🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀INDON BABA TSOHO
🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
Writing by RASHIDA USMANWattpad
rashmarrka
________________________________*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comBISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Page 14
"Ni dai Allah ya gani kuma yana kallon ka."
"Ai nasan yana kallo na. Amira bani cazar wayar ki dan Allah.""Basai ankai can ba to amma baka karanta min ba."
"Khaleel koya mata ka tabbatar kafin mudawo daga sallar magariba ta iya shi."
Murmushi jin daɗi yayi ya ce "angama ranka ya daɗe, ke kuma yau sai kingane waye mai ranƙwashe shen kai."
"Ba'a so ɗin kaga wallahi ban rama abinda kayi min ba to kashiga hankalin ka kar kabari najuyo kanka dan bazaka ji daɗiba."
Daga haka ta juya gurin Amira ta ce "masoyiyar asali koya min duk sai na basu mamaki duk da idan nayi karatu dayawa kaina ciwo yakeyi amma sai na nuna masu ni ba takwalla bace."
Mtswwwwww Khaleel yaja tsaki ya ce "aikin banza ba masoyiyar asali ba maƙiyiyar asali."
"Wallahi kabini ahankali ko na tona ma asiri kasan naganka ko."
"To da hauka nabiki halan, kiyi abinda aka sakaki ni nayi nan inada test gobe zan yi karatu."
Bai jira ta sake magana ba ya shige ɗakin sa.
Sauban ya ce "meye yayi ne."
Tunani ta fara sanan ta "ce namanta."
Karatu suka fara sun kai K tace ita ta gaji a bari ta huta ƙwaƙwalwar ta ta ɗauki zafi sai ta huce, Sauban na ganin haka ya san alamun bazata yi ba kenan cazar dake kusa da shi ya ɗauka yana maganar miƙewa tayi saurin cewa "muci gaba ai har ta huce."
Dariya Habu yayi wanda tun ɗazu yana kallon diramar da sukeyi, ya ce "ashe akwai wanda Indo ke tsoro a duniya."
Murmushi Sauban yayi yace "koni ba tsoro na takeji ba tasha gayamin idan nashiga hanunta bazata min da wasa ba."
Dariya sukayi gaba ɗaya.
Assalamu alaikum.
Wa, alaikumussalam, suka amsa sallamar da Dady yayi gaida shi sukayi ya amsa ya cewa "ah Abbakar har ka iso kenan?"
"Eh wallahi Baba mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau ya maman taka da kuma Baba tsoho?"
"Duk suna lafiya sunce a gaishe ku."
"To madalla Allah ya hutar da gajiya bara nashiga ciki.""To Abba a fito lafiya." Bayan sallar magariba suna zaune gaba ɗaya suna kallo su Sauban suka shigo, Indo ya kalla ya ce "ke tashi kije ki ɗauko hijabin ki muje me lesson ɗinki ya zo."
Kallon sa tayi ta ce "ni banda hijabi sai dai naje momy ta bani aron nata."
Kallon gaba ɗaya sukeyi jin wai hijabin momy zataje aro, ba wanda ya kulata har shi Sauban ɗin har ta haura sama bata jima ba sai gata ta dawo da wani ƙaramin mayafi a hannun ta bata kula kowa ba ta fita daga falon girgiza kai Sauban yayi sanan yayi murmushi ya ce "very soon zakiyi hankali koba dai kinga ina ɗaga maki ƙafa ba." Daga haka ya fita, tsaye ya sameta sai turo baki takeyi tana jujuyawa bai ko kalle ta ba ya wuce ta binsa tayi a baya tana hararar sa har suka kai gurin da malamin dake jiranta tsaye tayi bata gaida shi ba, kallon ta yayi ya ce "baki iya gaisuwa bane?"
Baki ta turo tana ƙunƙuni ta ce "ina yini." Murmushi kawai malamin yayi ya amsa sanan ya kalli Sauban ya ce "a ina zamu fara?"
"Ai kawai ku fara daga ABCD dan babu abinda ta'iya nan da kake ganin ta."Yana gama faɗar haka yaja farar kujera ya zauna yana kallon su, turo baki Indo tayi tana ƙunƙuni tana share hawaye da ya sauko mata dan ji takeyi kama ta ture shi daga kan kujerar da yake zaune, zama itama tayi akan kafet ɗin da ke shimfiɗe a gurin.........
Kuyi maneji Please
Follow me on Wattpad
Vote
Sharing
CommentIt's Rashma.