27&28

327 34 0
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*D'AN BA K'ARA........*👹
            ( _gajeren labari ne_)
    
*Written By:-*
    _Ameera Adam_
                _AmeeraAdam60_
              *@Wattpad*

☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
   FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*

                   27&28

      Gaba ɗaya gurin babu wanda Mai unguwa bai bawa dariya ba, sosai su Ado suke dariya harda riƙe ciki shi kansa Baba Alasan ba ƙaramar dariya yayi ba, Magaji ne ya kalli su Ado yace, " Mai unguwa fa da alama farar kura ne ji yanda ya take ƙafarsa ya xuba aguje yana tsoron kar akamashi arama dukan da yayi, kunsan fa ya sha ƙasa bai manta ba " yana kaiwa ƙarashe suka ƙara kwashewa da dariya gaba ɗaya, suna cikin haka suka ji sallamar su Mariya, Uwani ce kan gaba tana tafe tana leƙe ganin su Ado azaune yasa suka saki jikinsu suka ƙarasa ciki, ɗan dube-dube suka farayi Mariya tai farat tace, " Ado banga malam ba lafiya ina yayi " Mai unguwa dake kulle aɗaki ya zuro kai ta window yace, " gani nan Mariya kune kuka shigo " ganin haka Baba Alasan ya lalli Mai unguwa yace, " Mai Unguwa bismillah munasan ganin ka muyi-muyi mu ƙarasa mu kama gabanmu " Mai unguwa kallon Baba lawan yayi yaga ko kallansa ma baya yi ahankali ya zare sakatar ɗakin, ya fito yana gyara babbar rigarsa cikin mamaki Uwani tace, " Malam lafiya muka ganka ba rawani gaban talakawanka " tsuke fuska Mai unguwa yayi yace, " Andawo za'a fara sa mana ido ko Uwani? " Uwani ɗauke kai gefe tayi dama ɗiban kayanta ne ya shigo da ita gidan tunda taci alwashin ba ita ba ƙara zama tare da Aljanu acikin gidansa.

       Mai unguwa gurun zamansa ya koma kan kujerar sa ya miƙa hannu ya ɗauki rawaninsa ya ɗora aka sannan ya ƙara tsuke fuska kamar ba shi ne ya gama birgima atsakiyarsu ba, gyaran murya ya hau yi yana baxa riga yana muzurai cikin kausashshiyar murya ya fara magana, "  Dukkam yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin talikai tsira da aminci su tabba ga Annabinmu Annabi Muhammad S.A.W, Yanxu kamata yayi ku fara zuwa ɗaya bayan ɗaya kuna miƙa gaisuwa sannan sai mu bada umarnin wanda zai fara magana daga ƙarshe sai mu sallami kowa ya kama gabansa " kallan raini wayo Haruna yayi masa afili yace, " kai amma wannan gayen ka raina mana hankali, ka gama tusa ka gama ihu ka gama iya shegenka agabanmu sannan yanxu kace muxo mu kwashi gaisuwa agurinka, kuturin kayyasa amma kazo da latsin basira fa, kai wallahi duk wanda naga ya tashi ma wallahi sai na datse mai ƙafafu "  Mai unguwa tsit yayi yana kallan gefe da gefe cikin borin kunya yace, " kai mu ake gayawa haka agaban iyalinmu ansan mai ake faɗa kuwa? Kai Ado anaji baza'a kwaɓeshi ba " Ado na shirin magana Baba Alasan ya katseshi ya fara magana.

              " Jama'a Salamu Alaikum dan Allah ku dakata da wannan surutan naku saboda da yawanmu muna da abinyi, wani ɗan jan hankali zanyi garemu ƴan uwa ko ince tunasarwa, Duk cutar da kuka ga Ubangiji ya saukar da ita to akwai maganinta, haka zalika Alkur'ani waraka ne ga duk abinda ya shige mana duhu, yawan cinmu muna yawan sakaki da Addu'a kamar abin nan da ya faru idan abun firgici ko na tashin hankali faru sai kuga mun rasa nutsuwarmu da har zamu iya ambaton Allah, na tabbata dai duk cikinmu kowa nada iliminsa dai-dai misali amma kuma dake muna cikin wani yanayi da ya sa muka mance da saninmu yasa bamu aywatar dasu ba, kuna gani babu siddabarun da Aljaninun nan basuyi mana ba amma dake mun dage sosai da Addu'a cikin lokaci ƙalilan Allah ya kawo mana ƙarshenmu, ina kira da jan hakali atakaice Dan Allah kar mu dinga wasa da Azkar da ambaton ayoyin Allah duk hatsabibancin Aljani Allah zai kareka daga sharrinsa duk da dai bawa baya taɓa gujewa ƙaddararsa " jikinsu ne yayi sanyi kowa sai gyaɗa kai yake sannan Baba Alasan ya cigaba da cewa.

