*بسم الله الرحمن الرحيم*
*D'AN BA K'ARA........*👹
( _gajeren labari ne_)
*Written By:-*
_Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@Wattpad*☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*29&30
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚Baba Alasan ne ya kalli Mai unguwa yace, " Mai unguwa ina buƙatar muyi magana da kai zamu iya ƙeɓewa gefe " Mai unguwa ƙara baza babbar rigarsa yayi yace, " za'a iya faɗa anan, mune zamu taso mu biku dan muji daga gareku " girgiza kai Baba Alasan yayi yace, " to shikenan hakan ma yayi, dama shawara ce zan baka amatsayinka na shugaba mai jagorantar al'umma, shi shugabanci da kake gani Mai unguwa ba yana nufin ka sarrafa jama'ar ka bane yanda kake so, kuma girma basai mutum na waɗansu irin abubuwa ba sannan mutane zasu dinga girmama shi ba, basai mun nuna san girmanmu afili ba sannan za'a girmama mu ba, Alfahari da nuna jiji da kai basu ne halin ƙwarai na shugaba nagari ba, Allah yasa mu dace Aameen " Baba Alasan na rufe baki gaba ɗaya suka amsa da Amin wallahi maganar ka gaskiya ne yanxu anyi yunwa halin kowa ya fito ba wani buɗe ido da za'a kuma yi mana " jikin Mai unguwa sanyi yayi bai ce komai ba yabi su da kallo.
Baba Alasan ya kalli Goggo yace, " Goggo zamu iya tafi yanxu? " gyaɗa masa kai tayi ba musu suka miƙe tsaye harda su Haruna, su Ado ne suka farayin gaba suka wuce sannan su Baba Alasan suka bi bayansu, Haruna har yayi hanyar fita ya dawo gurin Mai unguwa yace masa, " Master ayafi juna fa dan bansani ba ko nayi maka eh yaneh kasan zuciya bata ƙashi " Mai unguwa hannu ya miƙawa Haruna yace, " haba mutumina ay na yafe maka kuma ni ba abinda kamun sai dai fa ya kamata adaina wannan eh yaneh ɗin, nima kaga na ajiye izzar sarauta agefe " dariya Haruna yayi yace, " shege master karka damu andaɗe ma ba'a haɗu ba kasan idan aka saba faɗar eh yaneh ɗin nan sai a slow kawai, kai na ware fa " Haruna na kaiwa nan ya sa kai ya fice, duk sun fice daga Mai unguwa sai su Mariya.
Su Baba alasan ne bakin ƙofar gidan Goggo duk yanda sukayi da Goggo da Maijidda su shiga ciki dan su haɗa kayansu ƙi sukayi saboda tsoro, sai Baba lawan ne ya ɗebo musu kayansu na sawa aka janyo kofar gidan aka saka key, Baba Alasan ne yace su wuce washegari zaizo da mota ya kwashe sauran kayan Goggo, hakan kuwa sukayi gaba ɗaya suka tarkata suka wuce gidan Baba alasan.
Duk yanda Mai unguwa yaso ya dakatar da Uwani akan tafiya abu ya gagara har sai da ya kira mahaifinta ya zayyane masa halin da ake ciki sannan yayi mata faɗa ta haƙura ta zauna.
Bayan kwana biyu Maijidda ta samu sauyin rayuwa ƙwarai da gaske musamman da take gaban Baba alasan kuma mai ɗakinsa macece tsayayyiya akan yaranta shiyasa ta haɗa da Maijida sam bata banbanci, duk abinda za'ayiwa Maijidda bazaka taɓa jin Goggo ta yi magana ko nuna ɓacin ranta ba.
Mai unguwa duk wata izza da fuffuƙa haɗi da cika baki duk yanxu babu su zaune yake da mutanen unguwarsa lami lafiya ba nuna wariya ko bambamci tsakaninsa dasu, hakan ne yasa suka ƙara bashi girmansa dai-dai misali ba tare da wani raini ya shiga tsakaninsu ba, haka nan a ɓangaren iyalinsa hatta tsuke fuskar da yake musu ya kauda ta shiyasa suka ƙarajin daɗin zama dashi fiye da cen baya.
_TAMMAT BIHAMDULILLAH_😁
*FAƊAKARWAR DAKE CIKI ALLAH KA BAMU IKON ƊAUKA, KUSKUREN CIKI UBANGIJI KA YAFE MANA.*👏🏼👏🏼👏🏼
_MU HAƊE CIKIN SABON LITTAFI_👇🏻
👽 *MARWAN*👽
_BY_
_*AMEERA ADAM*_
_@WATTPAD_
_*Ameeraadam60*_☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️
https://chat.whatsapp.com/JgZ9nIId3CxB67nFSbrz5F
_*DEDUCATED TO MY LVLY SISTERS:-*_*ZAINAB ADAM*
*SA'ADAH ADAM*
*AFNAN ADAM*
*HIND ADAM*
*ELAF ADAM*1&2
" Maryam mai kike yi ne wai tun ɗazu nace miki kije ki kwashe mun tuwo amma kina ɗaki banga wucewarki ba, idan bazaki kwashe ba inje inkwashe abina da kaina " Umma ta ƙarasa maganar tana sauraren abinda Maryam zata faɗa, da sauri Maryam ta ajiye wayar hannunta tace, " wallahi Umma kinga nazo tashi kenan kayan drower ta suka zubo shi ne na tsaya nake gyarawa " ta ƙarasa maganar tana rufe murfin drower kamar wacce ta gama gyara kayan nata da gaske, Umma ce ta cigaba da mita tana faɗin, " ay na ɗauka wayar ce ahannunki kike dannawa dan inkika rike waya kamar mai ibada " fitowa tayi ta wuce cikin kitchen ɗinsu alokacin tuni anfara kiran sallar magriba, kwashe tuwon tayi sannan taje tayi alwala ta gabatar da sallah.
