🎀🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
INDON BABA TSOHO
🎀🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
Writing by RASHIDA USMANWattpad
rashmarrka
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comBISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page 9
Sun sauka lafiya, duk a gajiye suke ko wanne so yake ya samu guri ya kwanta, Sauban ne ya nuna ma Indo ɗakin ta yana kusa dana Fatima, shiga tayi duk da babu gajiya a jikin ta, sai bacci da take ji na jiya da ba tayi ba, dan a jirgi tsoro ya hana mata yin bacci.
Shiga tayi ɗakin a gyare yake an shimfiɗa zanin gado ɗakin sai ƙamshi yakeyi, wani ƙaya taccen murmushi tayi najin daɗi, ba wani tunani ta haye gadon ta kwanta sai murmushi takeyi, bata jima ba bacci yayi awon gaba da ita.
Tana cikin bacci taji ana kiranta, ido ɗaya ta buɗe dan ganine wanene ke tashin ta, Ameera ta gani tsaye, idanun ta buɗe gaba ɗaya tace"miye ne kika zo kina tashin mutane suna bacci?.
"To bara naje na gaya masa kin ce an dame ki.
Da sauri ta kamo hanunta, ta ce "yau she na gaya maki haka,Tukunna ma wanena yace ki tassan ?
Bosss ne yace" na tado ki idan kuma bazaki zo ba sai naje na gaya masa.
"Wanene boss ɗin ni ban san shi ba?
"Mtswwwwww Amira taja tsaki ta ce ke ni wallahi kin fara isa ta da waɗannan tambayoyin naki, ya Sauban ne ke kiran ki idan kuma bazaki ba sai naje na gaya masa.
"Oh ho kice mugu ke kirana, to kice ganin tafe kwana nan zan gyara masa zama a gidan nan.
Baki Amira ta buɗe tace" ya Sauban ne zaki gyarama zama lalai kuwa zamu sha kallo, daga haka ta fita dan ta sanar da shi ta gaya mata.
Ita kuma Indo ta shi tayi dan ta wanke fuskar ta, sanan ta fito falo kusan dukan su suna zaune a falo suna kallo, Sauban da Safwan suna kan kujera ɗaya zaune, rasa waye Sauban ta yi a cikin su dan haka gaban su ta je tayi tsaye tace"waye Bosss a cikin ku?
A firgice su Amira suka kalle ta ba abinda cikin su keyi sai ƙululu A lamar ba ƙaramin firgici suka shiga ba.
Ita kam ko a jikin ta.
Kallon ta sukayi da mamaki, Sauban kuwa mamaki yake waye kuma Boss. Shikuma Safwan yana mamakin ta ya a kayi ta san sunan da su Amira sukeyi wa Sauban.Fuska ɗaure Sauban ya kalle ta ya ce"ke Bama son shashan ci a nan waye kuma Bosss?
"Ga duk kan alama kaine Ya Sauban ko, bata jira ya sake magana ba ta ce to ai kaine Bosss ɗin ko ba haka su Amira kike kiran ka ba?
Kallon sa ya maida kan su Amira duk da Ac dake kunne amma zufa sukeyi, jikin su yana ta rawa, ya kalli Indo yace"su suka gaya maki haka ne sunana?
"Eh Amira ce ta zo ta ce man wai Boss yana kirana.
"Ok yayi kyau kinyi Sallah kuwa?
"A'a sai in zan kwanta sai na haɗa nayi.
Ƙara tsuke fuska yayi ya daka mata wata uwar tsawa saida ta tsora ta, yace"kafin na rufe idona kin ɓace mani da gani kin wuce kinyi Sallah.Ai bata ma jira ya gama rufe baki ba ta kwasa a guje.
Kallon sa ya maida kan su Amira yace" ku kuma badai ni ne Boss ɗin ba ko zakuga aiki da cikawa duk ku tashi kuje ku wanke motocin gidan nan.
Idanu gaba ɗaya suka zaro, zasu fara basa haƙuri ya ɗaga masu hannu ya ce idan baza kuyi ba kawai ku gaya man.
Ta shi sukayi suka fita a compound ɗin gidan gurin da ake parking ɗin motoci suka kalla motacin dake gurin a ƙalla sunkai shidda.
Khaleel ya ce "Wallahi yariyar nan shegiya ce gashi daga zuwan ta taja mana aikin da bamu taɓa yi ba.
Amira ta ce"rabu da shegiya saina ci uban ta ai kowa shegen kan sa ne.
Fatima tace" aikin zamuje muyi ko kuma mita har yazo ya tadda mu a nan tsaye.
Ita dai Khairat bata da bakin magana dan dai ita kam suna gama wanan aikin gidansu zata gudu babu mai haka ta tanaji tana gani ta riƙa aikin bauta.
Kuyi maneji Please
Please don't forget to:
Comment
Share
Vote
Follow
Follow
FollowIt's Rashma