AURENTA ZANYI.....37/38

312 32 1
                                    

_*AURENTA ZANYI....._*🌷

_Wattpad@Aufana8183_

  _37/38...._
Ranar yau ta ahalin shuwa arabs ce, tinda yau ake Arabians day, dik girman holl din Royal event saida yacika taf da shuwa wasuma harsun rasa gun zama sai tsaye sukayi.

Amarya da yayyenta mata da yan uwanta mata dakuma k'awayenta dakuma iyayenta mata da maza dan hatta abban ramadan yaje, momy dataje batawani jimaba tafice wai ita kunya.

Anci kuma ansha anyi ankuma gudanarda al'adu daban daban na yaren shuwa, daga bisani akai pictures sannan aka watse kowa yakama gabansa.

     Washe gari itace ranarda za'ayi walima itace kuma ranarda zaa d'aura auren mashkur da bunayya, da dare kuma a gudanarda dinner amma ita a yola zaayita sbd abokanan mashkur ne suka d'auki nauyinta.

Har safiya tawaye bunayya bata rintsaba sai faman juyi take akan gado zuciyarta acike da tarin mamakin wai itace za'ad'aurawa aure gobe, a wani b'angaren kuma tarin kewar mahaifiyarta ne yamata katutu yahanata sakewa,gakuma tinani da tausayin halinda dadynta yake aciki,musamman idan ta tino da irin daddad'ar rayuwarda sukai abaya tindaga Australia har London.

Bata ankaraba kwallah suka fara bin kuncenta,ta d'auki abunda yafaru amatsayin k'addarar rayuwarta kawai, zakuma ta dauwama tana yiwa mahaifan nata adduah dakuma fatan dacewa gobe k'iyama, sunrik'eta rik'o nakwarai sunkuma kula daita sunbata daddad'ar rayuwa wacca take cike da tarin farinciki da jin dad'i.

Saikusan asuba sannan bacci yad'auketa.

Washe gari ranar d'aurin aure anko tayi da momyn ta, wata tsadajjiyar shadda suka saka gizna light blue mai shegen kyau akamasu dinkin gown aka saka mata stones agaba, bayan sunshirya sai akamasu pictures masu kyau.
   ......................

Around 10am dot aka d'aura auren MASHKUR ABDULLAHI da FATIMA KADEL KABIR akan sadaki mafi tsoka naira dubu d'ari cif masha Allah,abban ramadan shine uba shiya bada auren inda abban ruwaida yazama uban mashkur ya karbi auren.
   Allah isanyawa aure albarka ameen.

Can nahango ango acikin dandazon bil adam sai washe hakora yake yana musabaha da mutane masu masa Allah sanya alkhairi yana amsawa, shi da babban amininsa mahbub wanda suka taso tare tin yarinta har girma kayansu iri d'aya farar shaddah mai manyan riguna maikyan gaske,dakaganta kasan taci kudi sosai kodan irin yanayin d'inkinda akamata kasan bak'arama bace.

Ya ramadan hargun mashkur yaje yabashi hanu yamasa Allah sanya alkhairi cikin sakin fuska sannan yawuce, sai bayanda yawuce ake fadamasa shine wanda yafara san bunayya kuma d'an kanen dadyn bunayya ne, nantake kishi yamotsawa mashkur saiya tab'e baki kawai.

Saikusan 1pm sannan sukabar jihar kebbi suka fice yola adamawa, acan d'inma canja kaya yai suka fice gunda zasu gudanarda tasu walima kan amarya taiso.
   ......................

A b'angaren amare kowa,tinda aka fad'a an daura aure bunayya take tana kuka tamak'ale gun momy tana kuka tin tanayi momy na rarrashinta cikin taisasan kalamai har tazo tasaka zuciyar momy tai rauni takasa hkr itama tafara kukan.

Dakyar aka samu suka hkr aka fice da bunayya gunda zaayi walima.

And'auki tsawon lkc ana gudanarda walimar inda wata shahararriyar malama ta gudanarda walimar, tayi nasihohi sosai akan zaman aure nasihohi masu ratsa jiki waenda suka k'ara narkarwar bunayya da jiki, bayan angama sannan aka d'akko amarya tareda k'awayenta izowa gida.

Bayan sun iso ne aka fara shirin tafiya yola kai amarya, aunty kuluwa ce tai tsaye wajen shirinta, saida tashirya tsab sannan suka sakata agaba sunamata hud'uba, momy aunty kuluwa yaya hauwa da aunty Rukayya da dai sauran yan uwan momy mata.

AURENTA ZANYIWhere stories live. Discover now