YAR TSILLA-TSILLA

10 1 4
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
(Sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

Story & written
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)

_________✍️________

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱((Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A

__________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/

__________________________


Follow me on Wattpad
@deejerleen

Didicated to deary mom (janafnancy)😘😘

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.


NOT EDITED 🛠️


Page 25&26

Kwatsam ogan sa dayaji wannan labarin saiya ce aiyana zuwa ghana inhakane zai taho dani.

Bawanda ya musa masa ko ya zargeshi akan wata manufa sudai fatansu suga nadawo cikin ahalina.

Ina cikin hakanne wata mai girma ya riskeni a kasar ghana wato Ramadan kareem, fitowa ta daga gidan shekara ɗaya ba wata ɗaya ne kasancewar watan qaramar sallah akayi bikina ko watan siyen raguna kuma aka saceni.

Mashallah azumi a kasar ghana akwai dadi ga abubuwan al'ajabi danayi ta gani, ba abinda yafi burgeni irin yadda suke sadaka ga mabukata tun kafin ayi buɗa baki har bayan ayi buɗa bakin, awannan watan suna rage farashin duk wani nau'ikan abinci na ci ko na sha.


Sannan talaka baya kukan rashin abin buɗa baki a wannan wata ba, hakan yasa nakejina kamar a gida nake ga wata sabuwar kulawa danake samu daga iyalan sarkin hausawa abin ba'a magana sai dai nace alhmdlillah 😅.

Anyi azumi lafiya, bayan sallah ne ogan hamza ke shaidamin yana tafe don tafiya dani, murna wajena bazai misaltu ba zanje naga iyayena abin alfahari nah.

Bayan sati daya da sallah sai ga ogan hamza kuwa yazo kamar yadda ya faɗa, dama nasan da zuwansa hakan yasa na shirya tsaf duk wata tsaraba dazanyi nayi kuma na tattara duk abinda aka bani waje guda.

Isowarsa keda wuya aka loda kayana abayan boot dinsa, Kasancewa gidan sarkin hausawa ba boyayye bane yasa baisha wahala bah.

Bayan angama komai ne nashiga yiwa makota sallama dayake babban gidane haka nabiysu namusu sallama masu kuka nayi masu addu'a ma nayi nima dai ina kuka haka na fito zamu wuce dan yace yanaso mu kwana a legos ne, dakyar yaa rabani da kawayena yasani motar muka wuce ina ɗaga musu hannu😢.

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now