🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
INDON BABA TSOHO
🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀Writing by
RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comبسم الله الرحمن الرحيم
Page 25
Hannayen sa ya saka a cikin aljihun wandon farar shaddar da ya saka kallon ta ya keyi ba tare da ya ƙifta idanu ba faɗa takeyi sosai akan lallai sai ya saki Indo ba tare da ya ce uffan ba ya fita Habu ma ya mara masa baya aka bar Safwan tsaye yana mata kallon mamaki yanda take taya waɗannan mutanen yaƙi akan Sauban yaƙi auren ƴar su zama ya yi kusa da ita ya dafa ta ya ce "momy me yasa kike biyewa mutanen nan suna neman halaka ki?"
Numfashi ta sauke ta ce "Safwan bazaka gane bane ina cikin tashin hankali wanda ban taɓa zato ba sun bani zaɓi ne indai har Sauban bai auri Safiya ba to ni zasu kora yaya Zulaiha ta auri Dady ɗinku."
"Sai kuma ki kwanta kullum suna mulkar ki bazaki tashi ki ƙwaci ƴancin kanki ba?" Cewar Sauban da yake bakin ƙofa yana niyyar shigowa, "bazaka gane ba ɗannan amma ni nasan ina cikin tsaka mai wuya."
Uhmmm kawai ya ce dan shi yana ganin koma menene ita ta tajawa kanta makullin sa da ya faɗi ya ɗauka ya bar gidan, haka dai aka ƙarasa biki ba daɗi sai gurin shida momy ta fito dan shirin tafiya da amarya akeyi duk wannan abinda akeyi Indo da Amira na can gidan amarya basu san wainar da ake toyawa ba dama can tunda aka fara biki suke fushi akan Sauban ya hana ayi event ko ɗaya na abinda ya danganci party walima ce aka haɗa washe gari ranar da aka kai amarya a gidan ta, ƴan biki suka fara tafiya Dady ya san da rikicin da ke faruwa amma yaƙi magana baya son tashin hankali baƙi suna nan shiya sa ya kawar da kansa daga maganar har sai ya gama sallamar baƙi tukunna, da dare bayan duk manya baƙin sa sun gama watsewa ne ya samu zama dasu ya ce "kuyi haƙuri da abinda ya faru ba laifina bane ko na yaron wannan umarnin Baba tsoho ne." Faɗa momy ta fara yi tana cewa "miye nasa a ciki da har zai bada wannan umarnin, to yazama doli ya saketa dan bazan haɗa iri da dangin matsiya ta ba." Tashi ya yi ransa a matuƙar ɓace ya ce "lallai Amina wuyanki ya yi kauri nikike gayawa wannan maganar da kike cewa bazaki haɗa iri da matsiya ta ba aiko kin gama dan ko niɗin jinin su ne karki manta A'isha ƴar ƙanwa tace dan haka ki shiga hankalin ki."
"Ka faɗa mani duk zuri'ar ku akwai mai kuɗi ne bayan kai kaga ko dole akiraku matsiya ta." Waigowa ya yi ya kalle ta dakyau yasan waɗannan kalaman ba nata bane na Hajiyar su ne gyaɗa kai kawai ya yi ya fita, su Baba tsoho satin su ɗaya suka koma dan ba yanda Dady baiyi da shi ba ya zauna amma yaƙi dole ya barshi ya koma su yaya Zulaiha suma sun tattara suka tafi harda yi masu sallama, da bama momy haƙuri suka nuna mata komai ya wuce driver na sauke su tasha ya koma, suna ganin fitar shi suka fito suka nemi abin hawa ya kaisu wata unguwa dake gefen wata unguwa wacce gidan gwamnoni ne suka fi yawa wato Asokoro, ƙauye ne sosai unguwar anace mata kasuwar dare gida suka kama wanda a gidan ɗaki ya kai goma sha anan suka ci gaba da zama suna ƙulle_ƙullen su, momy kuwa ta saki ranta tana sha'anin ta amma ta ɗayan ɓangaren har yanzu Dady fushi yakeyi da ita wanda hakan kesa idan taga Indo take jin kamar ta kashe ta ta huta, ba yanda Indo batayi ba akan zata koma gurin Narba da zama amma fir Habu ya hana kuma har yanzu bata da masaniyar auren da ke kanta babu wanda ya gaya mata dan Sauban ya hana koda wasa a gaya mata.
