13&14

390 48 3
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*D'AN BA K'ARA........*👹
            ( _gajeren labari me ban dariya_)
    
*Written By:-*
    _Ameera Adam_
                _AmeeraAdam60_
              *@Wattpad*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
   FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*

                  13&14

        
         yanda Mai Unguwa yaga rana haka ya ƙarasa ganin darensa, kiran sallar asuba shi ya tashi su Mariya, suna farkawa suka hangi Goggo yashe daga ƙarƙashin gado suka hango ƙafafunta, dariya Uwani tayi tacewa Mariya, " yau naga ikon Allah dama ana samun tsofaffi masu birgima, kiga tsohuwar nan akan gado take amma saboda bacci yayi mata daɗi ji inda ta shige " Mariya da tsoro bai gama sakinta ba tace, " Uwani ba wannan ba kina gani jiya yanda aka tsoratamu dama yaya lafiyar kura " cikin halin ko inkula Uwani tace, " ke ina jin Aljanun da Mlm ya gama artabu dasu ne ko basu gama ficewa daga jikin Mejidda ba " zaro ido Mariya tayi tace, " Mlm dinne yayi artabun da Aljanu? " Uwani labari ta bawa Mariya aykuwa ta dinga ta'ajibi, tashin Goggo suka farayi shiru bata motsa ba kallan junansu suka yi tsoro ya fara kamasu, jijjiga Goggo sukayi amma ba motsi, duk maganganun da su Uwani sukeyi akunnen Mai Unguwa cikinsa ne ya karta tsoro ya ƙara kamashi musamman da yaji sunce goggo bata motsi.

      Ya jima abakin window yana san fita yayi alwala amma ganin garin da sauran duhu ya sa ya kasa fita, Uwani da mariya tashi sukayi kai tasaye ɗakin Mai Unguwa suka nufa cikin tashin hankali suka fara masa magana, ba tsammani Mai Unguwa ya ja da baya yana dafe ƙirji, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama sauraransu ya gyara tsayuwarsa a fakaice yana leƙen window sannan yace, " to ku wuce gaba muje muga me yake faruwa da  ita " hanya suka bashi alamun ya fara wucewa cikin tsawa yace musu, " Mu za'a sa agaba kuna biye damu kamar yaranku ? " sum sum sum suka wuce gaba, sai da Mai unguwa ya leƙo ya kalli gefe da gefe sannan ya taho da sauri har yana angije Mariya tsoronsa dan kar su shige su barshi a waje, bayan sun shiga ɗakin Goggo suka nuna masa daga cen nesa ya tsaya da ita yana cewa, " ku janyo ta mu gani mana " janyota sukayi ya kuma ce musu, " wai so kuke na taɓa macen da ba muharramata ba, ku yayyafa mata ruwa man " ba musu suka ɗebo ruwa lokacin tuni an idar da sallah gari ya fara haske, suna yayyafawa Goggo ruwa ta sauke ajiyar zuciya ganin haka yasa Mai unguwa yace, "mu fice mu bata guri idan ta gama farfaɗowa ma dawo"  ya faɗi hakan ne gudun kar wani abun ya ƙara shiga tsakaninsa da Goggo, suna ficewa kowa yayi alwala Mariya na shiga ɗakinta ta tashi Mejidda  aɗaɗɗare itama ta fito ta tafi tai alwala ta koma ɗakin.

