🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀
INDON BABA TSOHO
🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀
🎀🎀
🎀Writing by
RASHIDA USMAN
Wattpad
rashmarrka
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.comبسم الله الرحمن الرحيم
Page 26
Da kallo Indo ta bita har ta ɓace ma ganin ta sannan ta juyo gurin Amira ta ce "ko kin gane kaman matar nan?"
"Ke baki gane me take nufi bane?"
"Ko ɗaya ban gane ba kilama ta fara hauka in bashiba niwai take kira matar yaya Sauban."
"Yanzu ke duk zaman ki baki san akwai auren ya Sauban akan ki ba duk rigimar da akayi a gidan nan?"
Shiru ta yi dan maganar gaskiya Habu ya gaya mata komai har taso ta tada rigima a lokacin amma sai ya dinga lallashin ta har ta amince tabar zancen kawai dai ta zuba masu ido ne taga iya gudun ruwan su dafa ta Amira ta yi ta ce "A'isha meya sa bazaki gaida ta ba ko ba komai ai ta girme ki?"
"Har abada bazan taɓa gaishe ta duk abinda zatayi ta daɗe batayi ba."
Shiru Amira ta yi tana mamakin irin taurin kan Indo babu mai iya tanƙwasa ta sai abinda ta yi niyyar yi, a fusace ya ya Zulaiha ta shiga cikin gida tana huce ɗakin Hajiya ta nufa banka ƙwafar ta yi saida Hajiya da ke zaune bakin gado ta waigo da sauri, jakar hannun ta yar ta na huci ta ce "Hajiya idan bazaki iya yin wani abu akan Indon nan ba ki gaya mani dan wallahi banaso ta ƙara sati da aure a kanta so nake kafin ta tare ta zama bazawara kinga kuwa hakan yafi komai ciwo."
"Yanzu ke kina tunanin zan zuba ido ina kallon su ne bayan kuma sunsa naji kunya sannan kuma su suyi farin ciki?"
"Abinda bazai taɓa yiwa ba kenan ki zuba ido ki gani indai ina numfashi babu macen da ta isa ta zauna da Sauban sai Safiya."
Wani irin murmushi jindaɗi yaya Zulaiha ta yi ta matso kusa da Hajiyar ta ce "shiyasa nake sonki dayawa Hajiya ta."
Kwance yake akan doguwar kujera dake falon part ɗin su kwana biyu kenan kwata_kwata baya jin daɗin jikin sa ko kaɗan sai ya dinga jin ransa yana ɓaci da jin haushin komai gaba ɗaya baya son jin muryar mace idan kuwa yaji hankalin sa yakan tashi ji yake kamar wuta na cin duk ilahirin jikin sa ga wata ƙara da yake ji a duk lokacin da ya ji Muryar Indo yakanji ana bashi umarnin da wata murya ana ce masa ya sake ta, kwata_kwata shi yanzu idan ya ganta ji ya keyi kamar ya ga mutuwar sa haka ya ke ji.
Ana saura kwana uku saukar su hakan ya sa Amira da Indo suka rage zama gida kullum suna makaranta sosai Dady keyi masu shiri, Habu ya je har Zariya ya gayam su Abba maganar saukar su bai bari Habu ya dawo shi kaɗai ba sai tare da shi da dukkan ahalin gidan a gidan su Babu suka sauka kafin anjima su je gidan sa dake garin, basu jima da sauka ba saiga Indo tazo gidan tana ganin baƙi saita fara washe baki tana gaida su amsawa sukayi amma banda Zaki da ko kallon ta baiyi ba taɓe baki ta yi ta nufi maman ta cikin shagwaɓa ta ce "nidai wallahi ayi dani cikina dambe kawai akeyi." Ɗagowa Zaki ya yi ya kalle ta ya saki wani irin tsaki da ƙarfi yana miƙe tsaye, har ya kai ƙofa yaji ta ce "aikin banza ni kam gyara ma zama zanyi kazo gidan mu kuma ka cika mutane da baƙin rai da tsaki kamar dangin tsaka."
Waigowa ya yi ya kalle ta yanda take motsa ɗan ƙaramin bakin ta baidai ce komai ba ya fice, murmushi Abba ya yi ya ce "mamana kema ashe haka kike kamar Abubakar?"
"A'a Abba karma is haɗamu da wannan magana siɗun dan ko sati ɗaya bazaku iyayi da ita ba tuni zata saka maku ciwon kai."
