🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
INDON BABA TSOHO
🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀Writing by RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
________________________________*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comBISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page 12
"Insha Allahu bazamu daɗe ba zamu dawo."
Amira ta ce "yaya Sauban nazo nayi maku rakiya?"
" Uwar gulma zauna ba inda. Zakije."
Dariya akayi mata dan kowa ya san Amira da gulma da bin didigi, hannun Indo ya kama suka fita suna masu adawo lafiya, saida suka fara zuwa gurin tela ya auna ta sannan sanan suka je Sahad sukayi soyayya komai ta gani tana so shi kuma sai biye mata yakeyi duk abinda ta ɗauka baya hanata dan so yake tayi sabo da shi yana so tayi karatu sosai dan yaga alamar tauri bazai lanƙwasa Indo ba sai da lallashi da bin duk abin da take so to hakan shi zai saka su zauna lafiya, daga Sahad yawo suka fara yi a gari duk abinda taci sai ta ajiye wa su Amira, ƙarfe takwas dai_dai suka dawo da kaya niƙi_niƙi, har ma bata iya ɗaukar su, dan harda kayan sawa ta ƙara kwasowa da takalmi harda jaka ba abinda bata kwaso ba, ba ƙaramin kuɗi ya kashe mata ba.
Suna cikin ganin kayan malamin su ya zo, rufe akayi akan sai sundawo, ran Indo bai so dan kana ganin fuskar ta kasan ranta ya ɓaci, ba wanda ya kula ta har suka ƙarasa harabar gida gurin da suke shimfiɗa kafet suka tsaya Khaleel ne ya shimfiɗa masu, duk suka zauna suka gaida malam amma banda Indo da take ta turo baki, dan ita a rayuwarta ta tsani karatu.
Gabatar masa da Indo sukayi ya jinjina kai yace "dama Hajiya ta gaya man."
Saida ya fara karɓar karatun su sanan ya ƙara masu, ya dawo kan Indo ya ce "malama A'isha wace surah kike?"
Yatsarta ta saka a baki sanan ta ƙure shi da idanun da mutane da yawa idan ta kafe su da idanu sukan daburce.
Zungirin ta Fatima tayi dan tayi magana amma ko gizau, magana malam ya sakeyi mata, nan ma shiru saida tayi niyya sanan ta ce "ni namanta inda nake."
"Kinyi Huruf?"
"Miye shi Uruf ɗin?"
Saida ya ƙare mata kallo sanan ya ce "shikenan zamu fara daga kansa, idan kinji ance Huruf ana nufin harrufa, a Hausa ce kuma ana cewa Baƙi.
Kingane yanzu?""Awo nagane yanzu na taɓa yinsa a makarantar Allo."
"To naji yanzu dai matso mu fara."
Ba musu ta matsa suka fara ba laifi tana ganewa amma fa sai ya haɗa mata da wasa sanan take karantawa.
Sai ƙarfe goma sanan aka tashi koda aka tashi Indo kam ta daɗe da yin bacci, Khaleel aka goya ma ita sai mita yakeyi suna isa falo Amira ya amshe ta tace "ragon banza ni, barima na wuce da ita ɗakina dan ma gobe zan kwaso kayanta ta dawo ɗakina da zama.
Momy da Dady dake zaune suka kalle su, momy tace "dako kin kyauta dan nayi tunanin haɗe ku."
Sallama sukayi masu, ko wanne ya nufi ɗakin sa.
Washe gari tun asuba ta tada Indo domin tayi sallah saida sukayi faɗa sanan tayi sallar ta koma bacci, ita kuma Amira ta fara shirin zuwa makaranta, ƙarfe bakwai da minti ashirin na safe (7:20am) suka fito zasu tafi a compound suka haɗu da su Sauban suma sun fito, gaidasu sukayi suka amasa har sun fara tafiya Sauban ya ce "Ina A'isha take?"