AURENTA ZANYI......29/30

283 29 3
                                    

_*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

   _29/30....._
Kuka momy keyi mai tsanani tana fad'in "haba kadel haba haba...wannan wane irin gurb'ataccen tinanine zuciyarka keyi,kada kabari zuciyarka ta rinjayenka mana,katinafa bunayya y'a take agaremu ba k'anwa ko y'ar uwa ba,kadel taya zaka furta wannan kalmar ta SO tsakaninka da bunayya" shikansa kwallah yake zubarwa waenda yakasa sanin namiyene.

Cikin muryar kuka yake fadin "nima bansan sadda abun yashiga zuciyata ba Maryam,nadade ina d'awainiya da SON bunayya,wannan dalilin ne yasa nahana kowanne namiji ya rab'eta dasunan soyayya ko san aure badan komaiba saidan naji saukin samun kanta wajen amincewa dani, wlh maryam bazan taba iya rayuwaba idan ban auri bunayya ba,nikad'ai nasan irin k'aunarda nakemat...." bai k'arisaba momy tai wata k'ara mai sautin gaske tareda furta "ya'isa haka kadel,banasan nasakejin wannan maganar".

K'ararda tai yasa hankalinsu aunty kuluwa yatashi sukayo d'akin dagudu domin ganin abunda ke faruwa, momy naganinsu taje da gudu tarungume aunty kuluwa tana kuka mai tsanani,gaba daya hankalinsu yatashi matuk'a ganin momy da dady suna kuka,tambayarsu suka shigayi a firgice abunda ke faruwa.

Dakyar momy taiyayin magana cikin sheshekar kuka "kufad'amasa yajanye k'udurinsa na auren bunayya dan Allah,nayi nayi amma yadage akan saiya aureta wai,nikuma wlh bazan iya zama da y'ata a matsayin kishiyata ba,wlh mutuwa zanyi dik yak'i daina wannan maganar".

Gaba daya sun rikita kwakwalwar su aunty kuluwa sam sunkasa fahimtar inda zancensu yadosa,cikin rashin fahimta yaya hauwa tace "wai jolde me kike nufine,kunsakamu acikin rud'u kun rikitamuna kwakwalwa, kumana kyakkyawan bayaninda zamu fahimta dan Allah mana" momy kuka take sosai kamar ranta zai fita,shikowa dady yadafe kansa da hanunsa d'aya.

Dakyar momy ta sausauta kukanda take sannan tafara masu bayani sbd tasani yau ranar bayyanar asirinda suka dad'e suna rufewa ce tazo,saidai bata tab'a tinanin kadel ne silar fallasar wannan sirrin ba,nannauyan numfashi tasauke had'eda shesheka sannan tafara magana cikin muryar kuka.

     "Kuyafeni aunty kuluwa, dan Allah kugafarceni sannan kuyiman kyakkyawor fahimta akan kuskurenda na aikata abaya wanda babuwani mahalukinda yasani sai kadel da doctor haji,saikuma ainahin iyayen bunayya dasuka sani yanzu"  mamakine yabayyana k'arara a fuskokinsu aunty kuluwa,sai momy tacigaba da magana.

"Hak'ika sai yanzu ne nake nadama dakuma dana sani mai tarin yawa,batareda dogon nazari dakuma zurfin tinaniba nabiyewa kadel muka aikata babban lefin wanda akarshe yanzu nine narufta aciki,saidai wlh insha Allah koda zan rasa dik abunda na mallaka ne bazan taba bari hak'ar kadel tacimma ruwa ba" yaya hauwa tace "munajinki jolde" sai tacigaba da magana "a lkcn shekarun baya lkcnda nake neman haihuwa ido rufe a lkcn ne na amince akamun dashen kwayayan haihuwar kadel a mahaifata, cikin ikon ubangiji kowa saiga ciki ya bayyana a mahaifata,nayi matuk'ar farinciki hakama ku dangi musamman ni sbd koba komai zan rabuda gori da wulakancin uwar mijina wacca a kullum takeda burin rabani da mijina, bayan cikina yaisa haihuwa mukaje asibiti nahaihu,

To saidai wani iko na ubangiji sai haihuwar tazo da matsala sbd babyn yamutu tin aciki,dagani har kadel munshiga tsananin tashin hankali musamman ni sbd a lkcn banaji bana gani idanuwana a rufe suke domin samun d'a, to hakan ne yasa kadel yasamu wani doctor haji yarokesa yakuma biyasa mak'udan kud'i domin yab'oye mutuwar babyn mu tahanyar yin exchanging babyn mu dawani babyn, haka kowa akayi sai aka canja namu babyn da bunayya.

Amma asali mu namu babyn yamutu, nad'auki bunayya nakuma so ta tamkar y'arda nahaifa acikina kai har gobema jinta nake a zuciyata amatsayin d'ana dana haifa yamutu,saidai ashe shi kadel bahaka yad'auketa ba, bunayya tahad'u da mashkur makaranta wanda yana ganinta yafara bincike akanta sbd tana matuk'ar kamanceceniya da wata kanwarsa ruwaida,koda komai ya kamkama ashe bunayya tagwayece ita ruwaida itace abokiyar tagwaicinta, dafarko abun yadauki zafi daga karshe Allah yadaidaita komai iyayenta na haihuwa suka barmana ita har abada.

AURENTA ZANYIWhere stories live. Discover now