*بسم الله الرحمن الرحيم*
*D'AN BA K'ARA........*👹
( _gajeren labari ne_)
*Written By:-*
_Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@Wattpad*☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*9&10
Me Unguwa na ganin haka ya hau tsalle-tsalle yana girgije-girgijen wando amma ga mamakinsa ba abinda ya ga ya faɗo sai gudawar da kebin wandonsa, tafiyar tsutsa yaji awajen gwiwoyinsa aykuwa da gudu ya bazama tsakar gida yana ihu, gaba ɗaya gidan bacci sukeyi banda Mejidda da take rabi bacci rabi ido biyu, tana jiyo ihun Me unguwa ta ƙara lafewa tana tura kanta cikin hijabi gabanta sai dukan uku-uku yake.
Cikin bacci Uwani ta ke jiyo ihun Me Unguwa sama-sama azabure ta tashi zaune, tashinta yayi dai-dai da tashin Goggo ita ɗinma azabure ta tashi cikin tsoro dan inbanda bacci ɓarawo ne da Goggo batayi bacci ba, cikin rawar murya Goggo tace, " Uwani me nake ji agidan nan badai makaran nan ne suka biyomu ba? " Uwani na shirin magana ihun Me Unguwa ya katse su da gudu Uwani ta fita har kallabinta na faɗuwa, Goggo cikin tashin hankali da firgici ta haye Gadon Uwani cen ƙuryar gado ta maƙale tana maida numfashi, tsoro ne ya ƙara kamata musamman da ɗakin yake baƙiƙƙirin ba fitila, idan ba numfashin Goggo kaji ba bazaka taɓa zatan akwai mutum me rai agurin ba.
Uwani Salati tasa tana tafa hannu cikin mamaki ta fara yiwa Me Unguwa magana, " Malam yau me nake gani wai me yake faruwa da kai cikin dare kake ihu haka, ke Mariya ! Mariya kina ina ki fito yau Malam ba lafiya tamu ta samemu " Uwani na ƙarasa maganar tana buga window Mariya, cikin magagin bacci Mariya tace, " haba Uwani wane Malam da gashi anan muna kwance " takaici ne ya rufe Uwani bata ƙara magana ba saboda tasan yanda Mariya take da maganin bacci, Me Unguwa ji yayi motsin gwiwarsa ya tsagaita gyara tsayuwarsa yayi yana tsuke fuska haɗe da gyaran murya sannan yace, " Uwani gayyar mutane ake mana " Cikin girmamawa Uwani tace, " Allah ya taimakeka abun ne ya bani mamaki naji kanata ihu tun ɗazu shi ne nake ganin kamar ba ƙalau ba " zaro idanu Me unguwa yayi ya hau muzurai yana neman hanyar da zai nemarwa kansa mafita gudun kar su Uwani su kawo masa wargi, jin yayi shiru Uwani ta buɗe baki zata kuma magana, cikin tsuke fuska ya dakatar da ita cikin muryar taƙama.
" Uwani mu akaji muna ihu, adubi kamar mu ace anji muna ihu kamar wasu ƙananan yara, Aljanun jiki yarinyar cen ne muka fara artabu dasu shi ne kike jin ihunsu, yanxu haka har so sukayi su taɓa dubi jiki na sun samun gudawa ajiki" Me Unguwa ya ƙarasa maganar yana nunawa Uwani wajen ƙafarsa, cikin zaro ido Uwani tace, " Mlm wai kana nufin aljanun da suke tsoratar da Mejidda kaine kukayi artabun dasu " gyaran murya Me Unguwa yayi ya ƙara tsuke fuska yace, " Uwani za'a gyara mana gurun kwanciyarmu ko surutu za'a zauna yi, kuma a ɗaukomun wani wandon da jallabiya zan sake waɗannan " ɗauke kai gefe Uwani tayi ƙasa-ƙasa tace, " bari na taso Mariya tunda ay yau ba girki na bane " Me Unguwa kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace, " ku biyu zakuyi aikin ke ki gyara ɗakina ita ta wanke waɗannan kayan " cikin jin haushi Uwani tace, " to bari na taso tan "
Me Unguwa na ganin Uwani ta yi gaba ya waiga gefe da gefe atsorace yabi bayanta gudun kar wani abu ya biyoshi, tana fitowa daga ɗakin Mariya taci karo dashi da mamaki tace, " Mlm lafiya wai naganka duk a firgice karfa kaje mutanen nan su fara taɓaka fa " karkaɗa rigarsa ya hauyi yana ɗaga kafaɗa haɗe ta muzurai suna haɗa ido da Uwani ya watsa mata mugun kallo ba shiri taja bakinta tayi gum, Mariya ce ta fito daga ɗaki tana soshe-soshe sannan Me unguwa yace ta ɗebo masa ruwa a bokiti zai gyara jikinsa, ba musu ta wuce ta ɗebo ta kawo masa ita kuma Uwani ta wuce turakarsa tana gyarawa, duk waɗannan maganganun da ake yi tsakin Me Unguwa da matansa kaf akan kunne Mejidda da Goggo suke sauka wani sabon tsoron ne ya ƙara ɗarsuwa azuciyarsu.
