*بسم الله الرحمن الرحيم*
*D'AN BA K'ARA........*👹
( _gajeren labari ne_)
*Written By:-*
_Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@Wattpad*☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*25&26
Haruna dariya ya ƙarayi yace, " hege master anji wuya dole ayi biyyaya" Baba Alasan duk abinda yake faruwa yana kallo girgixa kai yayi cikin zuciyarsa yake yiwa Mai unguwa dariya, ganin Haruna na niyyar dila shi ya bashi wuya yasa yace, " kai Haruna banasan sakarci bani wuƙar nan " cikin ƙunƙuni Haruna ya zaro wuƙar ya miƙawa Baba haruna yana faɗin, " wallahi kana kawo mun eh yane kawai sai ina tsaka da fa da ta sai kace mun eh yaneh haba...... " katseshi Baba Alasan yayi da, " kai banasan sakarci bani nan " ya ƙarasa maganar yana karɓe wayar hannun Haruna.
Mai unguwa yana ganin Baba Alasan ya karɓe wuƙar Haruna ya watsa masa harara cikin nuna isa yace, " Ɗan iskan banza da wofi ashe kana da wanda kake jin tsoro kace da kai shege ne " afusace Haruna ya kaiwa Mai unguwa naushi a gefen kunci sannan yace, " Kai zan sama ka fa innuna maka ni babban Gwaska ne, kaci darajar ina gaban babban yaya da sai ka gane kurenka kasan ko agidan giya akwai babba " tsawa Baba Alasan ya ƙara bugawa Haruna ba shiri yayi shiru yana ɗauke kai gefe, tunda akayiwa Mai unguwa mahangurɓa ya riƙe bakin ya sunkuyar da kai bai ƙara dagowa ba, su Ado ne suka dafa shi suka shiga jero masa sannu, banda gyada kai ba abinda Mai unguwa yake yi, bayan wani lokacin ne Ya ɗago da kai suna haɗa ido da Baba lawan yace, " Allah ya ƙara Haruna yamun dai-dai " ya ƙarasa maganar yana yiwa Mai unguwa dariyar ƙeta.
Baba lawan na gefe ji yayi zuciyarsa fes da abinda Haruna yayiwa mai unguwa har afili farincikin sa yaƙi boyiwa, Baba Alasan zama yayi ya ɗago Goggo da take sharɓe, akan cinyarsa ya ɗora kan Goggo ya fara karatu yana ba ƙaƙƙautawa, ya jima yana karatu sai ji yayi jikin Goggo ya fara karkarwa kamar mai jin sanyi yana ganin haka ya cigaba yi da ƙarfinsa basuyi aune ba sukaji Goggo ta taƙarƙare ta kwarma ihu tana zabura, riketa yayi gam bai fasa karatun ba wuyar da yaji ne ya fara magana, " dakata ka dakata zan fita dama ni bani sukayiwa laifi ba, nima gayyatoni yayi nine babban Abokinsa shiyasa na shiga jikinta amma zan fita yanxun nan " Baba Alasan najin haka yace, " maza kayi ka fice ko inƙoneka " hankali atashe yace, " yanxu zan fice" yana rufe baki sai ji sukayi Goggo na hamma wani irin gumi ne ya fara ƙetowa Goggo bayan ta dawo hayyacinta kallansu ta fara yi ɗaya bayan ɗaya ji tayi gaba ɗaya jikinta yayi mata nauyi babu daɗi sosai, ahankali ta kalli Baba Alasan tace, " Alasan kune gaba ɗayan ku haka " cikin farin ciki Baba Alasan yace, " eh mune Goggo sannu kinji " bata amsa ba idanunta ya kai kan Haruna da ke gefe tace, " ɗan haru na zo mana harunena " ba kunya Haruna ya taso yaxo gurin Goggo yana jingina da ita cikin sigar shagwaɓa, Maijidda ce ta farka jikinta na tsami ta tashi ta zauna tana kallan mutanen gurun ɗai-ɗai, Baba lawan ne ya kalleta yace, " ja'ira mai siffar ifuritai kin wani tsatstsaremu da idanu duk iftila'in da kuka shiga ba kece sila ba " cikin jin haushi Goggo ta tsuke fuska tace, " Kai Lawan ka fita sabgar marainiyar yarinyar nan dama na lura duk cikinku Alasan ne yake santa sai kuma haruna shima naga baya nuna mata ƙiyayya " ta ƙarasa maganar tana watsa masa mugun kallo.
Mai unguwa da har lokacin haushin haruna da Baba Lawan yake ji azabure ya ɗago, fuskarsa har ta fara kumburewa daga gefen bakinsa cikin sarƙewar murya yace, " Lawan ɗin da harunan ma ay ƴan bura uba ne" yana rufe bakinsa ya tattakura ya kaiwa Baba Lawan dundu abaya kafin kace kwabo ya zura aguje ya faɗa ɗakinsa ya danno kofar.
_*WANNAN SHAFIN NAKU NE ƳAN ƘUNGIYATA TA FIRST CLASS WRITERS KU DAƊE KUNA ƘARKO MUTANE NA INA YINKU IRIN SOSAI ƊIN NAN.*_
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
ESTÁS LEYENDO
ƊAN BA ƘARA COMPLETE
TerrorSalati goggo ta rafka tana ja da baya cikin tsoro take Fad'in, " me nake gani ni hansatu kamar danyen kifi ke mejidda zo ki tayani gani " mejidda atunaninta rikicin Goggo ne tana daga zaune ta cewa Goggo, " tunda kifin Kika gani ay shi d'in ne, kema...