page 17

334 34 0
                                    

🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
INDON BABA TSOHO
🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀


Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 17

             Dady dake fitowa dan duk yaji abinda ke faruwa ya ce "rabu da ita Abbakar zata haɗu danine."

   Komawa yayi ya zauna ya gaida shi ya amsa da sakin fuska sauran ma suka gaida shi ya zauna ya fara kallon news miƙewa sukayi ko wanne ya kama harkar gaban sa  sai ƙarfe biyu suka dawo daga islamiyya raɓe_raɓe Indo keyi babu dai wanda ya kulata har yamma tayi   da taga ba wanda yabo ta kanta ta saki jiki ta fa harkar gaban ta  sai bayan magariba duk suka haɗu a falo suna kallo suna fira Safwan ne ya kalli Khaleel dake kwance har yanzu dan ya sha allura, dariya ya tuntsure da ita ya ce "malam Khaleel na Indo."


     Tashi yayi ya zauna ya na cewa "ai kaidai yaya idona idon munafukar yariyar nan saina karya ta."

   "A'a fa kayi haƙuri ni inama tunanin mu aura ma ita." A zabure ya ce "dan Allah yaya ka rufa min asiri inani ina wanan aljanar, ai wata rana sai dai ku kwaso gawata dan ko guba tana saka min na mutu."

      Gaba ɗaya dariya suke dan sai yanzu suke tuno abinda Khaleel ya dinga faɗa da dare miƙewa yayi yana takawa da ƙyar kallon sa Sauban yayi ya ce "amma dai anyi raggo wallahi shekarar ka fa ashirin ita kuma inaga ko sha ukku batayi ba wai ace itace ta lalasa ka haka."

   

      Baki ya turo ya shige ɗakin sa dan duk haushi yake ji dariyar da sukeyi masa momy ce ta ce "kunga kun korar mani da auta ko ina ruwanku da shi."

    Miƙewa Sauban yayi yana cewa "ai wanan autan naki raggo ne ace ƙaramar yarinya tayi masa irin wannan dukan har saida ya kai kwance." Daga haka ya fice ya barsu suna fira ya ɗan jima da fita ya kira Amira ya ce mata ta turo masa Indo ya na compound, kallon Indo tayi da ta nutsu kamar wata saliha ta ce "tashi kije ya Sauban yana kiran ki."

       Mairairace fuska tayi sanan ta ce "Aunty Amira kice masa bacci nakeyi." "Lalai ma yarinyar nan idan ma zaki tashi ki wuce kitashi dan nidai babu ruwana." Miƙewa tayi jiki a saɓule ta fita jingine da motar sa ta same sa yana danna wayar sa, tana ƙara so wa gurin sa ya buɗe mota ya shiga ya ce "muje ki rakani wani guri."

      Shiru tayi na wani lokaci sanan ta shiga ya ja suka bar gidan ita dai shiru tayi tana jiran taga ina zasuje, sunɗayi nisa da tafiyar ya rage gudun motar sanan ya kalle ta ita ma kallan sa takeyi ya ce "yanzu A'isha abinda kike ya kamata kenan?"

     Baki ta turo ta ce "to ni yaya me kuma nayi?" Nisawa yayi ya ce "abinda kikayi wa Khaleel koya kinsa bai kamata ba tunda yayanki ne."

"Ai na fita harkar sa shine yake ta ranƙwashi na kuma yana cemani takwalla ƴar ƙauye."

"Shine ke Kuma kika nuna masa ke ɗin ƴar ƙauye ce ko?" Shiru tayi bata bashi amsa ba hakan yasa shi ci gaba dayi mata faɗa ita dai tayi shiru bata ce masa komai ba har suka  harabar asibitin su Muhsin tare suka fito sai kumbure_kumbure takeyi shi dai bai kula ta ba har suka isa cikin office ɗin Muhsin, yana zaune yana aikin sa hankali kwance gaisawa sukayi sanan ya samu guri ya zauna sannan ya nuna ma Indo itama ta zauan sai kallon Muhsin takeyi, kallon ta yayi ya sakar mata murmushi baki ta turo maida kallon sa yayi ga Sauban sanan ya ce "me ya haɗaka da mutniyar ne yau?"


