page 19

326 31 0
                                    

🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
INDON BABA TSOHO
🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀

Writing by

RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 19

          Satin su ɗaya a Sokoto suka fara shirin dawowa Indo har da kuka ita kam Gwaggo Narba harda kukan farin ciki tayi ganin ƴar ta ta fara hankali ba kamar da ba da kowa yake ƙyarar ta ana gudun ta ana la'antar ta wasu kuma na ganin babu wanda zai aure ta a yanda  take saboda su sunayi ma yara aure da wuri a ganin su shine kwanciyar hankali su  sati ɗaya da dawowar su suka fara shirin komawa school  ana gobe zasu koma suna zaune a falo suna kallo suna fira gaba ɗaya su wayar Fatima ce ta yi ƙara kallon wayar tayi sanan ta maida kallon ta ga mutanene dake zaune  sannan ta maida kallon ta akan wayar ƙin ɗagawa ta yi har wayar ta katse sake kira a kayi gaba ɗaya ta ruɗe ta ma rasa me zatayi ta na kame_kame ta miƙe ta shige ɗakin ta  taɓe baki Sauban ya yi, ya ci gaba da aikin sa a laptop ɗin dake sama ƙafafuwan sa fitowa ta yi sanye da hijabi har ƙasa sunne ka takeyi ƙasa ta na tsoron ta yi magana Sauban ya mata faɗa kusa dashi ta ƙarasa ta ce "ya dama...." Sai tayi shiru ɗagowa ya yi ya kalle ta ya ce "dama me?"


            Numfashi ta sauke Sannan ta ce "dama ya Muhsin ne ya zo yana kirana." Ba abin da gaban ta yakeyi sai faɗuwa ta na jiran taji saukar mari ko faɗa ji tayi ya ce "to karki daɗe kinga dare yayi." Godiya tayi masa ta miƙe ta nufi ƙofa ta jiyo Indo  na cewa "aunty inzo in raka ki?"

Waigowa ta yi ta ce "eh taso muje." Hijabin ta dake kan kujera taja ta saka sannan suka fita a tare basu jima ba suka dawo sai tamyoyi Indo keyi mata ita kuma tayi mata shiru, koda suka shigo sauran mutane sun watse sai Sauban da Habu ne kaɗai a zaune har sun wuce su Sauban ya kira Fatima dawowa tayi  Indo ma ta ja ta tsaya ɗagowa ya yi ya kalle ta ya ce "kece Fatima?"

      Baki ta turo ta wuce ɗakinsu ta na ƙun_ƙuni bai bi ta kanta ba ya maida kallon sa kan Fatima ya ce "miye tsakaninki da Dr Muhsin?"

          Shiru  ta yi ta sauke kanta ƙasa "ko bakiji me nace bane?" "Naji yaya." "To inajinki meye tsakaninku?" "Dama wai ya ce ya na  so nane." Kanta ta sauke ƙasa zuciyar ta na dukan uku_uku saida ya kalle ta na wani lokaci sannan ya ce "to ki gaya masa ya zo ya sameni idan auren ki yake sonyi sai ya turo idan kuma shashaci ke kawo sa kuma ya kama kansa dan bana son wanan kiran da yake maki."

          Insha Allahu zan gaya masa daga haka ta wuce ɗakin ta kwantawa tayi ta na sauke numfashi buɗe ƙofar a kayi ɗago wa tayi dan ta ga ko waye Indo ce ta shigo ta ƙara so kusa da ita ta na cewa "aunty Fati me ya ce maki?"




                "Ina ruwan ki kema zaman ki da Amira ta koya maki gulma ko?"  Baki ta turo ta ce "ni dai ba wannan ba Allah ya sa ba rabaki zaiyi da ya Muhsin ba dan wallahi ya nada kyau sosai."


         "Ohni Fatima wai Indo duk nawa kike da har kin san wanan na da kyau."  "Kijiki Aunty Fati nifa yanzu na girma." "Ai naga alama nidai bana so surutu tashi ki yafi."

     Ta shi tayi ta na cewa "ban ma sake zuwa gurinki."  Daga haka ta fita Fatima dai ta bita da kallo har ta rufo mata ƙofa sannan ta koma ta kwanta, falo Indo ta fito a wannan karon ba kowa zama tayi ta fara kallo sai ga momy ta fito gaida ita tayi ta amsa mata fuska a ɗaure kwana biyu kenan momy ta na ɗaure ma Indo fuska ba ta  sake mata hakan ya sa Indo takura idan ta na gurin, kallon ta, ta yi a wulaƙace ta ce "ke dan ubanki ban hanaki zama a falon nan ba?"

