1&2

1.4K 78 5
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*D'AN BA K'ARA........*👹
            ( _gajeren labari ne_)
    
*Written By:-*
    _Ameera Adam_
                _AmeeraAdam60_
              *@Wattpad*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
   FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*

                  1&2

           " Mejidda mejidda wai kina Ina sai kwala Miki Kira nake kin shanyani daga d'aukan kallabi tuni kin shafe lokaci har na Fara gajiya, ko so kike mu rasa motar  kina sane dai yau juma'a ga Rana da d'aga " goggo larai ce ke tsaye da shirinta da alama fita zasuyi, mejidda ce ta karaso mayafinta ahannu tana kokarin d'aura D'an kwali, cikin mita da tsiwa take yiwa goggo larai magana, " haba goggo ke kincika raki duk kibi ki tayiwa mutane sanabe muje ni ko a soro na sa hijabin " rike haba goggo larai tayi cikin takaicin abinda mejidda tayi Mata tayi kwafa tace, " Allah ya shiryaki Y'ar Nan kinji Allah ya nunamun ranar da zanga auranki, mejidda kinsan dai banasan laifinki Amma ni meyasa bakya shayin fad'a mun magana ne? " Mejidda ko ta Kan goggo batabi ba ta cigaba da sabgar gabanta.

      Har sunje kofa suka ji me kifi na talla da sauri goggo ta tsaidashi, har ya kusa Shan kwana ya dawo guda uku aka zubawa goggo suka Fara ciniki da ita, sunyita ciniki ita da me kifi har suka karkare a dari hudu da hamsin, goggo har ta zuge kajarta ( _D'an aljihun da akewa tsofaffi ajikin sket dinsu na ciki_ ) ta ciro kud'i tuni me kifi ya yanka kifi Yana Shirin zubawa acikin leda aykuwa mejidda tai karaf tace, " goggo wannan mitsi-mitsin kifin Zaki siya dari hudu da hamsin wallahi ya daki hancinki wannan kifin da Bai wuce d'ari da hamsin ba, chabdi lallai ma kudin ne sukayi Miki yawa"

     Aykuwa da sauri me kifi ya kulleta Yana watsa Mata harara, goggo jin kalaman mejidda tuni ta hau ta zauna ya mutsa fuska gogg tayi sannan tace, " Kai yaro jeka da kifinka wallahi na fasa siya tunda mejidda tace yayi tsada idan munje rumfar D'an Tani ma saya inajin nashi sunfi wannan arha dama ajiyeshi zanyi sai yamma idan mun dawo, kila ma ragowar na jiya ne Kar naje ya buga kafin mu dawo, Dan yanda naga wannan jagulallen kifin Nan da alama kwantai ne" me kifi sakin Baki yayi Yana kallan goggo larai, tuni me jidda ta karb'e zancen, " kema goggo da wayace ki tsaidashi sai wani zubawa mutane ido yake kamar mujiya, ni irin dama masu tallan kifin Nan ban yarda da kifinsu ba, gaskiya mu wuce Kar muje arufe hanyar masallaci kinsan dai basa d'aga k'afa " goggo najin Haka ta yi gaba me jidda da mukulli ahannunta tasa Masa key ta rufe sukabar me kifi atsaye da yankakken kifi a hannu mejidda harda bangazar robar kifinsa da gefen hannunsa bisa tsautsayi kifin hannunsa rabi ya zube tayi gaba abinta ko ajikinta.

    Su Inna na zuwa titi suka tari bus din da zata kaisu Rimi asibiti, me jidda akan maleji ta zauna goggo na kujera sannan suka tafi, bayan wani lokaci motar dasu goggo suka hau ta cika makil har maleji, fad'a ne ya tirke tsakanin  me jidda da wata Yarinya ba kunya goggo ta shigar Mata, saboda ko kadan goggo batasan laifin ta Dan  mahaifi da mahaifiyar me jidda sun rasu shiyasa ta taso a hannun goggo asangarce ba kwab'a sai abinda tayi niyya shi take yi, kuma komai tayi goggo bazata Mata fad'a ko tsawatarwa ba, har suka K'arasa goggo nata masifa gidan babban D'an goggo sukaje, shi ma Kuma dama me jidda ce ta damu sai sunje saboda shima kawu haruna mutum ne bame fad'a ba akwai shi da sanyin hali shiyasa tasu tazo d'aya da me jidda.

        Su goggo basu suka dawo ba Sai yamma likis, goggo na bud'e kofa wasu y'an Mata suka k'araso da sauri gurinta kowa da karar Daya kawo Mata ta mejidda, tsuke fuska tayi ta zage su tass sannan ta koresu, haushin goggo ne ya kamasu suka tafi suna gunguni suna watsawa mejidda mugun kallo, sanin halin mejidda ba kanwar lasa bace shiyasa yasuyi gigin tab'a ta ba, Amma yanda suke Jin haushin mejidda yaci su nad'a mata dukan tsiya.

      Bayan sun shiga cikin gidan goggo tabarma ta shinfid'a tana maida numfashin gajiya, mejidda ma gefen Goggo ta kwanta ta d'ora kanta akan cinyar Goggo.
            Karni-karnin kifi Goggo ke ji Dan waige takeyi tana neman inda zataji yake karnin, bayan sun huta goggo tashi tayi zata d'ora Musu girki tana d'auko tukunya ta bud'e sai ganin yankakken kifi tayi aciki tana kallan kwayar idan d'aya ya kirfta Mata ido.

    *Coming soon*
             👉🏼1/November/2020

     _Ummou Aslam Bint Adam_😉

ƊAN BA ƘARA COMPLETEWhere stories live. Discover now