YAR TSILLA-TSILLA

9 0 0
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
(Sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

Story & written
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)

______✍️________

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱((Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A

_____________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/
_____________________________


Follow me on Wattpad
       @deejerleen

Didicated to my sweetheart (aysher humaira)💋💋💋

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.

NOT EDITED 🛠️

Page 7&8

*******************
Gari na wayewa yatashi yashirya cikin shirin sa na fita kasuwa, koɗakin da take bai kallah ba ya wuce abinsa,

Abu najin fitarsa tayi wuf tafito da gudu kofar gidan tasawa dan mukulli ta kulle sannan tadawo cikin gidan tana sauke yar karamar ajiyar zuciya,,

Bandaki ta faɗa tayi wanka, fitowa tayi ta shiga dakinta dan ta shirya yau sai tah bar masa gidansa kafin ya hallaka ni, duk acikin zuciyar tah take faɗin hakan,,,

Asalin labarin
1986

Mallam musa Ahmad shine cikakken sunan maifin abu, haifaffan garin Azarene fulanine gaba da baya, su biyu ne wurin mahaifiyarsu da mahaifinsu, sun taso cikin gata da kaunar junan su, musa shine babba sai kanin sa mai suna Muhammad wanda sunan kakansa yaci,,

Musa yakance yayi karatun boko, kuma alhmdlillah yatsaya ne a diploma, inda ya samu aikin karantar wa a wata makaranta ta primary, yayi aurensa na farko inda ya auri kattume, tana da ƴaƴa biyar ne (dan ladi, habu,hannatu,jummai,sai dan asabe, bayan nan ya sake aure inda ya auri rakiya, itama tanada ƴaƴa uku (ummi,nana fatima,tawakkaltu) bayan nan ya sake aure, inda ya auri aysher(inna hurera).

Inna hurera tataso cikin tsangwamar kishiyoyi  kasan cewar duk cikin matan mallam musa yafisonta, dan itace wanda sukayi auren soyayya sabanin sauran da wasu kyauta akabashi wasu kuma hadin gida,,,

Inna hurera mace ce mai hakuri bada da gulma kaifi daya ce, tana zaune da kishiyoyin tah da zuciya daya bata rikon kowa duk da tsana da tsangwamar da suke mata suda ƴaƴansu hakan baisa ta daina kyauta ta musu bah..

Kullum su uku kansu a haɗe yake hakan yasa takeshan wahala, wurin mallam musa kawai take samun sauki, da wannan ne suka miqata wurin boka dan yasaka tsanarta a zuciyar mallam musa harya koreta,,

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now