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah a yau Indo ke shirin fara zana jarabawar ta na kammala secondary, murna a gurin ta ba'a cewa komai haka kuma suna shirye_shiryen saukar al'ƙur'ani sosai suke shiri, amma banda momy dan yanzu ta sare da al'amarin su Hajiya dan yanzu ko wayarta basa ɗagawa inba kuɗi suke nema ba a gurin ta, zaune yake a office ɗin sa yana danna wayar sa buɗe ƙofar akayi, kallon ƙofar ya yi Habu ne ya shigo yana sanye da ƙananan kaya sunyi matuƙar kar ɓarsa kujera ya ja ya zauna hannu ya basa suka gaisa Sauban ya ce "sai ina naga kaci kwalliya haka?"
Murmushi ya yi ya ce "dama sai za'aje wani guri ake kwalliya?" Wayar ya ajiye sannan ya ce "kai ni duk ba wannan ba so nakeyi mu fara shirin tarewa da madam."
"Au dama kiran da kake yi mani kenan?" "Eh shine."
"Amma lallai baka da kunya ina sirikin ka kake gaya mani irin wannan maganar." Taɓe baki ya yi ya ce "su siriki anji jiki." Wayar Sauban da tayi ƙara ne ya hana ma Habu magana duba wayar Sauban ya yi ya ga Safwan ne mai kiran sa ɗagawa ya yi da niyyar masa faɗa akan bazai zo ɗaukar sa ba sai yaji muryar sa ciki tashin hankali yana gaya masa gobara ta tashi a Company ɗin Dady, a zabure ya miƙe zufa na karyo masa sai ya ce "yanzu kuna ina ba wanda yaji ciwo?"
Ajere yake jefoma sa waɗannan tambayoyin yana gama sauraren abinda Safwan ke gaya masa ya katse wayar ƙofa ya nufa yana yima Habu bayani shima ba ƙaramin tashi hankalin sa ya yi ba, Sauban bai iya jan mota ba saida Habu ya jasu, yana gama parking Sauban ya ɓalle murfin motar ya fito mutane ne tsaye a gaban Company ɗin sai masu kashe wuta da ke ƙoƙarin kashewa ciki ya nufa hankali sa a tashe jin wai Dady yana ciki security gurin ne suka riƙe shi sai ƙoƙarin ƙwacewa ya keyi suna cikin haka aka fito da Dady kamar matacce wani irin ihu ya yi yabi bayansu motar asibiti da aka kira ne aka saka Dady a ciki shima Sauban bai tsaya komai ba ya shiga, a motar Sauban, Habu da Safwan suka bi bayan motar asibitin, daƙyar aka samu ya farfaɗo saida ya dawo hayyacin sa sannan suka masa allurar bacci, bayan likitoci sun gaya masu yana lafiya hakan baisa hankali su ya kwanta ba saida ya farka bayan allurar ta sake shi duk da ya tashi garau baisa sun sallame shi ba sai washe gari suka sallame shi, bayan sati ɗaya da faruwar haka aka fara bincike menene ya tada wannan wuta sosai suke bincike amma sun kasa gane kan komai, a dai_dai wannan lokaci ne kuma Hajiya iya da yaya Zulaiha suka zo duba Dady daga nan kuma suka ce sun sami gurin zama, gaba ɗaya ma'aikata gidan basu ji daɗin zuwan nasu ba har yaran gidan ba mai murna da zuwan nasu yanzu Indo na gida Kasancewar sunyi graduation sai jira saka mako sukeyi, idan ka ganta yanzu da wuya ka gane ta dan ta ƙara girma kyanta sai ƙara fitowa yakeyi gata da kyan jiki komai ya ji saidai kace masha Allah wata rana suna zaune a compoud ɗin gidan akan fararen kujerun da ke tsakar gidan yaya Zulaiha ta dawo daga unguwa kenan Amira ta gaida ta amma Indo ta kauda kanta hakan ya bala'in ɓatawa yaya Zulaiha rai har tayi gaba ta dawo baya ta kalle ta ta ce "inaga dan munbar ki har yanzu da wannan ƙadaddararen aune nan ne kike jin ke ɗin wata ce ko?"
"To bari kiji idan kin ƙara sati da auren Sauban akanki kice niba ƴar halak bace."
Muje zuwa
Follow me on Wattpad
Vote and shearing
Comment
It's Rashma