AURENTA ZANYI....19/20

266 27 0
                                    

_*AURENTA ZANYI...._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

   _19/20...._
Sannu ahankali shak'uwa da kusanci sukacigaba da shiga tsakanin mashkur da bunayya, har yanxu baidaina kula daita ba dakuma yimata yan nasihohi akan takare martabarta ta y'a mace, Alhmdllh kuma tanajin maganarsa sosai sbd ayanzu jinsa take kamar d'an uwanta najini.

Idan baiganta wajen karatuba kokuma masjid kokuma restaurant tosaiya nemi hamdallah yatambayeta ina take, nan hamdallah zata fadamasa, haka itama idan tai kwana biyu bata gansaba dakanta take zowa nemansa agun abokanansa jalal da majnun.

Suna acikin wannan yanayin har suka kammala zana jarabawa sukai Hutu.

Kokad'an bunayya bataji dadin hutun ba sbd yanda tafara shak'uwa da sabon brother d'inta.

Bata ankaraba damuwar rashin ganinsa kwana biyu tafara kusantota, saitaji batasan zama acikin mutane any time tana d'aki itakada'ai tana tinanin brother d'inta, gashi tai ragon tinani batada ko number dinsa hakama dik abokanansa bawanda takeda number dinshi bare takira tace a turomata.

Haka taita fama da kewarsa dakuma damuwarta har momy ta fahimci tanada damuwa,amma data tambayeta saitace bakomai gajiya ce kawai ke damunta, saidai momy kam bata yardaba sbd taga tarin canji agun bunayya.

     Yau takasance Monday itakad'aice a gida momy da dady dik sunfita office,yanzu tariga tasaba da hayaniya sam bata iya zama itakad'ai,danhaka tashirya tadauki motarta tafice gidansu hajiyar dady, acan tawuni sai dare sannan tadawo.

Haka tadingayi kullum har tai sati daya da dawowa school,kuma tanajin dadin zowanta sbd koba komai tana rage kad'aici da tinane tinanen brother d'inta mashkur.

Yau takasance Saturday danhaka su dady nagida kowama yana gida tinda weekend ne, dady da ya Amir suna waje bakin lambu sunashan iska,itakuma bunayya da momy suna cikin gida a parlor hadimai kuma kowanne yana aikinsa.

Zaune kawai take amma gaba d'aya ruhunta da zuciyarta basa a gangar jikinta,ta lula tai nisa sosai acikin duniyar tinanin MASHKUR, itafa sai yanzuma take hango tsintsar kyanda yakeda harma take ganin dik kyanda ake fadar tanadashi gani take kamar mashkur yafita, komai nasa is accurate from face to his foot, mashkur irinsane yammata ke mafalkin samu arayuwarsu, kai auren irinsama fitinane wlh sbd yammata bazasu barka kai yanda kakeso dashiba.
  Wani dan murmushi tai wanda batamasan tayisaba lkcnda tatino da bakinsa mai d'aukeda pink lips sadda tayanke da wuka tayakaita clinic ana dressing din wajen tana kuka shikuma yanamata wasa yana tsokanarta dikdan tabari ayi dressing din agama.

Itakanta tasan yana matuk'ar shagwab'ata tamkar yayanta na gaskiya.

Tanacikin tinanin batasan momy nakirantaba har saida ta tab'ata sannan tai firgigit tadawo hayyacinta, momy tace "what's wrong with u bunayya....are u okay, me kike tinanine haka bunayya inata kiranki amma bamakya jina" murmushi tai tareda rufe fuskarta cikin yanayin kunya,karo nafarko kenan data farajin kunyar mahaifiyar tata tace "am okay mom...bakomai" momy ta tab'e baki tareda fadin "idan tai wari maji" saitai dariya momy tace.

"Kije dadyn ki yana nemanki a waje" ohk tafada tareda mik'ewa tafice.

Ahankali take tafiya izowa lambu, sanye take da wandan jeans blue iya guiwa da riga mai gajeren hanu pink, kanta yar hulace akai.

Tindaga nesa tahango mutum durk'ushe a kusa da dady suna magana saidai bata hango fuskarsaba bayansa ne kawai take hangowa.
  Tana isa saitace "dady..." saiya kalleta cikin murmushi yace "mashkur ne yazo yanzu" saida gabanta yafad'i dataji sunan mashkur.

A fili tamaimaita mashkur cikin tsintsar mamaki, mik'ewa yai tsaye yana dan murmushi,waro dara daran idanuwanta tai cikin tsintsar mamaki tareda rufe bakinta lkcnda sukai ido biyu.

AURENTA ZANYIWhere stories live. Discover now