanadin komai shima dai Sauban sosai ya ke jin zuciyar sa na zafi motar Habu ya ja ba wanda ya sake magana daga cikin su sai da misalin goma na dare suka isa Gwadbawa duk a gajiye ga kuma ɓacin rai da dukan su babu walwala akan fuskar su duk yanda Baba tsoho ke jansu da fira basu tanka masa ba shi kuma duk a tunanin sa gajiya ce washe gari suka nufi meli basu wani daɗe ba suka dawo Gwadbawa haka suka zauna ba wani armashi zaune suke a ƙofar gida dukan su Habu ya kalle su ya ce "dan Allah inaso ku bar maganar nan a cikin zuciyar ku har lokacin da komai zai bayyana banason ku zama sanadi bayyanar komai."
"Haba Abbakar ya kake so muyi ne wace irin uwa Allah ya bamu mai son kanta da yawa haka." Katse shi Habu ya yi, ya ce "kaga Sauban da nasan bazaku bamu haɗin kai ba ko kusa bazan taɓa gaya maku ba inaso ne momy ta gane waɗanne irin mutane ne su yaya Zulaiha kafin komai ya fito fili tunda kaga yaya Zulaiha ta fara nuna kwaɗayin ta akan Dady to ba shakka Hajiya su zata goya mata baya kuma yin haka shi zai rusa tsakanin su."
Safwan ya ce "wai kuwa Hajiya ce ta haifi momy mu?"
Murmushi Habu ya yi ya ce "koma dai menene ai zaku gani nan kusa kuma bada daɗewa ba akwai wata ƙulalliya wacce har momy bata sani ba amma koma dai menene zaku gani." Kallon sa sukeyi dukan su badai wanda ya ce masa ƙala tashi ya yi zai shiga ciki har ya kai bakin ƙofar shiga ya waigo ya ce "Safwan dan Allah kar kayima momy wannan maganar ko a fuska kada ku nuna mata ku danne fushin ku har kuji komai ta ɓangaren su yaya Zulaiha na tabbata idan kunji bazaku ga laifin momy ba."
Muje zuwa
Follow me on Wattpad
Vote
Sharing
CommentIt's Rashma