*بسم الله الرحمن الرحيم*
*D'AN BA K'ARA........*👹
( _gajeren labari ne_)
*Written By:-*
_Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@Wattpad*☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*3&4
Salati goggo ta rafka tana ja da baya cikin tsoro take Fad'in, " me nake gani ni hansatu kamar danyen kifi ke mejidda zo ki tayani gani " mejidda atunaninta rikicin Goggo ne tana daga zaune ta cewa Goggo, " tunda kifin Kika gani ay shi d'in ne, kema Goggo Banda abinki kifin k'afa garshi da zai shigo cikin gida bama nan, idan nace kinfiye rigima kice zan gaya miki magana " ganin kifin na yi Mata murmushi yasa Goggo ta K'ara rafka wani salatin tana sakin tunkunyar tana yowa gaba, mejidda dariya takewa Goggo harda rik'e ciki tace, " Goggo wai me yake faruwa ne Dan Allah ko kunyar gudu bakiji ba? gudu kikeyi amma kamar me rawar Etigee" Goggo Bata bi ta Kan mejidda ba ta rabe ajikin katanga tana leken tunkunyar data jefar ,wani Kan kifi ta hango suna had'a ido ya K'ara kashe Mata ido daya😉 sannan ya washe Mata baki😃, daskarewa Goggo tayi cikin tashin hankali ta mik'a hannu tana nunawa Mejidda kifin, da saurinta Mejidda ta K'arasa gurin ba shiri ta dakata musamman yanda taga Kan kifin Yana wangale Mata baki, k'ank'ame Goggo tayi tana ihu cikin tashin hankali Take Fad'in, " wayyo Goggo Kan kifi Yana wangalen Baki zai cinyeni, ki taimake ni Goggo na yi gamo da Aljanin kifi ".
Ita kanta Goggo abun tsoro yake Bata Amma sai ta D'an dake ta K'ara lek'awa Amma ga mamakinta sai taga tukunyar wayam, ko irin alamun jinin kifin babu.
Goggo ta Jima tana kallan tukunyar Amma ko d'ishin kifi Bata gani ba, zame mejidda take Shirin yi daga jikinta caraf ta Kara k'ank'ame Goggo kamar za'a k'wace Mata ita, itama goggo Bata gama sake wa ba suna cikin Haka ba zato wani almajiri ya rafka ba ra, " Waaahiiideeeeeee " Me jidda ce ta Fad'a aguje cikin d'aki tabar goggo jikinta sai rawa yake ta Mara Mata baya, kafarta D'aya d'ingisa ta takeyi Amma alokacin Nan tuni ta take ta bata sani ba, Almajirin shi dariya ma abin ya bashi yi yake yana k'yak'yatawa, goggo dake d'aki ta cika fam Dan Jin yanda Almajiri ke b'ab'b'aka dariya, lek'awa tayi Dan tayi Masa magana tana kallan fuskar almajiri sai gani tayi kansa ya koma rafkeken kifi da y'an hak'ora biyu Yana wangale Musu Baki, mejidda dama tuni ta haye gadon goggo ta kudundune kanta.
Hankalin goggo K'ara tashi yayi ganin hokoran kifin na cirewa Yana komawa bakin kifin da kansa, da sauri ta mak'ale gefen mejidda tana sauke ajiyar zuciya k'irjin ta sai dukan uku-uku yake, shi kuwa almajiri Yana ganin goggo ta matsa daga kofa ya kama gabansa Yana tafe idan ya tuno gudun su Goggo sai ya fashe da dariya Abunsa.
Jin shiru ba alamar almajiri yasa Goggo lek'awa ganin bayanan cikin sand'a ta Fara rad'awa mejidda magana k'asa-k'asa tace, " taso mu fice daga gidan Nan mejidda, wallahi da alama aljanu ne agidan Nan " mejidda najin Haka ta zabura ta d'ago kai zatayiwa Goggo magana taga Kan goggo ya koma Mata na katon kifi irin manyan tarwad'ar Nan ya wangale Baki yana Shirin had'iye ta, mejidda mutuwar zaune tayi tana ja da baya, ganin irin kallon da mejidda ke Mata yasa Goggo ta Fara Shan jinin jikinta D'an waigawa tayi atunaninta ko wani abun mejidda ta gano yasa take Haka, ganin babu komai yasa Goggo ta Fara magana sannanye tace, " mejidda ko wani abun Kika gani " Mejidda a idonta kuwa gani tayi Kan kifin jikin goggo ya wage Mata hakoransa yana kad'a harshe sannan ya yunkuro zai Kai bakinsa kanta, da gudun gaske mejidda ta fice daga gidan tana ihu tana Fad'in, " wayyo Allah ku taimaka mun Goggo ta koma kifi zata cinye ni.
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
YOU ARE READING
ƊAN BA ƘARA COMPLETE
HorrorSalati goggo ta rafka tana ja da baya cikin tsoro take Fad'in, " me nake gani ni hansatu kamar danyen kifi ke mejidda zo ki tayani gani " mejidda atunaninta rikicin Goggo ne tana daga zaune ta cewa Goggo, " tunda kifin Kika gani ay shi d'in ne, kema...