*بسم الله الرحمن الرحيم*
*D'AN BA K'ARA........*👹
( _gajeren labari ne_)
*Written By:-*
_Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@Wattpad*☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*7&8
Wulgawar wani abu ya gani daga banɗakin ya faɗa cikin kitchen ɗin, ta window yaga ana turo jela ana karkaɗata alamar jelar kifi ce, ƙurawa gurin ido yayi yana kallo sai kuma yaga babu komai jelar kifin ta ɓace, me unguwa cikinsa ne ya karta tsoro ya fara kamashi,cikin rashin sani Mudi ya katse me Unguwa da, " Ranka shi daɗe " aykuwa azabure ya waigo gurinsa yana muzurai, gudun kar su Ado su fahimci halin da yake ciki yasa me Unguwa mazewa ya dake yana muzurai shi adole bayasan raini.
Mudi ne yace, " Allah ya taimakeka ya Ƙara yawancin kwana, wane hukuncin kuka yanke yanxu? " Me Unguwa Ƙara Baza babbar rigarsa yayi yana kallan gefe da gefe sannan yace, " Mun yanke hukuncin Amaida ita Goggo larai da jikarta gida...... " Tun me Unguwa bai dire maganar ba Mejidda tayi tsalle ta dire ta katse shi da, " Ni wallahi bazan koma ba Goggo cinyeni zatayi kanta ya koma na tarwaɗa ni ku maidani gidan kawu Alasan " ta Ƙarasa maganar tana Ƙara Ƙwakwume mudi cikin jin tsoron ganin fuskar Goggo, Mudi baya yaja yana shirin janye Mejidda amma ina Ƙara riƙeshi take tsam.
Goggo haushi tuni ya cikata tana ganin lamarin na Mejidda kamar harda iskancinta, Azuciye tayo kan Mejidda zata daketa aykuwa tana ganin haka Mejidda tayi bayan kujerar me Unguwa da gudun gaske, Goggo faɗa ta farayi cikin huci da ɓacin rai, " Mejidda yau ni zakiyiwa iya shege dan ubanki mayya kika maidani da zan cinye ki zamu gauraya dake ne, ƴar banza ni ce na koma tarwaɗa ko ni idan na kamaki sai na maidaki sukumbiya " Ado ne ya kalli me Unguwa yan gimtse dariyarsa yace, " Allah ƙara girman masarauta ina ganin wannan lamarin kamata yayi asanya su mudi aciki ko malan liman domin kowa yasan irin ƙaunar dake tsakanin Goggo larai da Mejidda ni ina ganin aduba lamarin sai....... " azafafe me Unguwa ya katseshi, " Ado me aka maidamu wato lamarin ya gagaremu harsai wannan ya shiga ciki? ko kuma mlm liman lallai yawan zamanmu daku yasa anfara kawo mana wargi, wai ba taƙamarka ko Aljanu bane suke razanasu? To ba wasu Aljanu da zanji shakka ko shayinsu nina fi san ms su fito muyi artabun kwanji dasu daga nan zasu gane banbancinmu dasu su gane gadon masarautar me Unguwa ba wasa bace gado sai ɗan gado " kallan goggo yayi ya cigaba da cewa, " Goggo tashi ki tafi ita kuma Mejidda sai munyi maganin abinda yake kanta tukunna "
Zaro idanu goggo tayi cikin tashin hankali tace, " Wallahi wannan gidan na barshi ko a lahira bana fatan kuma ganin me kama dashi ma, da idanu na naga kifi namun dariya sannan ace na koma ciki da tsohon daren nan...." cikin tsuke fuska haɗeda muzurai Me Unguwa yace, " Gyara dai adinga iya magana agabanmu, yakamata asan agaban waɗanda ake kai mudi kunaji babu me magana ne " mudi ne ya kalli Goggo cikin sauri yace, " Goggo ana gaban me Unguwa adinga gyara magana ba komai za'a dinga furtawa ba, atashi atafi gida wannan umarnin ranka shi daɗe ne "
Ɗauke kai Goggo tayi gefe kamar ba da ita ake ba, mudi ne ya ƙara magana amma Goggo tayi biris dashi, ganin haka yasa me unguwa yace a ƙale Goggo itama ta kwana zuwa safiya sai yayi musu magani, cen gefe Mejidda ta koma ta rakuɓe tana satar kallon Goggo, itama Goggo daga gurun da take tana wurgawa Mejidda harara suna haɗa ido sai mejidda ta ɗauke kai dukda taga fuskar Goggo ta dawo dai-dai yanda take, Bayan sallar Isha'i Me unguwa ne yasa aka kawowa Goggo Abinci sannan aka miƙawa Mejidda nata.