        "Ai ni yau munyi faɗa da ita tunda bata jin magana." Murmushi yayi ya kalli Indo ya ce "wai haka ne?" Rau_rau tayi da idanu sai ga hawaye "subahanallah yi haƙuri daina kuka ai keda shi mutu ka raba takalmin kaza." Miƙewa Sauban yayi ya ce "kai ni tashi muje gurin marar lafiyar nan na gan ta na mata tambayoyi sai nasan ta inda zan fara."  Miƙewa yayi yana ma Indo alamar ta taso su tafi ba musu ta fito ya rufe office ɗin nasa suna tafe suna fira akan marar lafiyar atare suka shiga tana kwance sai bacci takeyi matar da ke jinyar ta suka gaida sanan sanan ya duba file ɗin ta da ƴan dube_duben sa sanan ya ce "muje kawai." Fita sukayi ita dai Indo bata ce dasu uffan ba sai binsu takeyi sun jima suna tattauna wa sanan sukayi sallama suna hanyar komawa ne Indo ke masa maganar wanan ciwon ba na asibiti bane, da mamaki yake kallon ta baidai ce mata komai ba gurin masu sayar da gasashin kaji ya tsaya ya siya masu sanan ya nufi gida koda suka dawo har su Amira sun fara karatu tsaya wa yayi suka gaisa da malamin sanan ya umarci Indo da ta zauna ba musu ta zauna yau ƙarfe tara suka tashi basu kai goma ba kasancewar hadari da suke gani suna shiga zaune suka samesa yana aiki a laptop ɗin sa ɗagowa yayi ya kalle su sanan ya mayar da kansa ya ci gaba da abinda sukeyi  har sun wuce sa ya kira Indo ya miƙa mata namanta karɓa tayi tana sosa idanu alamar bacci take ji "nagode."

          Kawai ta ce ta nufi ɗaki su tare da Amira suka ci suka kwanta.
    

            Washe gari ta kama mondy sai shirin tafiya school sukeyi kana kallon fuskar Indo zaka ga baƙin ciki kwance a haka dai take shirya wa tun da ta tashi batayi ma kowa magana ba  harkokin ta kawai takeyi  driver ne ya kaisu tun da ta shiga makarantar batayi magana ba ta nemi guri ta zauna ita kaɗai ce saman sit ba kowa duk wanda ya zo baya zama kusa da ita dan sanin halin ta da sukayi  tanan zaune taji cikin ta na mata ciwo daurewa takeyi har aka tashi bata yi faɗa da kowa ba ana zuwa ɗaukar su ta shiga baya ta kwanta da mamaki Amira ke kallon ta ta ce "hajiya lafiya kike kuwa yau banji bakin ki ba?"

    Bata tanka Mata ba ta dai lumshe idanu shiga Amira tayi bata sake yi mata magana ba suna kawowa gida ta sauka ta wuce jakar ta ma nan ta barta tayi wucewar ta da kallo kawai Amira ta bita ta ɗauki jakar da ta bari ta nufi cikin gida a falo ta ganta kwance tayi rubda ciki hawaye na tsiyayo mata kusa da ita ta duƙa tana cewa "wai me yake damun ki ne?"

     Idanu ta matse sanan ta nuna mata cikin ta sannu tayi mata sanan ta shiga ciki, momy ce ta fito cikin shiga ta alfarma  tana ganin Indo ta tsaya saida ta ƙare mata kallo sanan ta ce "ke kuma lafiya kika kwanta anan?"

     "Wai cikin ta ke ciwo." Cewar Amira da take fitowa daga ɗaki, taɓe baki momy tayi ta ce"ai maganinki kenan ba bakida aiki sai shan kayan zaƙi ba." Tayi wucewar ta tana cema Amira idan Fatima ta dawo kice mata tayi Mani  farfesun kifi daga haka ta fita batare da ta gaya masu inda zata je ba tanan kwance bata tashi ba har bacci ya kwashe ta cikin baccin taji cikin ta yayi bala'in murɗawa wata ƙara ta saki tayi wani juyi sai gata ƙasa mulmula ta fara yi Khaleel ne ya fito daga ɗakin sa yana ganin yanda takeyi ya nufe ta yana salati jin muryar sa ya saka Amira fitowa daga ɗakin ta tana ganin Indo duk ta ruɗe Khaleel ne yayi ƙarfin halin kiran Sauban ya gaya masa halin da ake ciki ya ce gashinan tafe ba'a ɗauki lokaci ba sai ga shi ya shigo gidan koda ya zo Indo har ta fara fita hayyacin ta.




Muje zuwa

Follow me on Wattpad

Vote
Sharing
Comment


It's Rashma.

INDO BABA TSOHOWhere stories live. Discover now