          Uwani na zaune bayan ta idar da sallah taji Goggo na faɗin, " Alasan Alasan kuna ina Hamisu kaima kaxo, ku taho dan Allah kuxo ku kawon agaji wallahi Mai Unguwane zai kashe ni Mai Unguwa yana neman halaka ni, Mejidda ku dubamun ko ya halaka Mejidda, Alasan wasiyya ce nake bar muku ko mutuwa nayi banyafe masa izayar da yamun ba, ku miƙashi gurun hukuma duk wanda bai cika umarnina ba ban yafe masa ba. " Uwani ja da baya ta farayi da sauri ta tashi ta fice ɗakin Mai unguwa ta faɗa ta sanar dashi halin da Goggo take ciki, yana jin haka ya rufe Uwani da faɗa, " to ni me kike so nayi mata zafin ciwo ne kawai akanta idan kuka barta zata dawo hayyacinta " Uwani da haushin Mai unguwa ya kamata tace, " to Mlm ay kai kace kayi artabu aljanunsu yanxu ma ka tashi muje ko sune suka  dawo dan wallahi ni bazan koma ɗakin ba, sannan naji har wasiyya take bayarwa wai zaka kashe ta " Mejidda na daga ɗaki tanaji ana zancen Goggo zata mutu hankalinta yayi matuƙar tashi da sauri ta fito a ƙofar ɗakin  Mai Unguwa ta tsaya cikin tsiwa ta fara masa magana, " na rantse da girman Allah duk abinda ya samu Goggo kaine tunda lafiya kalau muka kwanta, wato kai ba ruwanka tunda ba tsohuwarka bace" Mai Unguwa na shirin magana sukaji Goggo tace, " Alasan ga mai Unguwa nan yaxo xai kashe ni wayyo Allah ku taimaka mun sai zaro harshe yake zai lashe ni, mai Unguwa dan Allah ka yafeni kayi hakuri "  gaban mai Unguwa ne ya yanke ya faɗi saboda abun na Goggo ƙara gaba yake shi atunaninsa zafin ciwo ne amma yaga kamar Goggo da gaske take, yana shirin yiwa Mejidda dabara ta juya ta koma ɗakin Mariya idanta har ya ciko da kwalla, kai tsaye wayar Mariya ta ɗauka number kawu Alasan tasa ta kira yana ɗauka tace, " kawu kira yanxu Mejidda ce " bayan kashewarta ba jimawa sai ga kiran kawu alasan tas ta zayyane masa duk abinda yake faruwa da musababbabin zuwansu gidan Mai Unguwa, agaggauce yace mata gashi nan zuwa kuma zai kira sauran ƴan uwansa su haɗu a gidan Mai unguwa, da haka sukayi sallama ta katse wayar tana juyowa taci karo da wani narkekeyar saniya abayanta, mai ɗauke da kan ƙaton kifi kwayar idonsa ɗaya ta ciro tana tsalle a tsakar ɗakin mariya girmanta tayi ƙafar jariri, sai kuma baki data buɗe mata ta hangi Mariya zaune aciki harshenta ya zazzago.

       Mai Unguwa na daga ɗakinsa suka jiyo ihun Maijidda azabure ya miƙe gaba ɗaya ma ya manta da Uwani da ke bakin ƙofa, janyo ƙofarsa yayi yabar Uwani da tsoro ya kamata tana ihu tana buga ƙofa tana kiransa,  Mai Unguwa na daga cikin ɗaki yace wa Uwani, " ki koma ɗakinki ni nan da kika ganni wallahi inmutuwa zakiyi bazan buɗe miki " Mariya da ta fito daga banɗaki ganin halin da Uwani take ciki yasa tsoro ya kamata, Mariya da tai wuri-wuri saboda tsoro tace wa Uwani, " wallahi nikam gidanmu zan tafi waɗannan mutanen sun kawo mana masifa har gida inmuka zauna zamuga zama" Uwani na shirin magana suka  hango rufin ɗakin Mariya ya ɗaga wani narkeken abu ya fito da kansa yana fesar da wani irin koren ruwa me yauƙi, atare suka bazama sukayi kofar gida suka fice kai tsaye maƙota suka faɗa, Mai unguwa da yake ɗaki banda ƙwala musu ƙira ba abinda yake yi, cikin tashin hankali yake faɗin, " Uwani, Mariya dan Allah ku dawo kar Aljanun nan su halaka ni "

       _Ummou Aslan Bint Adam_😉

ƊAN BA ƘARA COMPLETEOù les histoires vivent. Découvrez maintenant