Lokacin kwanciya Goggo a ɗakin Uwargidan Me unguwa akayi mata shimfiɗa, ita kuma Mejidda a ɗakin amaryar akayi mata, duk da haka Mejidda a tsorace take bata saki jikinta ba gani take kamar wani abun zai kamata.
Cikin dare Me Unguwa na ɗakinsa kimanin ƙarfe ɗaya zuwa ɗaya da rabi na dare yana kwance har yayi bacci da alama dai baccin nasa baiyi ƙarfi ba, motsi yaji daga bakin ƙofa yana buɗe ido inuwar mutum ya hango daga ƙofar ɗakinsa anleko an koma, zaiyi magana ya hango ankuma tahowa an tsaya abakin ƙofar ana lekowa, cikin alamun me bacci yace, " ke mariya leken me kikeyi haka kamar munafuka " da yake mariya itace da girki ranar, shiru yaji ba magana daga nan sai yaga anjuya antafi.
Me Unguwa na kwance bacci har ya sake ɗaukansa yaji alamar mutum yaje ta bayansa ya kwanta, duk yayi zaton mariya ce cikin magagin bacci yace, " kin fiya nunkufurci wallahi da kike kaiwa da dawowa leƙen me kike mun? ni nan bacci nake ji kya gama kwanciyarki ki ƙara gaba?" ya ƙarasa maganar yana ɗora hannu ajikin ta duk atinaninsa jikin mariya ne, wani irin gashi yaji ahannunsa me ƙayoyi har yana sukarsa ga wani gurnani da yaji lokaci ɗaya, da sauri Me unguwa ya ɗauke hannunsa yana miƙewa tsaye cikin tashin hanksli jikinsa na karkarwa, wani tafkeken abu ya gani nannaɗe yana ta kanannaɗewa tsawon abun har waje bai gama ganin karshesa ba kuma abun shigowa yake tayi, Me unguwa jikinsa ne ya ɗauki rawa ya ƙara maƙalewa ajikin bango, yana nan yana ganin ikon Allah har abun ya gama shigowa ya cure guri guda sannan yayi wata irin walkiya da ta haske idon Me unguwa, wata mummunar hallita ya gani sai zaro harshe takeyi daga ƙarshenta kuma jelar kifi gareta , gumi ne ya rufe Me unguwa yanajin cikinsa na ƙara karta masa, gani yayi abun yayi tsalle ya bugi saman ɗakinsa har sai da rufin ɗakin ya buɗe ta yanda har yana hango sararin samaniya, sai kuma yaga abun ya faɗo ƙasa tiimmmm atake ya ɓace da sauri ya hau waige-waige cikin tsoro da fargaba.Ajiyar zuciya Me unguwa ya sauke yana maida numfashi ji yayi abu ya dira a kafaɗarsa, shafa gurun da zaiyi yaji wani ɗan gajeren mutum Me unguwa na kallan gurun ɗan Aljanin ya kece da wata irin dariya yanayi yana tsalle akan kafaɗar me unguwa, bakin sa yafi ko ina girma ajikinsa da wasu haƙora guda biyu, bakinsa sak irin na kifi yana wage shi ƴan haƙoran zasu fara tsalle, gudawa ce ta fara biyo wandan Me unguwa jikinsa rawa yake kamar mazari, ɗan Aljani yayi tsalle ya dire ƙasa sannan yabi ta ƙafar Me unguwa ya shige wandonsa.
_Yawan comments shi zai sa ku samu posting kullin_🤷🏻♀️
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
ŞİMDİ OKUDUĞUN
ƊAN BA ƘARA COMPLETE
KorkuSalati goggo ta rafka tana ja da baya cikin tsoro take Fad'in, " me nake gani ni hansatu kamar danyen kifi ke mejidda zo ki tayani gani " mejidda atunaninta rikicin Goggo ne tana daga zaune ta cewa Goggo, " tunda kifin Kika gani ay shi d'in ne, kema...