AURENTA ZANYI....7/8

340 30 0
                                    

_*AURENTA ZANYI....*_🌷

_Wattpad@Aufana8183_

   _7/8......_
Koda taje parlor momyn ta nakan laptop tana aiki, zama tai a kujerarda ke kusa daita tana fadin "momy...hala dady London zaije" gun d'ayar matarsa kenan momyn ammar.

Batareda tad'ago ba tace "eh,kinsan yau kwananta ne" tab'e baki tai batareda tasake cewa komaiba, can takwallawa cookie dinsu kira "roben...roben where are u wai.." tafad'a da k'arfi, dagudu wanda takira da roben yazo yana fadin "yes ma, am sorry ma am here" wata muguwar harara tagalla masa tareda watsa masa harara kamin tace.

"Oya..go and help me with some food, am so feeding hungry wlh" dasauri yace "ok ma" tareda juyawa izowa kitchen, kwanciya tai kan kujerar tareda fara latse latsen wayarta.

Acikin yan mintinanda basufi 5 ba yakawomata abincin tafaraci tana cigaba da latsar phone d'inta.

Bayan tagama yakwashe kayan yakai kitchen.

Around 8:30pm tafara shirinta cikin wata had'addiyar gown pink color mai tsadar gaske dagani ma yanxune tafara sakata dan ga ledarta nan datafitarda ita daga ciki, powder kawai tashafa mawa fuskarta sai lipstick white mara kyalli.

Bayan tashafa sannan ta taje sumarta gu d'aya da ribbon mai kyau nantake fuskarta tafara haske tana kyalli tamkar hasken farinwata a sararin samaniya ranar daren 17.
     Tsaye tai tana kallon kanta a mirror saitai d'an murmushi wanda bansan ma'anarsa ba.
Ahankali taje tad'akko takalmanta hills pink masu kyau tasaka, bayan tasaka sannan tafeshe jikinta da tirare dan bunayya kwaita dasan k'amshi sosai.

Bayan tagama sannan tad'akko wata yar jakar hanu itama pink color ce tasaka wayarta aciki sannan tafita.

Kai tsaye bedroom din momyn ta tafice, koda taje tana sallah danhaka tatsaya tajira harta k'arisa, bayan tagama saitace "please....! momy borrow me your car" kallonta tai sama da k'asa sannan tai murmushi tace "where are u going bunayya...?" itama D'an murmushin tai tace "am just going to birthday party na jasmine, I think bazanma dad'e ba bcoz....tai inviting samari dayawa, so nikuma I don't like hakan tasani itama" momy batasake cewa komaiba.

Dahanu tamata nuni da key car din tad'auka tareda ficewa.

      Hmm...lkcnda naga tafito da motarda zata fita daita tsaye nai nawage baki da ido da hanci ina kallo sbd tsabar had'uwarta, haka tafigi motar dak'arfi tafice.

Koda taisa kowa Wurin yacika sosai fam da y'ammata da samari, fiye da rabin wurin yayanmu ne na africa, some karatune yakaisu some kuma tareda iyayensu suke kamar bunayya.

Tin 8:30pm aka fara party din amma ance sai 12pm za'agama, itakam 10:30pm dot tabar wurin takoma gida abunta, koda takoma dik a gajiye take danhaka wanka kawai tai tabi lafiyan gado.

Washe gari ma lettin tashi tai dan sai 7:30am ta tashi, aikwa dagudu tafada toilet tai wanka tafito tafara shirin school, dasauri harta gama ta d'auki school bag dinta tafice, yaukam bata tsaya yin break ba tafice.
    
    Kimanin kwana hud'u dady yai a London sannan yadawo, aikwa koda yadawo daga momy har y'ar tata sunyi matuk'ar yin missing dinsa haka shima, kamar yanda yake al'ada agunsa dik yaje idan zaidawo saiyayowa abar k'aunarsa tsaraba, to yanxuma hakan take.

Hakan wasu english wears ne yasiyo mata masu kyau kala kala kasancewar tafisan wandina shys yafi siyomata su, zan iya cemaku Alhj kadel shine wanda yake bama bunayya gudumawa wajen tasaka kaya irin na arna, wai acewarsa haka yanayin k'asarda suke yake ai idan sunkoma gida Nigeria zata bar sakasu, hmm.

Shys tinda taso har izowa yanzu batasan saka kayan yarenta ba batamasan miye atampa ba sbd itama mahaifiyarta ba sakawa takeba, haka dik wata mace yar asalin Nigeria datazo kasar bawacca kesaka kayan hausawa ko yarenta saidai English wears hakama yayan nasu suma.