Gaba ɗaya suna zaune Maryam da ƙannenta uku, biyu maza ɗaya mace sai mahaifiyarsu Umma suna hira bayan sallah isha'i yaro ne yayi sallama ya shigo cikin gidan bayan sun amsa yace, " wai ana sallama da Maryam inji Marwan " Umma ce tace, " kaje kace tana zuwa " kasancewar dama sun san da zuwansa duk ranar alhamis da juma'a yake zuwa hira, fitar yaron babu jimawa Maryam ta ɗauki mayafinta ta fita, kamar kullin yana zaune akan lifan ɗinsa da murmushi ta ƙarasa gurinsa suka gaisa, kamar yanda ya saba zolayarta cikin barkwancinsa yace, " ina nawa tuwon da kika ci baki rage mun ba " bata yi wani mamaki ba saboda dama ta saba da jin abubuwan almara daga bakinsa cikin hali ko inkula tace, " yana cikina ay idan naci kamar kaci ne " murmushi yayi yace, " haka ne my Queen, rufe idanki zan miki wani suprise. "
Ba musu Maryam ta rufe idanta tana murmushi, hannunsa ya ɗora adai-dai kanta wani haske ne ya fito daga hannunsa lokaci ɗaya suka ɓace daga gurun tafiya sukayi mai nisan gaske basu sauka a ko'ina ba sai awata babbar da'ira ta alƙarya, mai ɗauke da waɗansu irin hallitu marasa fasali abun tsoro ne ga duk wani bil'adama, da alama babbar masarauta ce ta aljanu wacce ta ƙunshi hallitun aljanu na duniyoyi daban-daban, duk abinda yake faruwa Maryam bata sani ba.
kallanta Marwan yayi cikin murmushi yace, " buɗe idanki My Queen " Buɗe idanunta Maryam tayi ga mamakin ta ta fara kallan tsakiyar fadar da suke ganin munanan halittun gurin yasa ta cikin ruɗewa da tashin hankali ta rungume Marwan tana runtse idanunta haɗe da kwallah ƙara mai karfin gaske, Marwan ya manta sam ganin haka ne yasa ya kalle su cikin jin haushi ya buga musu tsawa cikin wani irin yare, " kaskuwase kasmelasi kaskuwase papupasku hagabarsi mundadusi " ( Kun fara bijirewa umarnina ne bance muku bil adam zan aura ba ku rikiɗa yanxun nan ) jikinsu na rawa suka amsa masa da, " faaaaaakusakun malasin yatma " ( tuba muke Yarima mai jiran gado ) kafin ƙiftawa da bismillah lokaci ɗaya suka riƙiɗa zuwa bil adama hatta da alƙaryar gurun sun sauyata zuwa ta mutane.
kallan ta yayi yace, " haba my Queen mai yasa kin fiya tsoro ne kawo ki fa nayi ki gaida su mommy buɗe idanki ki gani " a tsorace Maryam ta buɗe idanta wani irin kyakykyawan guri ta gani da alama gidan masarauta ne wasu kyawawan ƴan mata ne suka ƙaraso gurinta suna faɗin, " barkanki da zuwa gimbiya muna miki fatan alheri " da idanu Maryam ta bisu tana kallo bata amsa musu sai Marwan da ya gyaɗa musu kai, wuce wa sukayi haka aka dinga zuwa gaida Maryam tun tana jin tsoro har ta fara sakin jikinta, Marwan ne yace mata, " mu ƙarasa ki gaida su Mai martaba " ba musu tabi bayansa suka ƙarasa wani babban falo ma ɗauke da ƙayatattun kujeru an ƙawata falon da zallar kayan sarauta, wasu ƙyawawan dattijai ta hango mace da namiji suna zaune cikin kamala sanye suke da alkyabba masu kyawun gaske, har ƙasa ta tsugunna ta gaida su sannan suka taso suka fice daga falon, suna fitowa Maryam ta fashe da kuka tana cewa Marwan, " ina ne nan kawo ni Marwan ko ka fara satar mutane ne bansani ba " kallanta yayi yana murmushi ya shammace ta yana hura mata iska afuska " lokaci ɗaya jikin Maryam ya saki Marwan dunƙule hannunsa yayi ya wulwula shi yana buɗewa wani irin haske ya mamaye ɗakin gaba ɗaya, atake suka ɓace daga gurin.
Bayan sallar Asuba Umma ce ta ƙara shiga ɗakin Maryam take mata magana, " wai Maryam kamar mai baccin mutuwa tun ɗaxu nake tashin ki kinƙi ki fito kiyo sallah " tashi zaune Maryam tayi tana cewa Umma, " Na fa tashi Umma " gaba Umma tayi bata ƙara mata magana ba, kallan ɗakin da take ta ƙarayi tana mamakin ganinta aɗakinta.
*coming soon*👇🏻
_15/11/2020__Idan naga ruwan comments na cigaba da typing._
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
ŞİMDİ OKUDUĞUN
ƊAN BA ƘARA COMPLETE
KorkuSalati goggo ta rafka tana ja da baya cikin tsoro take Fad'in, " me nake gani ni hansatu kamar danyen kifi ke mejidda zo ki tayani gani " mejidda atunaninta rikicin Goggo ne tana daga zaune ta cewa Goggo, " tunda kifin Kika gani ay shi d'in ne, kema...