_*AURENTA ZANYI....._*🌷
_Wattpad@Aufana8183_
_43.....END_
Rayuwa tacigaba da tafiya inda cikin yanzu cikin momy yatsufa sosai yaisa haihuwa koyaushe yanzu jiran zowan haihuwar ake.Bunayya sunshiga 300level yanzu har yanzudai haihuwa shuru ba ciki ba lbrnsa, tin abun baifara damun momy da mashkur ba haryafara damunsu musamman momy dan tamafi mashkur d'in damuwa,saidai itakam gogar ko ajikinta mamakinsu ma take yanda suketa damunta da maganar cikin.
Ita bamataso tai ciki yanzu sbd ga wahalan karatu ina zata iya da wahalan ciki musamman yanda taga momy tawahala da wannan cikin, ga amai ga kyankyami wannan takeso batasan wancan, sannan bakomai takesan kamshinsa ba, ita yandama taji lbrn labour yafi d'agamata hankali shys kokadan batawani d'ana hankalinta ba.
Sannu ahankali akafara shirye shiryen bikin ruwaida da ya ramadan, yanzu kusan dik bayan sati daya ko biyu sai ya ramada yazo yola gun habibiyarsa.
Anacikin shirye shiryen biki kwatsam saiga haihu tazowa momy, bunayya na school aka kirata aka fadamata momyn ta tahaihu,cikin farinciki takira mashkur dake habuja shima tafada masa, dagacan school tafice kebbi.
Koda taisa har sundawo daga hospital babyn na hanun yaya hauwa, cikin zumud'i da tsintsar farinciki ta karbi babyn tana tambayar yaya hauwa me aka haifa,yaya hauwa tafadamata namiji ne kamanninsa sak dady ba abunda bai d'akkoba na dady, aunty kuluwa dataji kama yaron yake da dady saitace Allah isa karya d'akko halinsa, nan akaita dariya.
Ranar bunayya da momy kwanan farinciki sukai da wannan abun alkhairin daya samesu,bunayya tace "momy ashe Allah yarubuta bazaki mutuba har saikinga jininki a duniya" cikin murmushi momy tace tana shafa fuskar bunayya "bunayya koda ban haihuba harna koma ga ubangiji na bazan tabajin bak'incikiba sbd yabani ke kyauta batareda nasha wahalar nak'uda ko kayan cikiba, ke d'ayace tamkar dubu agareni, kinzamoman tamkar yaya goma koma fiyeda hakan, nasameki a lkcnda nake tsananin buk'atar yaya haka kuma kin k'aunaceni a lkcnda nai kusa narasaki kikace bakyasan kowa saini,tin a lkcn naji nadaina kwad'ayin haihuwa a duniya nad'aukeki y'ata wacca natsuguna na haifa,
Sbd haka wannan haihuwar danayi yanzu wlh bawani abun dazai rage na tarin soyayyarda nake maki bunayya, tabbas kam nayi farinciki nakumayi gdy ga ubangiji daya bani haihuwar amma har jibi keta dabance a zuciyata kuma acikin y'ayana, bunayya inaso kisani naraba dukiyata biyu namallaka maki rabinta rabin kuma nabarwa wannan d'an dana haifa dama wasu dazan haifa idan Allah yabani" kwallah ke zuba a idanuwan bunayya, batasan lkcnda tarungume momynta ba cikin shauk'in soyayyar y'a da uwa.
Tana fadin "ngd sosai momyna da irin soyayyarda kika nunaman tin ina acikin tsumman goyo har izowa yanzu, Allah ibarmana ke momy, yanzu kinga Allah ya amshi addu'ahta yabani d'an uwa wanda nima zan kalla ince k'anenane" sai momy tai dariya.
Sai bayan kwana uku da haihuwa sannan mashkur yaiso haka shima yamak'e babyn ajikinsa kamar yalasheshi yakeji sbd mashkur akwaishi dasan yara sosai, samuwar wannan babynma saiya tasomasa da san haihuwarsa, bunayya dik kwanakinda akai tana mak'ale da babyn kota goyeshi kokuma tarungumeshi idan suna parlor, sai idan yai kuka sannan takaisa gun momy yasha nono kokuma idan yar barka sunzo.
Ranar koda mashkur yazo yataddata tawani rungume babyn kamar zata bashi nono saiya harareta yace "kiyi zuciya kema ki haifomana namu babyn mana, da wannan mak'ale babyn momy dakikeyi" dariya tai sannan tace "nak'i din,anki ayi zuciyar" hassala yai yaje yamatseta tana ihu ya karb'e babyn yafita dashi, kukan shagwab'a tasamasa tana fadin "momy zoki amshi babynki ya mashkur zaitafiyarmaki da baby" momy najinsu tasharesu tana dariya kamar batajisuba.
A ran daren suna dady ya aiko yana rok'on alfarma gun momy dan Allah tabada yaronshi akaimasa yagansa sbd yanzu andawo dashi gida yanacigaba da jinya sbd uncle Muhammad yace yajanye k'arar asaki dady kawai shys aka sakesa aka maidasa gida yak'arisa jinyar.