"Haba ya Habu niɗin kake yima irin wannan shedar?" "Yooo ƙarya kike son na faɗa kedai bi wancen miskilin da ya fita idan ba haka ba Allah karyaki zaiyi ya barki da jinya ba ruwana dan koni taka tsantsan nakeyi dashi kar wata rana ya zubar mani da haƙora." Duk wannan maganar da yakeyi ƙasa_ƙasa yakeyi da murya dan karya jiyo shi su kwashi ƴan kallo, kallon sa Indo ta yi ta ɗaga murya ta ce "miskili kafi mahaukaci ban haushi kazo ga ya Habu nan yana gulmar ka."
Da sauri ya toshe mata baki ya sakar mata ranƙwashi aka cizo ta sakar masa a ɗayan hannu da ya toshe mata baki ƙara ya saki ya matsa yana zabga mata harara dariya duka aka saka masu ƙwafa ya yi ya fita fira suka ci gaba da yi kafin yamma Indo da Minal sun saba sosai sai ƙanan ta Habiba da Halima sai ƙaramar su Safna sai gurin shida sannan ta tashi tayi shirin tafiya gida ƙunƙuni takeyi bata son tafiya dan duk lokacin da tazo takan ce ita bazata koma ba sai Narba ta tasan mata tsaye tukunna take tafiya yau ma hakan ta faru da saida tasha faɗa sannan ta fito a ƙofar gida ta sami Habu da Zaki suna zaune dan ba wata fira sukeyi ba Habu ya ce "har zaki tafi kenan?"
Baki ta turo tana share hawayen dake zubo mata, murmushi ya yi dan ganin irin hararar da Zaki ke aika mata dan yasa baya son shagwaɓa ko kaɗan "to yi hakuri muje na saukeki kinji."
Gyaɗa masa kai tayi makulin mota ya karɓa tunda su sai bayan magariba zasu tafi gida suna tafe suna fira har suka iso a ƙofar gida suka ga Sauban tsaye fitowa Habu ya yi ya basa Hannu suka gaisa da harara yabi Indo har ta shige ciki wani irin haushin ta ya ke ji baima bari sun gama maganar da sukeyi ba yabi bayanta kamar Habu shima zai shiga saidai kawai ya juya ya kama hanya tana shiga falo yana shiga bata ankara ba taji hauri a bayan ta waigowa ta yi dan ganin waye da mamaki take kallon sa kafin ta yi magana ya kife ta da mari wata gigitacciyar ƙara ta saki wanda yasa mutanen gidan fitowa momy ce tayi ƙarfin halin tambayar sa abinda ta yi masa rasa dalilin abinda ta yi masa ya yi sai kawai ya juya ya fita, murmushi yaya Zulaiha ta yi dan tana tsaye tana kallon abinda ke faruwa juyawa ta yi ta koma ɗakin Hajiya anan take labarta mata abinda ke faruwa murmushi ta yi ta ce "yanzu ki kira Safiya duk inda ta ke gobe ta dawo nan gidan dan idan yana ganin ta komai zaifi ta fiya dai_dai, dan ma yana addu'a ne da ai tuni ya daɗe da sakinta."
"Ai bari Hajiya yanzu ma zansa ta kamo hanya ." Daga haka ta ɗaga waya takira Safiya saida ta kusa tsinkewa sannan aka ɗaga ta ce "Safiya kina ina?"
"To inason yanzu ki kamo hanya kizo Abuja gidan Amina kuma yau nake son ganinki a gidan." Daga haka ta katse wayar, kallo Hajiya ta yi ta ce "wai sunje birthday ɗin ƙawar ta a kaduna."
"To ai da suƙi tunda tana kusa."Indo kuwa kwana ta yi da zazzaɓi, saida safe ne Amura ta bata magani sannan taji sauƙi da misalin sha biyu suka fito domin zuwa gidan Fatima dan a can zasuyi kayan snacks da zasu raba a gurin walima, sun iso falon suka ga Safiya zaune tana taunar cingwam tasha kwalliya sanye take da ƙanan kaya riga da wando sun bala'in kamata fuskar nan tayi fari tas akan bilicin ga kanta ya sha ƙarin gashi, sai marmaɗa idanu takeyi da suka sha eye lashish taɓe baki Indo ta yi ta wuce bata ƙara kallon ta ba shewa ta yi ta na cewa "ni wallahi kallon bazawara nake maki."
Har sunkai bakin ƙofa Indo ta juyo ta dawo gaban ta ta ce "idan ni kallon bazawara kike mani to ni kallon karya nake maki...." Tas suka ji saukar mari akan kuncen ta waigowa tayi dan ganin wanda ya mare ta, Sauban ta gani tsaye sai huci yakeyi.
Muje zuwa
Follow me on Wattpad
Vote and shearing
Comment
It's Rashma.