Yanxin ma wani tsingilallen wando ne ajikin bunayya girmansa iya cinya kai baima k'arisa rufe cinyoyinta ba, sai wata yar singlet fara mai gajeren hanu kanta sam ba mayafi ko d'ankwali, kai idan kaganta sam bazakace musilma bace kuma jinin musilmai.

Kwonce take akan kujera tana assignment momynta na a k'asa a kishingid'e tanashan fruits, dady ne yashigo d'auke da wasu kayan a hanunsa,cikin murmushi yazauna yana fad'in "bunayya zomuga kayan nan ko zasu maki" dasauri tamike tsaye tana dariyar murna taxo agabanshi tatsaya.

Wani wando ne yad'akko yad'ora a k'ugunta wanda shima girmansa iya cinyoyinta ne, cikin faraa tace "ai xaiyi dady kagama irin najikinane" momy ma dake k'asa tace "zaimata ai, kasan halin k'ugun nata sai a hankali" dariya sukai sudika dady yace.

"Bakomai,munji dai inkin isa kiyi kamarsa" tai dariya tace "nikam mema zanyi dashi yanzu nida na tsufa" bunayya tace "laaa....kai momy ina tsufa yake anan, wlh yanxu haka class mates dina cewa suke wai ke yayata ce ba momy na ba" daga momy har dady dariya suka kwashe daita.

Bunayya kam tattara kayanta tai tafice d'akinta itama tana dariya, dady yace "sauran kayan suna a bedroom dina kije ki d'akko" toh tace sannan tafice.

         Washe gari takasance weekend danhaka kowa yana gida, kamar yanda suka saba weekend a gidan gonarda momy tasiya anan Australia sukeyinsa domin susha fruits kamar yanda suka d'aukarwa kansu shan fruits dik a weekend domin samun wani sinadari a gangar jikinsu.

Danhaka tin 9am suka shirya suka tattara sudika a gidan hadda masu girki da shara da dai gyaran gidan, mota uku suka cika suka fice.

Koda suka isa tini antsabtace gidan danhaka bawani wahala,
Bunayya dai swimming pool tafice taita wankanta sukwa su momy garden suka fice domin shan fruits.

Bayan bunayya tagama sannan taje tacanja kaya izowa wandan jeans bak'i girmansa iya guiwa da riga bak'a mai dogon hanu, bayan tashirya sannan tajegunsu momy.

Da dare sunjima sosai sunashan fira kamar yanda suka saba, dady nabasu labarin yarintarsa shi da yan uwansa sai shan dariya suke hadda rik'e ciki, sai kusan 10pm sannan sukaje suka kwanta shima saida sukaga bunayya tai bacci dan dadyne ma yad'auketa yakaita bedroom d'inta sannan sukuma suka fice.

Washe gari haka suka wuni cikin nishad'i acikin garden, sai 5pm sannan suka tattara suka koma gida.

Haka farinciki da jin dad'i suke cigaba da gudana acikin wannan ahalin.

Bunayya tacigaba da karatinta cikin walwala yayinda iyayenta kuma suke cigaba da gudanarda kasuwancinsu acan, yanzu abun harma yak'ara hab'aka dan sun fara ginin k'aton company a gida Nigeria mai d'aukeda tambarin sunan BUNAYYA, sunce sungaji da yawon k'asashen nan.

Dady kuma yace yanaso yahad'a kan iyalinsa gu d'aya kodan shak'uwa tashiga tsakaninsu kuma susan danginsu dakyau,amma wannan na london wannan Australia tin tasowarsu har girmansu taya zasusan danginsu kuma suso junansu.

Danhaka yamatsawa ma'aikatan ginin dasu matsawa aikin.
        Anahakan saiga wani business din yafito masu wanda zasu samu riba sosai acikinsa a London, danhaka suka tattara sukabar Australia suka koma London, saidai ba'a wuri d'aya suke dasu momyn ammar ba.

Kokad'an bunayya bataji dadin dawowarsu London ba sbd yanda tashak'u matuka da friends dinta,takuma saba sosai da k'asar tanajin dadin kasar sosai,
     Bayanda taiya haka tacigaba da rayuwa a London inda izowa yanzu harsunyi wata biyu da dawowa harma tafara zowa school a sabon school dinda aka maidata yanzu.

#/Vote nd' Comment..
#/Aufana for life.

AURENTA ZANYIWhere stories live. Discover now