_*AURENTA ZANYI...._*🌷
_Wattpad@Aufana8183_
_33/34....._
Rayuwa tacigaba da tafiya cikin farinciki da walwala,bunayya karatinta tasaka agaba sbd yanzu kwana biyu kacal suka ragemasu sufara zana jarabawa,yayinda a b'angaren ango mashkur kowa yaketa k'okarin ganin yakammala project dinsa nanda sati d'aya kacal zasu kammala komai na degree dinsa nabiyu.Kimanin sati d'aya kenan rabon mashkur yasaka bunayya a ido sbd yanayin karatinsu sudika gaba d'aya,bawanda keda lkcn kansama acikinsu kowannensu k'okarinsa yaga yasamu sakamako mai kyau.
Saidai mashkur kam gaba d'aya bayajin dad'i sbd rashin ganin hasken idanuwarsa kuma sanyin idanuwansa,haka itama bunayya tana kewar yayan nata amma kunya tahanata tanemesa bare ta tambayesa koda agun abokanan karatinsa ne, a wayama bawani cika yin waya sukeba,hakan yasa kewar junansu tamasu katutu acikin zukatansu.
Sannu ahankali har su bunayya sukafara zana jarabawan first semester ta 200level, abun ba sauk'i kokad'an saidai ace Alhmdllh amma sunashan fama kam,any time suna wajen karatu dikta rame tak'arin haske sbd dama can bunayya badamuwa tai dacin abincin kirkiba sai mashkur yaita fad'a koya sakata agaba sannan takecin tuwo ko shinkafa,ita bartadai da kayin mak'u lashe,to bare yanzu da exam tasa ruwanta shkn sai k'arisawa kawai.
A ranarda sukacika one week da fara exam aranar mashkur yakammala komai suka fara shirin tafiya gida,tin 3pm yasaka anemomasa bunayya amma baagantaba kaf school din sai kusan 5pm sannan akazo aka fad'amasa suna cikin exam,kokad'an baiji dadin hakanba yaso matuk'a yaga bunayya sbd yana k'ishirwarta sosai,gashi kuma tin 2pm akazo d'aukansa amma sbd ita yahana sutafi har wannan lkcn, neehal k'anwarsa ta uku da'akazo d'aukansa daita tace "haba brother,kazo mutafi mana,aunty bunayya fa takace nanda wani d'an lkc za'akawoma ita kaita ganinta kana kallonta har kagaji,tomeyasa zaka wani tsaya kace dole saikaganta yanzu,wlh mungaji sosai ni yunwama nakeji momy kuma sai kira take inacemata har yanzu bamuko tasoba bare har mu'isa gida" sauran yan uwanta najin tayi magana nan suma suka saka nasu bakin sunamasa magiya.
Aiko badan yasoba dole yashiga mota suka fice batareda yaga abar k'aunarsa ba.
Bayan su bunayya sunfito hamdallah kefad'amata mashkur yasaka akirata amma lkcn tana d'akin jarabawa harya wuce,yaune suka kammala dik sun wuce gida yan masters degree din nan, bunayya kamar tai kuka dataji lbrn nan hamdallah taita mata dariya.
Haka itama suka cigaba da zana exam dinsu ahankali,dik bayan kwana biyu mashkur yakan kirata susha soyayyarsu kamin daga bisani yabarta tacigaba da karatinta na exam.
Sannu ahankali lkcn biki ke k'ara k'aratowa yayinda aketa cigaba da shirye shiryen shagalin bikin.
Aunty kuluwa tini takira mai gyaran jiki domin tafara aikinta sbd sati biyu kacal yarage afara bikin sbd haka tanaso amata gyaran tsawon sati d'aya,itakuma bunayya gashi basu kammala exam ba.
Dahaka aunty kuluwa tahak'ura har suka kammala exam din sannan tadawo gida dikta rame.
......................Kamar koyaushe momy ce zaune akatafaren parlon ta tanashan fruits tana kallon news a aljazeerah channel, bunayya kowa kwance take akan center carpet tanacin tufa,sanye take da kayan bacci riga da wando iya guiwa,kanta bakomai sumarta dikta barbaje akan pillow dinda kanta yake akai.
Ahankali momy takalleta tace "waikekam bakya shirin komaine,naga bakima damuba matsayinki na amarya" wata iriyar kunyace taji takama saitai d'an murmushi murya k'asa kasa tace "toni wane shirin zanyi ne bayan wanda ku kukeyi" waro ido momy tai tace "lallai yarinyar nan,amaryace zatace wane shiri zatayi na bikinta,koda yake bazanga lefinki ba tinda bashiga mutane kikeba bare kisan yanda akeyi" saitace "to kingani,nikam ina nasan shirinda akeyi".