YAR TSILLA-TSILLA

23 2 5
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
(sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

story & written
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)
_______✍️______

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A

__________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/
__________________________

Follow me on Wattpad
     @deejerleen

Didicated to my sweetheart (aysher humaira)

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.

NOT EDITED 🛠️

Page 17&18

Bisa takurawar da hamza yake mata kwata kwata bata tashi yanzu, hakan ne yasa yau hamza ya lakaɗa mata dukan tsiya, daga baya yayi ficewar sa.

Bayan hamza ya fitane abu da kyar taja jiki tayi wanka kayanta tashiga haɗawa tana gama haɗa kayannata tayi gidan su.

Koda tashiga gidan ta tarar da inna hurera bata nan, dakin inna hurera ta nufa, taba kofar tayi tajita arufe qam, atsakar gidan tazauna rafka uban tagumi tayi har kusan sallar la'asar bata dawoba, sallah abu tayi tana cikin hakanne innan ta dawo daga yawon ta.

Da sallam dauke abakin ta tashigo cikin gidan turus tayi ganin abu zaune a kofar ɗakinta,

"Ke lafiya naganki zaune anan harda kaya kuma",

Inji innan,

Abu ce tace,

"Inafa lafiya inna wannan azzalumin ne yayi ta duka na kamar wata jakarsa takarasa fadin hakan cikin kuku",

Faɗa inna hurera tarufe ta dashi nakan cewa lallai yanzu zata koma gidanta, haka kawai kijawo min sallan siya da abin magana wurin mutane goggo tarasu ace kinqi zaman aure.

"Kitashi kitattara kayanki kikoma kafin raina yabaci inmiki rashin mutunci wallahi".

Cike da tsawa innan ke magana.

Abu kuka take yi sosai tana cewa,

"Dan allah inna kibarni zai kasheni...😭",

Tana kuka haka tafice daga gidan, maimakon natafi gidana kaitsaye gidan kanwar goggo na nufa duk da bawani iya gane gidan zanyi ba kasancewar sau daya nataba zuwa.

Gashi magrib ya gabato kowa na komawa gidan sa maza na nufar masallaci, tafiya nake ko ganin gabana bana yi ahaka na karasa unguwar, wanda tsakanin unguwar mu da unguwar qanwar goggon tafiya ce mai nisan gaske,

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now