AURENTA ZANYI.....17/8

265 31 0
                                    

_*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

   _17/18...._
Zaune suke acikin room d'in hamdallah sabuwar k'awarda bunayya tai anan FUBK, wata yar mitsitsiyar rigace ajikinta ta bacci sai d'an pant,itakuma hamdallah towel ne ajikinta da'alama daga wanka take.

Abinci sukeci atare indomie da dafaffen kwai,sunaci bunayya na chart itakuma hamdallah tana duba wani littafenta, bunayya tace "yar uwa" kamar yanda suke kiran junansu kenan "kinsan Allah idan bamuyi dagaskeba Mr habeb saiyabamu mamaki da muguntarsa,kinga dama yanajin haushinmu da surutu awajen lecture" hamdallah ta tab'e baki tareda fadin "hmm..bari kawai yar uwa,nima naga alamar idan bamu nunamasa munsan kanmuba bak'aramin mamaki zai bamuba wlh".

Bunayya tace "bari kawai,aikwa zamu bashi mamaki insha Allah, Allah dai yataimakemu yakuma azamu akanshi,sbd bak'aramin mugu bane wlh,zai iya cutarmu koda gb dinmu yai kyau" hamdallah takara gyara zamanta tana fadin "Allah yafisa yar uwa,muyita addu'ah kawai dakuma karatu" nan suka sake dakko wata firar har suka kammala cin abincin.

Bayan sungama sannan bunayya tashige toilet domin yin wanka,koda tafito tini hamdallah tashirya tsab acikin gown ta material yellow da d'an mayafi wanda tad'an d'ora akanta kasancewar ba d'an kwali akanta.

Cikin sauri bunayya tashirya acikin wandan jeans dark blue da riga fara wacca tad'an sakko mata tarufe matasan zamanta, saita taje sumarta sannan ta tufketa gu daya sannan tasaka yar hula akai, saikuma d'an k'aramin mayafi data dora kan shoulder d'inta, daganan tasaka tirare sannan tadauki handout d'inta da phone d'inta suka fice.

     Tin 8am dasuka fara lecture sai 6pm sannan suka fito gaba daya, dik agajiye suke bazasu iyayin girki ayanzuba, danhaka kawai suka fice wani sabon restaurant da aka bud'a nan domin suci abinci,
Koda sukaje wurin acike yake kuma samari sunfi yawa,danhaka kawai sukai takeaway suka fice.

Suna cikin tafiya saisukaji anamasu magana a bayansu, saisuka tsaya batareda sunjuyoba, cikin bacin rai yafara magana "ruwaidah ya inata magana kinajina kuma zaki kyaleni, kinsan banasan iskanci koh koni sa'anki ne dahar zan dinga kwallah maki kira kinaji kuma ki kyaleni,tukuna ma meya kawo school dinnan a wannan lkc...?" dik maganarda yake kallonsa kawai suke dan basuma fahimci inda yadosa ba.

Bunayya ce tacemasa "kai mallam,mufa bamu fahimci inda zancenka ya dosaba, inma wani abun kake nema kai hkr dan bamu gansaba" tana gama fadar hakan tajuya zasu tafi saiyai saurin shiga gabansu.

Cak suka tsaya cikin bacin rai saiyacigaba da fadin "wlh banasan iskanci,yanzin nan saina sassab'amaki wlh" abun nasa mamaki ma yabasu, bunayya tace "waikai wane irin mutum ne, idan har kama kaga munmaka da wasu to basu bane,kajaye kabamu hanya sauri muke yunwa mukeji abinci zamuci, kobakaga yanzu mukai takeaway ba" shuruu yai yana karewa bunayya kallo tindaga samanta har k'asanta kamin yace "baiwar Allah yasunanki dan Allah..?" dan murmushi tai sbd tafahimci yagane kurensa da'alama kama yaga tamasa da wata shys tamasa uzuri kawai amma badan hakanba daya yabawa aya zak'inta.

"BUNAYYA..." kawai tafada tana fice hamdallah itama tabi bayanta, har suka k'uremasa bai daina kallonsu ba,saida yad'auki tsawon mintina cikin al'ajabi da mamaki sannan yafice.

Sukwa suna zowa room din bunayya sukaita dariyarsa yanda yadage akan lallai bunayya itace wata wai ruwaida,
Saida suka gama dariyar sannan suka fara cin abincin, bayan sungama anan sukai wanka suka canja kaya sannan suka kwanta sud'an huta.

Y'ar fira sukeyi ahankali bunayya naduba wani handout.

          Around 10pm suka fita karatu kaman yanda suka saba, masallacin school din sukaje, koda sukaje again saisukaga wannan mutumin daya taresu yana kiran bunayya da ruwaida, aikwa basusan lkcnda suka tintsire da dariya ba, shima d'an murmushi yai tareda k'urawa bunayya ido, can wani gu suka samu suka zauna,shikowa bayan yagama abunda yakawosa saiya fice.
  Sai kusan 4am sannan suka koma hostel kunsan yanayin rayuwar school yanda take ba'awani baccin kirki,danhaka suka koma ma dakyar suka samu sukai bacci.

AURENTA ZANYIWhere stories live. Discover now