Bayan me unguwa ya gama gyara jikinsa har ya canja kaya yana daga bakin ƙofar ɗakin Uwani yana hangen Mariya na wanki idanunsa ne suka kai kan ɗakinsa da Uwani ke gyarawa, wasu tafka-tafkan kifi ya gani guda biyu kwance a bakin ƙofa, na farkon fuskarsa irinta Goggo ce na biyun kuma fuskar Mejidda gareshi, kowannen su sai wangale baki yake da ƴan haƙora biyu, ƴan aljanun nan ya gani irin wanda ya hau masa kafaɗa, gani yayi sun zama guda goma suna rawa da juyi idan sukayi rawa sai su faɗa bakin me irin fuskar Goggo da Mejidda atake suke taune su suna furzo da tuƙarsu zaiga sun girgije sun haɗe sun koma yanda suke sai su kalli Me Unguwa, ɗaya ne yayi tsalle ya tunkaro inda Me Unguwa yake, da gudun gaske Me Unguwa ya arce cikin ɗakin Uwani cen ƙarshen gado ya haye ya kwanta yana maida numfashi, Goggo dake kwance jin Me Unguwa ajikinta yasa ta rafka salati tana faɗin,
" Oh ni yau na shigesu na naga ta kaina me nake ji nake gani yau a idanuna, Me Unguwa me ya kawoka gurin tsohuwar Allah ta'ala " Goggo ta faɗa tana ƙokarin tashi daga gurin, shi kuwa Me Unguwa a idonsa gani yayi Mariya ce agefensa saboda tashin hankali ma ya manta da ya barota a tsakar gida tana wanki, cikin firgici Me Unguwa ya janyo Goggo duk atunaninsa Mariya ce yana faɗin, " Mariya dan Allah ki taimaka ki ɓoye ni taune mutane suke na tabbata nima zasu iya taunemun kai " ita kuwa Goggo ba haka taji a kunnenta ba ji tai Me unguwa na kawo mata maganganun banza, tsoro ne haɗe da mamakin Me unguwa ya kamata cikin jin haushinsa ta fisge hannunta tana Faɗin, " Amma wallahi kaidai Sale kayi asarar hali ja'iri ka rasa wacce zakayiwa iya shegen sai ni tsohuwar Allah da fata tayi yaushi, munafiki idan ka zauna a fadarka kayita baza riga kana zare ido ya mazarin tsire ashe a ɓoye mugun abun da kake ƙullawa kenan har ɗakin matarka, Allah wadaranka da kake tafe da sigar mutanen kirki " ta ƙarasa maganar tana angije Me Unguwa ƙasa.
Goggo na niyyar tashi taga Me Unguwa yayi wata girgiza ya koma wata hallitar me suffar raƙumi, sai dai wani abun tsoro kafuwanta na baya babu su sai jelar kifi harshenta ne yake ta fitowa har sai da ya ƙarasa gurun da Goggo take cak hashen nan ya ɗaga Goggo ya saƙaleta jikin ƙarfen gado da yake gadon irin na ƙarfen nan ne me rumfa, Goggo ta buɗe bakinta dan tayi ihu taji ta ka sa wannan hallitar ce ta dinga sa harshenta tana kaɗa kafafun Goggo kamar ana kaɗa reshen bishiya, Goggo saboda gajiya haka ta dinga hawaye ga tsoratata da hallitar nan take yi, gaba ɗaya Goggo ta jiƙe ɗakin Uwani da fitsari tun tanayin na hankali har ya wuce musali.
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
STAI LEGGENDO
ƊAN BA ƘARA COMPLETE
HorrorSalati goggo ta rafka tana ja da baya cikin tsoro take Fad'in, " me nake gani ni hansatu kamar danyen kifi ke mejidda zo ki tayani gani " mejidda atunaninta rikicin Goggo ne tana daga zaune ta cewa Goggo, " tunda kifin Kika gani ay shi d'in ne, kema...