           " Na dawo gareki Goggo, na tabbata duk wannan abun da ya faru ya faru ne ta sanadiyyar ku kuma hakan ya samo asali ne ga yanda Maijidda ta taso agurinki, ba tun yanxu ba Goggo nasha faɗa miki gatan da kike nunawa Maijidda yayi yawa wata rana abun zaizo ya dame ki damu gaba ɗaya, maraici ba kanta aka fara ba kuma idan mukace kowanne maraya zaka barshi yayi abunda yake so to da gaba ɗaya kowa haka zai taso asangarce ba tarbiyya, Goggo ada bansanki da haka ba baki da wasa ko kaɗan akan tarbiyyar yara tunda da ba haka kika tarbiyantar damu ba, Goggo Maijidda fa ƴa mace ce  gidan wani zata kinasan adinga yi dake ana cewa kece baki bata tarbiyya mai kyau ba? " jikin Goggo ne yayi sanyi a hankali tace, " a'a Alasan " murmushi Baba Alasan yayi ya cigaba da cewa.

        " to kinga hakan ba fa'ida bane, gashi nan agarin bin abinda take so har kunjanyo wa kanku mutanen nan, danma mungode Allah babu wanda suka cutar, shi ɗan adam daraja gareshi duk gazawa ko kasawarsa ko kuma nakasarsa to akwai wata baiwa da ubangiji yayi masa, kuma da darajar da yake da ita yanxu kamar mai kifin nan da kuka wulakanta na tabbata ba ku taɓa tunanin akwai wani abu da zai iya biyowa baya ba, kunga wannan ya zame mana iznina garemu baki ɗaya da mu daina biyewa san zucyarmu ko gudun ɓacin ran ƴaƴanmu da jikokinmu, ina fatan Goggo kin fahimceni ban faɗi waɗannan maganganun da wata manufa ba nayi hakan ne saboda bamusan gaba mai zata haifar ba " ya ƙarasa maganar yana kallan Goggo.
            Ajiyar zuciya Goggo ta sauke tace, " Alasan Allah yayi muku albarka, kun daɗe kuna nunamun illar tarbiyyar da nake bawa Maijidda amma tausayinta da ƙaunarta yasa bana ji bana gani har sai wannan al'amarin ya faru insha Allahu hakan bazata ƙara faruwa ba, kuma nabi na Amince zan koma cen gidan ka da zama kamar yanda ka daɗe kanaso mu koma cen Allah yayi muku albarka ubangiji ya ƙara shirya ɗan uwanku Haruna " gaba ɗaya gurun suka amsa da Ameen.

          Haruna harara ya watsawa Maijidda sannan yace, " banxa duk kinbi kin shige zuciyar Goggo ko ni Auta bata yiwa san da take miki ƴar latsi kawai wata rana sai nabi dare na sheme ki yasin " da sauri Goggo ta dafe ƙirji tace, " Haruna Maijiddan zaka sheme mun aykuwa sai dai ka haɗa harda ni ja'iri ina yabonka sallah zaka kasa alwala " ta ƙarasa maganar ta kaiwa haruna duka.

     _*WANNAN SHAFIN NAKU NE ƳAN GROUP ƊINA NA ƊAN BA ƘARA FANS KU CIGABA DA TAKU ƊAI-ƊAI INA BINKU DA TURARE INA FESHE KU CIKIN YANGA DA TAKU ƊAI-ƊAI INAYINKU IRIN SOSAI ƊIN NAN COMMENETS ƊINKU NA SANI NISHAƊI💃🏼.*_

      _Ummou Aslam Bint Adam_😉

ƊAN BA ƘARA COMPLETEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora