page 16

358 37 0
                                    

🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
INDON BABA TSOHO
🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀

Writing by RASHIDA USMAN

Wattpad

rashmarrka

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 16

           Tafiya take ta na zumɓura baki da jin haushin mutanen gida sun ƙi kula ta har ta kai gurin da su Sauban suke zaune zama itama tayi  sai faman turo baki takeyi ba tare da ɓata lokaci ba suka fara karatu suna cikin yi wayar Sauban tayi ringin  ɗaga wa yayi sanan yayi sallama shiru yayi sanan ya ce "ok bari na fito ko kuma  ka shigo ina compound  zaune." Daga haka ya katse kiran get masu gadi suka buɗe wata mota ta shiga fara tas, da kallo Indo tabi motar malamin na magana amma hankalin ta na kan  motar da ta shigo, wani kyakkyawan matashi ne ya fito fari tas ƙifta idanu tayi ta ƙure shi da kallo har ya ƙara so gurin su hannu ya bama  Sauban sanan ya bama uncle Salim hannu suka gaisa  kallon Indo yayi da har yanzu kallon sa takeyi kujera Sauban ya nuna masa ya ce "zauna mana."


     "Idan muka zauna anan bazamu takura su ba?"

"Kai dai ka zauna idan na tashi daga gurin nan to ina tabbatar maka baza'ayi karatun nan ba."

          Kallon Indo yayi sanan yayi murmushi saida kumatun sa suka lotsa kamar dai na Sauban sannan ya ce "wai dagaske ne ƙanƙara?"

      Rau_rau tayi da idanu sai ga hawaye ta ce "daure wa kawai nakeyi amma yanzu haka cikin  ƙwaƙwalwa ta gobara akeyi."

      "Subahanallah dama ƙwaƙwalwa na gobara ne?"

     Dafa sa  Sauban yayi ya ce "kaga Muhsin ka rabu da ita tsabar bata son karatun ne shine take wanan iskancin."

      Kallon ta yayi da mamaki sai dai bai ce komai ba Sauban ya ce "ina jinka me kake cewa ne?" Zama ya gyara sanan ya ce "wallahi wata marar lafiya ce aka kawo mani nidai nayi iya bincike na amma na kasa gane kan ciwon nata."

        "To yanzu ya kake so ayi kenan?" "Ina so ne ka gwada sa'ar ka ko Allah zai saka a dace." Shiru Sauban yayi na wani lokaci sanan ya ce "to bari zuwa gobe idan na tashi aiki zanzo asibitin naku." "Haba mana man mezai hana muje idan anyi magariba sai muje ka ganta." "Ba damuwa idan anyi sallar sai muje."


     Wayar sa ya janyo yayi danne_danne ya kara a kunne, ya ce "ki kawowa baƙo ruwa ina compound." Daga haka suka ci gaba da fira Fatima ce ta fito tana tafiya a hankali kamar mai jin tausayin ƙasa kallon ta Muhsin ya dinga yi tunda ta fito har ta ƙara so gaban su ta ajiye sanan ta gaida shi, murmushi yayi sanan ya amsa gyaran murya Indo tayi ya saka Muhsin kauda idanun sa daga kallon Fatima, juyawa tayi ta nufi cikin gida ya bita da kallo duk Sauban na kallon sa sai dai bai ce masa komai ba har ta shige.


    "To idan ka gama kallon nata kasha ruwa mana." Ruwan ya ɗauka yana murmushi  ya ce "wanan ma ƙanwar ka ce?"

      Bai kalle shi ba ya ce "a'a ba ƙanwata bace yaya tace." Dariya kawai yayi  ya tashi ya ce "to ni zan wuce." "Zaka wuce ina?"

     "Ko kamanta tare zamu fita idan munyi magariba?"

     Kan sa ya dafa ya ce "wallahi duk namanta  ganin  ƙanwar yasa na manta." Taɓe baki Sauban yayi, fira suka ci gaba dayi har  akayi magariba suka fita tare Indo kuwa ta nufi cikin gida tana shiga ta fesa ma Fatima duk abinda baƙon ya ce ita dai bata ce mata komai ba hakan ya bama Indo haushi har ta ce mata bazata ƙara kawo mata fira ba.

INDO BABA TSOHOWhere stories live. Discover now