_*AURENTA ZANYI....._*🌷
_Wattpad@Aufana8183_
_39/40...._
Yaukam bunayya tayi baccin gajiya, da asuba bayan tayi sallah ma sake kwanciya tai bacci mai nauyi yasake d'auketa, saikusan 10am sannan tafarka,koda tafarka su hamdallah harsun gama had'a breakfast danhaka tafice toilet tai wanka sannan tafito tashirya cikin wani tsadajjen material light pink mai kyau.D'inkin gown ne da d'ankwali sai mayafi white color da wasu plat shue white color suma, bawani make-up tai powder ce kawai sai lipsticks da kwalli amma tayi kyau sosai abunka da amarya sai kyalli take tana shining, bayan tagama shirin sannan tafita tasauka k'asa gunsu hamdallah.
Atare sukayi break sunata firar shagalinda akayi na jiya gun dinner sunata dariya har suka kammala, bayan sungama sai suka dawo main parlor suka zauna.
...................A b'angaren angwaye kowa, sunacan gidansu mashkur a side d'in mashkur, tini suka kammala had'a masa kayansa tsab izowa gidansa, su mahbub sai sharri suke masa wai yaje gidansa yabarmasu gidansu sun koresa, shikwa sai murmushi yake dayake mashkur ba ma'aboci irin yawan maganarnan bane.
Bayan sunshirya tsab saisuka shiga cikin gida suka gaishe dasu dady sannan suka fita, sunyi matuk'ar yin kyau sosai daka gansu kasan y'ayan masu gomnati ne, sunacikin naira suna wanka daita, acikin dank'ara dankaran motocinsu suka fita kowacce kagani kasan bak'arama bace.
Kai tsaye gidan amarya suka fice acikin mota sai iskanci sukamawa ango mashkur sunamasa irin wasan abokanan ango dai,shikowa sai hararansu kawai yake yana murmushi.
Bayan sun iso sukai parking suka fito sannan suka fice izowa ciki.
Su bunayya na cikin parlor sukaji sallama dakuma hayaniya kamin ayi nocking, nafisa ce tad'an leka saitaga ashe angwayen ne, aikwa dasauri tafadamawa su bunayya nan aka shiga k'imtsawa, saida suka gama kimtsawa sannan tabude k'ofar.
Atare suka shigo nan aka shiga gaggaisawa sannan suka zauna,bayan sun zauna nan fira tab'arke tsakaninsu, dik abunda akeyi bunayya dai bata saka bakintaba tai zamanta tana saurarensu idan akai abun dariya tayi murmushi tai zamanta takuma rufe jikinta da mayafinta.
Hmm readers nifa har mamakin hankalin da bunayya tai nake,kamar ba bunayyar London ba, Lol Allah ik'ara shiryardamu Ameen.
Mashkur kowa yanad'an tsoma bakinsa aciki, sadiq da mahbub sunfi kowa surutu hamdallah kowa tace tafisu bakin nan akaita kacamewa anayi, kamin daga bisani suna bamawa kowacce k'awar amarya tirmin zane na super wax wacca ak'allah kud'inta zasukai 35 thousand naira dakuma kud'i naira dubu ashirin sannan had'eda kayan biki waenda akayi, saikuma dankara dankaran motoci har uku waenda zasu maidasu har gidajensu.
Godiya su hamdallah sukayi sosai, daga bisani angwayen suka fita.
Anan su hamdallah suka wuni saikusan 5:45pm sannan suka kammala shirin tafiya gida, bunayya tarik'e hanun hamdallah tana hawaye musamman lkcnda suka fito zasu shiga motoci aifa nan tak'ara rikicewa wai karsu tafi subarta, kuka kowa take ba kaukautawa tanata sharan kwallah danma tana ganin idonsu mahbub ne da yanzu tafara dirar k'afafuwa tana kukan mai sauti to saidai bahali.
Dakyar hamdallah tasamu tafukce hanunta tashige mota sbd ita kad'ai ake jira, shima saida mashkur yacire hanun sannan tasamu tafice,hamdallah ma saida tai kuka sbd ganin bunayya nayi,aikwa motocinsu na tashi bunayya tafice dagudu cikin gida tahaye sama tashige bedroom d'inta tarufe k'afar.
Su mashkur kowa bayan su hamdallah sunfice fita sukayi daga digan.
Bunayya kowa dataga ba sarki sai Allah saita d'akko wayarta tadingayin game tana rage tsawon lkc, saida akayi magrib taji ankira sallah a masallacin unguwar sannan ta tashi tashiga toilet tad'auro alwala tafito.