      Kallon ta Indo ta yi da kyau sannan ta maida hankali ta ga kallon da takeyi ba tare da ta tanka mata ba momy na ganin haka ranta ya ƙara ɓaci ta fisgo ta ta kifa mata mari, kuncen ta ta dafe idanun ta na zubar da hawaye ta ce "momy kina cin albarkacin mutanen gidan nan ne da babu abin da zai hana na ɗauki mataki a kanki saboda ba'a taɓa buguna a ka zauna lafiya ba amma wallahi kinci darajar su Amira da Dady." Ta na kaiwa nan ta wuce ɗauke har tana bangaje momy, faɗa momy ta fara ta na zage_zage ta na kiranta dangin makwaɗaita "kinzo keda ƙanjamemen wanki kun tare mana a gida salon ku tsiya ta mu."

         Wunin ranar Indo ta yi  kuka sosai Amira ta yi ta tambayar ta amma taƙi kulata saida ta gaji ta kira Sauban momy na falo ta ga Sauban ya shigo ya nufi ɗakin Amira bayan sa tabi dan taga mai zaiyi  tana shiga ta ga ya kamo hannun Indo ya na lallashin ta tsawa ta daka masa da mamaki duka suka juyi suna kallon ta faɗi ta ke "wai banyi maka iyaka da wannan koɗaɗɗiyar yarinyar nan mai kama da Aljanu ba wallahi Sauban ka shiga hankalin ka dani in banda kwashe_kwashe na Alhaji ina shi ina kwaso mana ƴan ƙauye duk su cika mana gida da wari."

          Saida ya bari ta gama sannan ya ja hannun ta suka fita ya ce "momy meyasa kika koma haka da ba ruwanki da Indo kina sake mata fuska sannan kuma kina kula da ita to yanzu me yasa kike irin waɗannan maganganun?"

         "Sai ka matse ni na  gaya maka tunda kai kake da iko dani." Numfashi ya sauke ya dafa kansa da ya fara sara masa  sama ta hau tana mai sakin munan kalamai akan Indo da Habu juyawar da Sauban zaiyi sai ganin Habu ya yi tsaye ya saka hannayen sa duka aljihun shaddar dake jikin nufar sa ya  yi ya na cewa "Abbakar yau she ka dawo?"

         Bai bashi amsa ba hannun sa kawai ya ja suka fita a compound suka tsaya suna kallon juna iska Habu ya furzar sannan ya ce "kaga Sauban ka lallaɓa mahaifiyar ka kar ku sami matsala ni zan bar gidan in yaso ita kuma A'isha sai a mayar da ita gurin Baba tsoho."

          "Me kake faɗa ne haka Abbakar kaima kasan abin da bazai taɓa yiwa ba kenan indai kaga A'isha ta bar gidannan to aure zatayi amma banga dalilin da zai sa dan momy ta ɗauko wannan halin zaisa ta ce bazaku zauna ba idan arziki ta ke taƙama da shi ai ba ita ta bawa kanta ba."


          "Amma ka fahimce ni Sauban momy bata buƙatar mu kusa daku ta na ganin zaman mu a nan kamar an ɗaura maku wani nauyi ne."     "No Ka rabu da ita nasan ba aikin kowa bane wannan sai na Hajiyar ta nasan ita zata zuga ta."



           "Shikenan zan bar A'isha a nan amma sai kun sa ido dan nasan halin A'isha bata ɗaukar raini tun tana ƙarama bata san kanta ba bare yanzu da ta fara girma." Murmushi kawai ya yi duk da har yanzu ransa a matuƙar ɓace ya ke Habu ya katse sa da cewa "muje ka raka ni na samu gidan da zan zauna."

          "Ban gane ba shi kuma nan fa?" Murmushi Habu ya yi ya ce "a'a  bazan zauna a nan ba zan dai riƙa zuwa gaishe da momy dan hakan gaskiya zai fi mani kwanciyar hankali."

        Shiru Sauban ya yi  na wani lokaci sannan ya ce " ba damuwa inada wani gida a  gwarinfa sai ka zauna a can tunda ka matsa bazaka zauna damu ba."

           "Kayi haƙuri ɗan uwa hakan shine kwanciyar hankali na da ku gaba ɗaya kaga ban ga wani abuba bare  raina ya ɓaci dan zan faɗa ma gaskiya bazan lamunci ana cima iyayena zarafi ba to kaga ban ganiba bare nayi magana ranku kuma ya ɓaci ai kaga abu baiyi kyau ba."

       "Haka ne kuma amma ba komai zan ɗauki mataki akan Hajiyar nata, yanzu muje kaga gidan sai dai ba wani babba bane dan a lokacin da na siye shi wani aboki nane ya ke da buƙatar kuɗi shine ya sayar Mani dashi amma babu wanda ya san dashi duk gidan nan." Godiya ya yi masa sannan suka fita tare.




Muje zuwa


Please and please follow me on Wattpad

Don't forget to:

Comment
    And
Sharing
Voted




It's Rashma

INDO BABA TSOHOWhere stories live. Discover now