AURENTA ZANYI....3/4

508 37 0
                                    

_*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

_Page 3/4_

Koda suka shiga office d'in kasa zama yai sbd yanda hankalinsa yake matuk'ar tashe,shikansa doctor haji hankalinsa atashe yake sbd yasan matsalar tasu ta haihuwa musamman ita hajiya jolde.

Cikin tashin hankali Alhj yafara magana muryarsa har rawa take sbd yanda zuciyarsa kemasa suya.
"Doctor miye mafita,doctor kataimakeni kada matata tasami matsala sbd na tabbata idan har ya tabbata wannan babyn yamutu tabbas itama koda bata rasa ranta ba toh zata samu gagarumar matsala a rayuwarta,ina matukar k'aunar maryam bana son komai yafaru daita,kataimakeni doctor"

Gaba daya kan doctor haji ya d'aure yakasa samun mafita, can yad'ago yakalli Alhj kadel yace "nifa Alhj kana bani mamaki,wai na taimakeka kamarya kenan...? Inace babyn har a hanunka yake katabbatar cewa ya mutu,to kuma me kakeso namasa ne ko so kake nadawomar da ransa ne".

Dasauri Alhj kadel yamatso kusa dashi yace "ka fahimceni doctor,inaso nafad'ama wani sirrin,shi kansa wannan cikin dakaga anhaifa a yanzu bawai yashiga mahaifa bane ta hanyar jima'i, aa yashigane ta hanyar yin dashen kwayayan halitta nawa izowa mahaifarta sbd wani babban dalili,
Inaso kasani doctor yau kimanin shekara goma sha biyar kenan da auren mu ni da maryam amma sau daya ta tab'a haihuwa yaron kwanansa biyu kacal Allah ya amshi abunsa.

Tindaga lokacin maryam batasake koda b'ari bane bare haihuwa gashi tanasan yaya ido rufe, nikuma iyayena suntakurani har saida nak'ara aure inda yanxu nakeda yaya hud'u maza biyu mata biyu.

Maryam tanasan yayan nawa sosai amma dayake mahaifiyarsu masifaffiya ce sai take hana yaran suzo gun maryam,bayanda naiya sbd mahaifiyata ba wacca tafiso kamar Amina matata ta biyu da yayanta, kokad'an bata k'aunar maryam gashi nikuma ina matukar k'aunar maryam.

Babban abun tashin hankalin maryam shine, tarin dukiyarda takeda wacca tarasa magajinda koda bayan ranta zai gaji dukiyar, sannan koba komai itama tanasan taga nata jinin a duniya, ahalin yanxu ido rufe take neman yaya wannan dalilin ne yasa nanemi wani doctor a india wanda abokina yahad'ani dashi,
Tofa shine yamana wannan aikin har aka samu wannan cikin, ba kalar farincikinda maryam da ahalinta basuji ba sbd samuwar wannan cikin har kyaututtika aka bata wasunsu kuma sunce sai idan tahaihu zasu bata.

Doctor idan har ya tabbata wannan babyn yamutu me kake tinanin zai iya faruwa ahalin yanzu...?".

Zama doctor yai akan kujera tareda sauke nannauyan numfashi, yad'auki tsawon sakanni kamin yad'ago yacewa kadel "yanzu mekake buk'atar ayi kenan, ina nufin wane taimako kake buk'atar namaka?".

Dajin haka sai kadel yazauna kan kujera tareda kara matso daita dab da doctor sannan yace "inaso ka taimakeni ka k'aryata wannan mutuwar babyn nawa" cikin rashin fahimta doctor yace "as how...ban...banfahimceka ba" kadel yacigaba da fadin.

"Inasan kamana exchange na babyn mu da d'aya daga cikin jinjirayenda aka haifa a yanzu, nikuma namaka alk'awarin kud'i tindaga naira million d'aya har izowa naira million ashirin a kud'in najeria, dan Allah ka taimaka doctor please....!!!".

D'an murmushi doctor haji yai sannan yad'an d'ago daga risinarda kansa da yai tareda mik'ewa a tsaye yai tako d'aya zowa biyu sannan yajiyo yakalli doctor haji yace "wannan abun da zamuyi yanzu kasani yana d'aya daga cikin manyan laifuka a kundin dokar k'asar nan, hakama yana d'aya daga cikin babban laifi na wannan asibitin wanda idan har aka kama dik likitanda ya aikata hakan hukuncinsa d'aurin rai da rai a gidan kaso, sbd haka zan taimakeka a sbd halinda naga kake aciki wanda har kaiya fallasaman asirin gidanka".

Kadel najin haka baisan lkcnda yasauke wani irin nannauyan numfashi ba taredayin wani irin murmushi wanda rabonsa dayin irinsa tin shekaranjiya da hajiyarsa tafara labour.

AURENTA ZANYIWhere stories live. Discover now